Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
“Me ke shirin faruwa ne?”
Yayi maganan yana sake kallon hannunta da ta gimtse a cikin nashi har yanzu yana iya jin yadda jikinta ke rawa ta ciki….
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
25
Ko da suka isa asibitin Jafar ne ya duba raunin aka yi mata allura, ganin ko tsorata bata yi ba kaman yadda ta saba ba ya san har lokacin bata dawo daidai gabaɗaya ba, haka dae Jafar ya dawo dasu gida yana kallon yadda gabaɗaya Faizan ɗin Damuwa me yawa ya nuna a fuskanshi.
“Ka tafi da motar na ga kaman hadari ko gobe se ka ba driver ɗinka ya dawo dashi”
Cewar Faizan bayan sun sauƙa yana rike da hannunta, Afnan tayi mata Allah ya kiyaye kan suka fice daga gidan.
Haurawa suka yi zuwa ɗakinta, cikin kulawa yace
“bari na Haɗa miki ruwa ki watsa se ki sha magani ko?”
Girgiza kai tayi idanunta tab da hawaye ta sake riƙe hannunshi da yake Shirin zarewa cikin nata.
Fuskanshi cike da tausayinta yace
“babu abunda ze sake faruwa yanzu kin ji? Sake ni kiga”
Nan ma girgiza kai tayi se hawayen ya gangaro, babu yadda ya iya illa ya sa hannunshi ɗayan ya share mata kan ya ce ta tashi su tafi, a tare suka shiga bayin ya Haɗa mata ruwan ya zare mata hijab ɗin se ta ɗan ja baya amma bata sake shi ba, yace chan ƙasa
“Toh yanzu kiyi wankan bari na fita”
Cikin wani irin murya a shagwaɓe cike da sangarta tace
“uhm uhm ni de don Allah karka fita ka barni ka Juya bayanka kawai”
Babu yadda ya iya ya matsa daga bakin kofa ya juya mata baya, sharp sharp ta watsa ruwan tana ta kalle kalle, tana gamawa ta janyo towel ta ɗaura tana kokarin jan hijab ɗinta ta saka Bon ɗin da ta kama gashinta dashi sakwa sakwa ya kunce zuban gashin ya haɗu da ruwan dake jikinta yayi mugun firgitata ta kwalla ƙara, a hanzarce ya waigo kan yayi wani yunkuri ta faɗa jikinshi yayi saurin taro ta, yana cewa
“menene kuma?”
Siririn kuka ta saki tana cewa ya taimaka ya duba mata bayanta motsi taji kaman ƙadangaren ne ya dawo.
Daga ita har shi jikinsu rawa ya ɗauka, zuciyarshi na bugawa da karfi karfi jin yadda take kara mannewa jikinshi hannunshi na cikin wet gashinta yana shafa bayan wuyanta zuwa bayanta, ya salaaaam ya ambata cikin ranshi jin yadda take kokarin kunce mai notikan kai gabaɗaya.
Janyeta yayi suka fito daidai nan Fatima ta buɗe kofan ta shigo tare da nufo ciki gabaɗaya ai se idanunta suka mata mugun gani, baƙin kishi ne ya taso ya Rufeta idanunta har rawa suke yi..
“Me…me me zan gani haka? Me wannan?”
Be tankata ba yana rike da fauza har zuwa dressing mirror saide bata zauna ba ta kara mannewa a jikinshi fuskanta cikin kirjinshi tana sauke numfashin dake gigitashi ba tare da ta san me take aikata mishi ba.
“Zauna”
Ya faɗa calmly.
Zama tayi ya juya ga Fatima dake tsaye yace
“Next time pls ki nemi izinin me wuri kan ki shigar mata, and bata da lafiya find something da zata ci don bazata bari na fita nema mata abinci ba”
Har kaman zata lailayo Ashar ta maka se kuma ta fasa ta ficeee fuuu
Sama sama ya shafa mata mai, kan suka tafi tare ya buɗe wardrobe ɗinta ya duba mata riga marar nauyi ta sanya, bayi suka koma suka yo alwala a tare daidai lokacin da ruwa ya tsuge sossai kaman da bakin ƙwarya Dukda daminar bata wani shiga sossai ba especially a ta north ɗin nan amma Abuja ba laifi suna samu akai akai tun last week.
Shi ya ja su sallar magrib bayan sun idar ya bata Alqur’ani ta karanta, cikin tattausan muryarta ta fara karantawa wadda ya taimaka sossai wurin ƙara natsar da ita, se a sannan ya mike yaje ya duba Fatima ta kusa gama girkin ya sakata tayiwa husna wanka duka ranta a cunkushe, tunani kawai take me ya faru tsakanin fauza da Faizan da har yake riritata haka?
Shi kuwa wanka yayi ya sake alwalan isha ya fito sanye da dogon wando da jallabiya, hannunshi waya ne yana magana da Baba prof da yake ta jimamin wannan abu, nema yayi da ya bata wayan shima kuma dama daidai lokacin yake isa wurinta se ya zauna daga gabanta ya miƙa mata wayan.
Tana sawa a kunnenta ta fara hawaye cikin rawar murya suka gaisa da baban yake rarrashinta karta damu babu wani abu ta rike adu’o’in da ya bata sossai kuma ze kara mata wani, rikici ta sanya mishi akan ita kam zata dawo wurin jaddar ta tana jin tsoro.
Da kyar ya shawo kanta zata zauna Abuja ɗin kan ya ba wa babanta wayan shima dae ya mata sannu da Allah ya kiyaye gaba haka jadda da mammi ma, bayan ta sauke wayan se ta miƙa mai ƙin ƙarba yayi.
Idanunta da suka yi laushi yau ɗin gabaɗaya ta ɗaga se suka faɗa cikin nashi da ya kara lumshesu yana kallonta, a hankali tace
“Yaaaya ga wayan”
Ya rasa yadda take kiran nata yaayan da yake jinshi har cikin ɓargonshi ba ƙarya, a hankali yace
“ba zan karɓa ba” chan ƙasa
Kara marairaicewa tayi tace
“Meyasa to?”
“Me yasa kike son barin ɗakinki ki koma gida sbd wannan abu da be taka kara ya karya ba? Baki san kowacce mace da akwai abunda take fuskanta a nata gidan aure tana zama jaruma ne tayi over coming komai ba? Na Gaza wurin kula dake ne?”
Ya karashe tambayar da wata murya da ta sakata maida kanta ƙasa kan ta girgiza tace
“A’a ka yi hakuri”
Yace
“na hakura, tashi muyi sallah”
Isha suka gabatar da kanshi ya fita ya karbo abincin don Fatima dangwalarwa tayi a dining ta wuce ɗakinta.
Kasa hakuri tayi ta kira Auntyn ta take tambayarta meyasa bata fara ganin abunda tace ba, Auntyn tace mata an samu akasi amma ba shi ze sa su karaya ba, ta cigaba da zubawa sarautar Allah ido, rayuwar Fauza a gidan kaman a tafin hannunta yake.
Husna ya ɗauka da tayi bacci a parlorn yayi ɗakin Fatima da ita, tana sauke wayan yana buɗe kofan da sauri ta gyara zamanta, a kan gado ya kwantar da ita yace
“zata kwana wurinki yau”
Juyawa yayi ya fita yana mamakin yadda Fatiman ta kasa zuwa tayiwa Fauza ko ya jiki ne, har ya taɓa handle ya dakata ya juyo fuskanshi ba yabo ba fallasa yace
“kaman na ce miki Fauza bata da lafiya ko?”
Tace
“eh ka faɗa, me zan mata bayan girkin?” Ta faɗa cikin gatse.
Yace cikin mamaki
“wai dama haka zuciyarki yake ne ko yanzu ne ya koyi sabbin ɗabi’un nan? Fatima sannu bazaki iya zuwa ki mata ba? Wai me kika ɗau kishi ne?”
“Me kuwa na ɗauke shi? Ni yaya meyasa kake min haka ne? Meyasa a ko yaushe abu ya Haɗa mu ni ce da laifi? Ni da nayi ɓari ko sannu ta min bare Allah ya kawo na mora? Gwara ni na mata girki ita ko ruwa ta kawo min? Duk baka ce komai ba se ni yanzu da ban san hawa ko Sauƙar ciwon munafurcinta ba zaka wani ce in je in gaisheta? Kayi hakuri ba zan iya ba”
Dawowa yayi ya zauna ganganta yace
“Fatima ki fahimce ni, babu wacce nake fifitawa tsakaninku illa ma ita da nake tauye ta, kina sane tunda ta zo gidan nan sati na shidda kenan nake ga ban taɓa ware kwana ɗaya tal da sunan nata ba, ban cika mata duk wani hakki na matsayin matata ba kina kallo baki taɓa ce min hakan ba daidai bane, annabi fa cewa yayi mafi darajar mace itace wacce zata taimakawa mijinta wurin bautar Allah in taga zai kauce ta dawo dashi daidai, duk na rasa wannan daga gareki…”