Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Da sallama suka shiga gidan nasu da rabin shi a zube an kare da buhu duk jar ƙasar gasu nan a barbaje ko ta ina, idanun Fatima ne ya fara kaiwa ga mawanki kwanuka ne a wurin da wasu irin bakaken tukwane waenda zan iya rantsuwa tunda aka saye su basu taɓa ganin ruwa da sunan wanki ba, kuma duk sbd rashin kuɗin sayan omo ne.
Aunty ne ta kai idanunta kan dakunan gidan guda biyu banda jar block babu abunda ke jikin ginin ko arzikin Plaster bare fenti, kuka Fatima ta fara
“Aunty kina nufin anan zamu cigaba da rayuwa?”
Aunty tace
“na lokaci kaɗan ne kan mu samu mafita”
Tana maganan ne kaman itama zata yi kukan, kanta Sara mata yake sbd tsabar tashin hankali.
Maihaifiyartace ta fito kana ganinta kaga wahala da talauci ta zuba musu idanu tana kallo..
“Yau kuma shamsiyya da mu kika tuna?”
Kuka ta fara tana cewa
“inna Sulaiman ya sake ni!”
“Ashe muna da daraja da ƙima da har don an sake ki zaki waiwayi gidan nan? Mu da kike jin kunyar nuna mu a matsayin iyayen ki? Mu da duk yaran da kika haifa bayan wannan itama na manta shekarar da na ganta akwai wadda kika taɓa nunawa gidan nan bare mu? Shekara nawa Shamsiyya ki ci ki sha ki kwanta ba tare da mun zo ranki ko sau ɗaya ba? Aurenki na biyu fa hayan iyaye kika yi kika yi wannan aure hidimarki saide ƙawaye en karya da dangin su a haka dama kike son ganin alkhairi? Ba zamu kore ki ba ga ɗaki shiga ki zauna duniya ce ta fi bagaruwa iya jima”
Wucewa suka yi suka shiga fallan ɗakin da babu komai ciki se buhu a shimfide suka zube, kowa da abunda yake sakawa ita dae Shamsiyya Tunanin ta yafi tafiya ta yadda zata dau fansar wannan wahalar da ta sha, yayinda ta wani bangare take Adu’ar Allah ya sa ma wannan fitinanniyar yarinyar da ta tsole musu idanu ta mutu ma kan su isa asibiti.
****
Ta ɓangaren Fauza kuwa emergency aka yi da ita, Faizan ya kasa zama se jeka ka dawo yake yi hannunshi ɗaya dunkule yana dukan ɗaya dake ware, kusan duka en gidan zuwa yanzu sun iso har da su Prof da abun be faru a gabansu ba, saida likitoci suka share awanni sama da huɗu kan suka fito suna yarfa gumi a tsorace Faizan ke Kallonsu bakinshi ya gaza furta kalma ko guda ɗaya ne..
“Dr kayi magana mana kayi shiru?”
Cewar Farhan.
“Alhamdulillah mun samu mun ceto rayuwarta ba serious ciwo bane in shaa Allah, tsorata ce ta saka ta wannan doguwar sumar”
Duk ajiyar zuciya suka sauke, Faizan be jira wani bayani ba kuma ya wuce likitan ko jin kiran da yake mishi be yi ba ya tura kofan ya shige.
Tana kwance kan gadon ya karasa kaman ze zubda mata hawaye tsabar tausayi ya riƙe hannunta yana shafa kanta bakinshi ya buɗe a hankali ya fara magana
“kiyi haƙuri precious pearl I couldn’t save u from that bastard attack, am so sorry da kika kasance a haka in front of my eyes… Please be fine kin ji? Just be fine ki yafemin and I promise you a happy life that will last to end”
Dukawa yayi yayi pecking goshinta yana kallon lips ɗinta da babu komai a kai se ainihin red nd black color ɗinsu da suke sarƙe cikin juna suka bada wani kala me kyau, babban yatsarshi ya sa ya shafa lip ɗin yana ta aikin kallonta a ranshi kuma yana ayyana yadda ze fara neman Fatima ya koya mata hankali don bata sha ba.
Idanunshi zube a kanta ya tafi tunani, ya sani lokaci ɗaya Fauxa ta chanza akalar zuciyarshi ta sakata rusuna bisa burin da ya ɗauka nayi mata rashin mutunci a gidanshi har se ta gudu da kafafunta, ya fara gudanar da shirin ne ta hanyar Haɗata da ayyuka kala kala a gidan nashi kuma ya barta a matsayin ta na kanwarshi a tunaninshi zata kawo mishi musu ko rashin kunya yadda ze samu hujjar ladabtar da ita da kyau sede ta cinye wannan jarabawar ta hanyar haƙuri da juriya, sanyin hali da tsabta na ban mamaki wadda be taɓa zaton hakan take ba.
Abu na biyu shine son da take yiwa iyayenshi kusan sune komai nashi duk me son su kuwa dole ya so shi, wannan ya taka rawar gani sossai wajen ganinta da mutunci da daraja, Sam baze ce ga sadda ya fara son ta ba saide ya san ya zuwa yanzu zuciyarshi gabaɗaya cike take da tsananin so da tausayinta.. Dafa shi da Baba Alhj yayi ne ya saka shi ɗagowa tare da waiwayawa iyayen nasu ne ciki se Jaddah.
“Ka Daena zurfafa tunani haka Faizan in shaa Allahu zata samu lafiya”
Kanshi ya mayar ƙasa yana zare hannun nashi cikin nata ya mike tare da basu kujera, fuskanshi Sam babu wata walwala.
Kwananta biyu a asibitin don ranar da aka kaita da yamma ta farka, duk shigowar shi baze shigo hannu banza ba ze shigo da abubuwan ciye ciye kuma ya zauna ya jima suna ɗan hira da Jaddah ko ya zauna shiru rike da waya ko idanunta biyu bata taɓa gaisheshi ba Kallonshi ma ta ƙi tayi, abun na damun shi amma ya bata space ta warke tukuna.
Shi aka baiwa sallamar ta, bayan ya shigo yace
“zaliha Haɗa kayan ku mu wuce gida”
Kasancewar su biyun ne kaɗai a ɗakin Jaddah ta je gida.
Haɗa kayan tayi, fauza da fuskanta ba wani fara’a ta sauko sanye da hijab maroon har ƙasa, jerawa suka yi da zaliha tana rike da wasu kaya suka nufi motar tashi, zaliha ta zuba kayan a booth yayinda ta dawo ta buɗe baya ta shiga, Fauza ta buɗe bayan da niyyar shiga ta ji muryarshi daga bayanta
“Dawo gaba ki zauna”
Bata waigo ba kuma bata saki kofan ba.
Idanu ya zuba mata se yanzu take son nuna mishi taurin kan nata? Ya ayyana hakan a ranshi yanzu baze iya fushi da ita ba in yace ze iya ma ya san babban karya yayi, hannu ya sa ya buɗe gaban ya zare hannunta daga baya ya sanyata a gaban tare da rufewa ya zagaye.
Kamshi da sanyin motar suka ratsa ta, dukda ta san abunda take yin ba daidai bane amma dole ta nuna mishi kurenshi na laifin da ya aikata mata, har a asibiti bata bar anfani da wasu magunguna da Jaddah ta jiko su a wani katon buta ba tana tsarki Dukda ta warke se abunda ba’a rasa ba amma bata manta azabar da ta sha ba, haushin shi take ji kaman ta shake shi.
A hankali yake murza stirring ɗin idanunshi zube bisa titi, babu wadda yayi magana a motan har suka isa gida, be gama parking ba ta balle murfin motar tayi sashen Jaddah, da kallo ya bita har ta ɓace mai ya sauke ajiyar zuciya yana shafa gashin kanshi.
Zaliha ce ta tattare kayan sallamar tayi sashen jaddar itama.
Daga ranar ta fara wasan ɓuya dashi, bata bari su haɗu ko a hanya, ze zo sashen Jaddah ya gama zaman shi ko kyallin ta baze gani ba, ya san tana avoiding ɗinshi ne gashi yana da tafiya tunda ya jima a gida dole ze koma wurin aiki and babu wadda yayi mishi maganan ya kamata su koma haka har ga Allah ya gaji matarshi yake buƙata
Rigingine yake a kan kujerar Jaddah, chan yake jiyo sautinsu ita da Fa’iza tana tsokanar fa’iza akan wai sun sasanta kansu da Faraj don aiki suke daga shi har Farhan yanzu fa’izar ce ke level 1..
“Gwara ma ki bari a saka mana kusa mu sha buki, yadda zan zage na aurar da ƴar ƙanwata itama”
Fa’iza na murmushin yadda Fauza bata taɓa bari ta kuntata ko ta shiga Tunanin ba, cike da jinjinawa haƙurin Fauxar ta yadda kowa ze yaɓa mata magana ko ya zage ta ko ya mata zafi babu me fahimta sbd bata nunawa tace
“waye kanwar taki? Lallai ma yarinyar nan karki manta na baki kwana dai dai har talatin da ɗaya… Rainin wayau”
Dariya Fauza tayi tana cewa
“kin manta kwana ɗari ba ɗaya kika ba ni, ke ajiye batun wannan karki manta wadda nake aure don haka duk gidan nan karkashina kuke kuma wallahi dole ku ce min Aunty”
Yadda tayi maganan ba fa’iza kaɗai ba har shi seda ya murmusa, fa’iza na shirin magana suka Haɗa idanu dashi.