Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Ko da ta zo ya tambayi sunanta se ya gane mahaifinta mutum ne da baya ƙaunar shi don ko sallah baya zuwa masallacin shi ta bayan layi yake zuwa, murmushi kawai yayi ai ya riga ya san ba kowa ne ze so ka a duniya ba amma tunda akwai hakkin makotaka ze sauke.
“Zan sanya driver da ke kai Fauziyya ya dinga biyowa yana daukar ki se kuke tafiya tare kuna dawowa tare se ya fi miki sauƙin neman abin hawa a nan wadda suke wahala”
Har ƙasa ta duƙa ta mishi godiya Dukda kwarjini ne kawai da ya cika ta dashi in ba haka ba babu abunda babansu be faɗa musu akan Prof kaka ba.
Haka ko aka fara, abunda ya fara ba Fauxa haushi yadda yarinyar take shigowa har su je su yi paper su dawo bata gaisheta, dukda ita ba kalar wacce ta damu da damuwar wasu bane sede haushi ya kan cika ta da al’amarin yarinyar kina cin arzikin mutanen gida kina musu gadara.
Wata rana suna da papern rana tun da suka fito ma Fauxa ke wayanta da Zubair don yau din zasu haɗu a makarantar, musamman ya kawo wadda ze zauna yayi mata papern ranar a madadin ta ita kuma su fita tare.
Ko da ta isa bata nufi hall ɗin ba ta zagaye bayan classes anan Zubair ya ɗauke ta suka fita, ya nuna mata yayi kewanta ta amince mishi sau ɗaya dae kan ta gama paper ta koma kulle, lallaɓa shi tayi akan tunda suna son juna ya turo magabatanshi in ya so tana gamawa baban ya ɗaura mata aure su huta, yace ze yi tunani akai haka dae suka gama yawon su ya haɗo ta da chocolates masu yawa.
Ko da ta dawo kowa ya waste a school wanchan yarinyar se tsaki take ja, driver dae sanin halin Fauza yau ne kuma na biyu na farko sun hadu har dasu sakina yasa be ce komai ba.
Koda ta zo bata ce musu su yi haƙurin ajiye su da tayi ba kawai ta shiga ta zauna abunta tana bare diary milk, har sun kusa unguwarsu yarinyar da ko sunanta bata sani ba tace
“Fauziyya sunanki ko? Nace ya kamata kike sanin darajar mutane, don ana cin arzikin gidanku ba shi ze sa ki samu damar wulakanta mutane ba, sannan wallahi kika yi tsiya se in yi tattaki har gaban tsohon ki in sheda mishi abunda kike yi in kin fita, ko de!”
Ta taɓe baki tace
“na ji labarin da saninsu ma tunda arzikin na safarar yara ne ko me nasu tayi sakamako n…..”
Wani kalar buge mata baki da hanci da fauxa tayi da gwuiwar hannu se da yasa hancin ta da bakinta fara zubar da jini.
“Da alama baki san Fauxa bane! Ina me tabbatar miki wannan gargadi ne ɗon wannan ne karo na farko ko da bakin wasa wannan kazamtacciyar bakin naki ya sake ambatar iyayena ko da Kalmar alheri ne se na gurje shi bare ta tsiya”
Tana gama faɗa ta saka hijab yarinyar da already ya ɓaci da jini se yarfa hannu take tana kuka ta share bayan hannunta, don kowa ya san Fauxa er gayu da kwalliya ce, kayan ta bata yarda wani stain ya bata su.
Driver ne yace
“ashhha! Hajiya Fauxa ayi haƙuri ai duniya ɗan hakuri ne”
Bata ce mishi komai ba sbd be saba shigar mata idanu ba wannan ne na farko kuma ta ɗaga mai kafa, yana tsayuwa yarinyar ta sauka da gudu tana kuka ta shige gidansu.
Tsaki me karfi fauza ta ja tana rasa me ke damun baba prof da manna waenda basa kaunarka jiki.
Ta samu fa’iza ta dawo da sha tara na arziki don sayayya me dumbin yawa Faizan yayi mata matsayin kanwarshi, kowa seda ya samu tsarabar shi kasancewar shi mutum me kyauta sossai.
Washegari ko da suka tsayawa yarinyar bata fito ba Fauza tace su wuce, a makaranta ta samu yarinyar da wasu mates ɗinta don ita bata san makarantar ba tunda jarrabawa ne kawai ya kawo ta sbd gudun haduwa da su sakina yasa baba yayi mata registeration a wani makarantar.
Yadda suke ta hura hanci ga yarinyar fuska a kumbura yasa Fauxa kwashewa da dariya, irin kallon da suke mata na zaki daku yau tayi musu kan tayi wucewarta, bayan sun gama paper an waste tana tahowa don zuwa wurin mota en matan huɗu suka yi mata ƙawanya.
“Ke! Me kike takama dashi da zaki illatar da sukaina kuma kiyi Tunanin kin ci bulus?”
Sha ka hura dake bakinta ta ciro ta ɗan lasa tana Kallonsu dariya suke bata.
Ɗayan tace
“don an zagi prof kaka menene? Waye be san yadda kudinshin nan dake ta hauhawa ba na Allah da annabi bane? Ko karya aka yi don an ce yana safarar mata?”
Dayar tace
“ai ba mata da yara kaɗai ba har abubuwan shaye shaye don duk abunda kaji ana jita jita a kai da ƙamshin gaskiya”
Na farkon tace
“karki kai da nisa gashi har yaran yake baiwa suke sha, waye be san wannan ƴar fitsitsiyar babu abunda bata sha ba?”
Jakarta Fauxa ta sauke ta buɗe ta ciro paper ta fara naɗe sha ka hurarta na big bom, tana nadewa ta fara magana.
“Kaman yadda na miki alkawari bakinki ya sake aibata iyayena se na gurje shi to yau se na gurje shi da ƙasa idan gasa miki shi ne ba’a yi da kyau ba yayin wankan haihuwa yau za’a miki gashi me kyau…”
Tana kallon sauran tace
“ku kuma en korenta kowaccenku sakamakonta na rubuce a goshinta, ke yatsar da kika nuna ni dashi yau se an yi miki gyara, ke kuma haƙorin ki ɗaya se kin rasa shi, ke kuma zaki komawa uwaki da karyayyen hanci kin san Karyewan cartilage? To yau zaki sani”
Tana kai nan ta cire hijab ɗinta ta ninke, da gudu tayi cikinsu suka fara dambatuwa, dukda kwana biyu rabon da tayi faɗa tana acting classy yau seda ta zage tayi musu duk abunda tace don bata taɓa faɗan magana ta kauce akai ba.
Tana yi tana cewa
“Da kun tambaya tun farko waye Fauxa da baku shiga sabgata ba”
Duk saida ta cika alkawarinta kan da kyar aka dagata kan su.
Taje ta ɗauki hijab ɗinta tana haki ta saka ta ɗauki sweet ɗinta ta cigaba da tsotso tare da rataya jakanta tayi mota, ko da suka dawo gida ita har ta mance ma da abunda tayin.
Chan dare tana cin Samosar da tayi bayan dawowarta da tea kawai Ya Farhan yayi sallama
“Fauziyya zo mana”
Dukda be saba mata irin kiran ba haka dae ta miƙe ta bishi ɗakin su taga yayi, a zuciyarta take masifan Allah ya sa ba aiki ze saka ta ba, tana sanya kafafunta a ɗakin ya maida kofan ya rufe, Faraj dake zaune da dorina yace
“na lura barin ki da ake shi ya sa ko yaushe kika tashi ɗauko mana magana se ki ɗauko kalar wadda ba’a taɓa yi ba, bana Tunanin ko hanyar police station baba ya sani amma wai yau a ta sanadiyarki aka zo har wurin karantarwar shi za’a daukeshi..”
Takaici ya hana farzan din cigaba da magana, Farhan yace
“Fauziyya yau zan tabbatar da na huce duk takaicin da nake kwasa akanki, yau ɗaya zan saɓawa umarnin Baba na be amince kowa ya taɓa ki ba in yi miki dukan sauke takaici, wawuya wacce bata san me ke mata ciwo ba..”
Dukda yadda zuciyarta yake bugawa, bata nuna a fuska ba, ta san sun fi karfinta kuma ihun duniya tayi anan babu me jiyo ta bare a zo cetonta gwara ta sallamar kawai su kashe ta in sun so.
“In de akan yaran da na daka ne wallahi ko gobe suka sake maimaita abunda suka yi haka zan musu, ba police ba su kawo rundunar sojoji….”
Bulalar da Farhan ya fara sauke mata cikin takaici ne ya katse mata maganar, dukan kawo wuƙa suka mata tun tana ihu har ta dena tana jiran kawai su kashe ta, har hijab ɗinta seda bulala ya yayyaga fatanta har jini yake yi..
“Tashi ki fice ko in kasheki kowa ya huta”
Farhan yayi mata ihu hawaye na zuba a idanunshi, iyayenshi yake ji wa takaici, be taɓa ganin baba prof a yanayin da ya ganshi yau ba, wai har wannan yarinya ta ja ake gayamishi maganan da ya saka shi zub da hawaye dukda be yarda kowa ya gani ba amma sun san ba karamin zafi ya mishi ba.