Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
“Mun je birthday party ne”
Duka parlorn salati ya ɗauka, ga ɗiyar gidan baba prof a birthday party har Abuja.
“Ke da waye”
Baba ya jefa mata tambayar
“ni da sakina da rahama, wlh baba duk partyn da nake zuwa a cikin garin nan ne wannan shine karo na farko da muka tafi Abuja”
Salati aka sake dauka yarinyar kaman aljanu ke displaying ɗinta don ita fa idan lokacin abu yayi a yi shi, gaskiya komai dacinta fede ta take idan har ya kama ɗin.
“Unbelievable! So you have been doing this for long?”
Faizan ne ya jefa mata wannan tambayar.
Shiru tayi.
Ya sake cewa
“wayan dubu ɗari uku a ina kika samu?”
Tace
“wan…wani ne ya sa…ya min”
Farhan da su Faraj ji suke da a basu ita su yagalgalata ko zata yi bayani da kyau amma baba prof ya hana.
Ido kaman ze cinyeta tace
“baba wlh ni ban yi niyyar shan giya ba, Zubair ne ya munafunceni ya saka min cikin coke, shekaranjiya ma shisha ce kuma ce min yayi flavor ne ciki baya bugarwa shiyasa na sha”
Rasa me magana aka yi a parlorn Amminta ne ta rufe ta da duka tana kuka tana cewa duk wani abunda ze sa ta tozarta ta idanun kishiyoyi tayi, gashi har wasu na jin daaɗi nasu shiryayyu ne ita kuma gurbatacciya, ita kam bata koya mata hakan ba sai de in a wuraren da take zama aka hore ta da hakan.
Mammi ce ta kwace ta sauran matan parlorn duk babu wadda ya motsa, bakinta har yana jini ta lafe jikin mammi tayi shiru.
Nasiha me tsayawa a rai Baba prof yayi musu, ya kafa mata sharaɗoɗi babu ita ba sakina da rahama, babu ita ba boko ze biya mata neco tunda an yi nisa da waec tayi shima lokacin in yayi da sa ido sossai zata yi, ko bakin gate aka sake ganinta da kanshi ze ɗauki mataki a kanta, manyan be yarda kowa ya sake dawo da abunda ya wuce ba suyi ta mata Adu’a, sadaka da saukar Alqur’ani, yaran kuma in sun yi ma sun Santa don haka kar a kawo mishi ƙarar ta in aka goge ta da magana ta rama.
Rayuka dayawa ba haka suka so abun ya tsaya ba, sai de ya suka iya, haka ta koma sashen jadda da ta zage tayi ta mata nasihu batayi fushi da ita kaman babanta ba.
Bayan sati ɗaya Faizan ya ɗauki matarshi suka koma Abuja dama an je an mata jere, ita kam Fauza ta zama kifin gwangwani hakan ya dawo da halin ta na da kannenta basu isa sun sake a gefenta ba, haka duk wani wadda ya gayamata magana akan rayuwarta se ta gayamai shuwaka, ana haka sakina ta shirya ta zo gidan…
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
14
Daga bakin gate ta tambayi sashen Jaddah tunda ba zuwa gidan suka taɓa yi ba, mai gadi kuwa ganinta da jumbuleliyar hijab ya zata irin baƙin da jadda kan yi ne don ba’a raba ta da jama’a daga sashenta har sashen mammi, da hannu ya nuna mata sashen ya dae tabbatar mata jadda bata nan sun fita barka da sauran matan baba prof karshen layi.
“Babu komai zan bada saƙo ne kawai in juyo”
Da sauri tayi sashen tana shiga parlor ta fara kwala kiran Fauxa, da gudu ta fito jin muryar da ta sani ne tana ganin sakina kuwa ta rungumeta da murna.
“Kina lafiya Fauxa? Ai hankalinmu duka a tashe Zubair ya ƙi tafiya Sam wai se ya tabbatar da babu abunda aka miki a gida, yanzu haka ma shi ya kawo ni yana farkon layin nan”
Jan ta Fauxa tayi ɗaki tace
“babu abunda aka min sakina sai de na zama matar ƙulle, kowa baya sake min fuska musamman waenda muka yi sabo dasu, har baba prof gaisuwa ta kawai yake amsawa, ke a takaice dae gabaɗaya duniyar baya min daaɗi, ba cireni school bane damuwa don makaranta be dame ni ba amma rashin fitan nan ga aiki don yanzu dole in ke komawa sashen mu ina aiki tunda babu wani aiki sashen jadda, komai fa ni nake yi tare da umarnin Baba Alhj”
Sakina tace
“kaiii wannan rayuwa na gidan nan Allah dae ya fidda ki, yanzu ko gate baki leƙa wa?”
Na kara tabbatar mata da ko gate ba’a yarda in leƙa ba idon yayyuna duk a kaina yake, yanzu an yi min registern neco tunda an riga an gama waec ina ga shine kaɗai abunda ze sa na taka waje.
Wayar ta karamar touch ta mika mata tace
“gashi ki riƙe a hannunki zamu yi magana, bari naje tunda kin ce ko mu an rabaki damu wayanki kuma mugun wan ki yayi miki ajalinshi”
Karɓa tayi tana mata godiya harda jajjada mata bata san irin taimakon da tayi mata ba don bata san tana son Zubair ba seda aka katangeta da sauraron muryarshi.
Bata raka sakina ba don kar a gane, amma a fita saida sakina ta hadu da Fa’iza da kallo kawai fa’iza ta bita har ta fice, fasa shiga gidansu tayi tayo wurin Jaddah.
Ɗakin Fauza ta tura da sauri Fauza ta boye wayan karkashin pillow.
“Malama ya da shigo min ɗaki babu sallama?”
“Fauza me Sakina ta zo yi a gidan nan bayan irin kashedin da aka yi miki?”
Wani irin kallo Fauxa ta watsa mata
“last da na bincika dae sunanki ba ruqayya ba! Uwata kenan ko? Sannan a shekaru kin san na girmeki don haka ki fita sabgata kaman yadda kike tun farkon fara sabon rayuwata babu ruwanki, in kuma kika ƙi kin san halina bani da kyau ko na sulen kobo wallahi”
Idanu kawai fa’iza ta zuba mata kan ta girgiza kai tace
“Allah ya shirya”
A masifance Fauza tace
“Ameen in da gaske kike, kema na lura yayarki kan ta tafi ta tsammiki wannan munafurci nata in ba haka ba yaushe kika yi wani buɗewar idon gayamin magana yen yen yen da fuska kaman nawa anan”
Har Fa’iza ta bar parlorn tana jin masifar Fauxa.
Ita kuwa fa’iza na kulewa ta fiddo wayan dake ringing, Zubair ne nan ta gayamashi duk abunda aka yi mata a gida
“yanzu wani mataki kike shirin ɗauka?”
Tace
“ka bari tukuna in ga matakin su don na tabbatar ba shikenan ba, shurun baba prof wani abun ze kulla wadda babu wadda ze yi zato ko tunani, amma in na fara fita necon zan san yadda zan yi muke haduwa for now mu dinga wayan kawai”
Haka ta kasancewa Fauxa, kullum in ta tashi asuba bazata dawo sashen jadda ba se ta gama komai na sashensu ta kan yi mamakin Amminta wacce bata rabo da maganan Fauxa kin wulakantani kin zubar da ƙima ta a idanun kishiyoyi, hakan yasa har ta gama ayyukan idan ba gaisuwa ba daga babanta, mamanta har Aunty Amarya babu wadda take sake tankawa.
In ta gama na sashen ta koma sashen jadda tayi na nan da aka ware mata, kan ta karya, jadda zata sakata wucewa ta gaida duk matan gidan, bata fitowa daga sashen mammi kuwa se da nasiha me tsayawa a rai, hakan be hana ta waya da Zubair ba, sossai yake kara riritata yana hure mata kunne akan rayuwar gidansu ba rayuwa bace takura ce.
Ana haka take samun labarin ɓarin da Fatima tayi, dukda babu wadda yake magana akan zaman su don haka bata san yadda suke yin ta ba amma ta tabbatar kowa se da ya shiga damuwa kan wannan bari har Fa’iza aka tura dake an gama jarabawar makaranta Hutu ne kawai za’a bada abunda ba ɗabi’ar Baba prof ba, don baya yarda wata cikin en matanshi taje gidan wata zama da ko wanni nufi kuwa.
Ko a jikin Fauza kaman ma bata san me ake yi ba, bayan sati biyu da tafiyar fa’iza ta fara Neco, driver musamman aka ajiye mata shi ze kaita ya jira har ta fito ya dawo da ita, to ranan baba prof ya fita za shi unguwa da ya Faraj kenan ya hangi wata yarinya me irin uniform ɗin Fauzan a farkon layi saka Faraj parking yayi ya kira mishi ita.