Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya zuwa wannan layin
09039206763
Ko ki tura katin waya ta layin na sama tare da shedar biya ta what’sapp.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DIDDIGAR ƘAYA
(Mai Wuyar Tsincewa)
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
And Now..
*Diddigar ƙaya… Paid*
*Shafi Na huɗu*
*PAID BOOK*
ƊANƊANO
**WANNAN SHAFI SADAUKARWA CE GAREKI MRSJMOON GWANATA KUMA SHUGABATA❤️**
Da wani kalar sauri ta amsa tana me miƙewa tace
“Na’am Alhaji! Sannu da dawowa”
Be amsa ba se idanu da ya zuba mata, duk cikin yaranshi itace yake jinta na karshe a cikin zuciyar shi, Allah ya gani babu yadda ya iya ne yake zaune da ita amma ya gaji iya gajiya da halayyarta babu randa za’a wayi gari a yini ba’a kirashi kan case ɗin Fauxa ba, a gida babu irin rashin kunyar da baya ji da kunnuwanshi tana yiwa yayyun ta, duk gidan babu wadda baya girmama na gaba dashi se Fauxa, dokarsu kuwa ba a bakin komai yake ba a gareta.
“Ki je Baba Prof na kiranki”
Daga haka yayi gaba sbd saƙo ne Yayan nashi ya bashi Idan ya shigo ya tura ta, mikewa tayi da hijab ɗinta dogo har ƙasa kaman ta Allah ta fice, harabar gidan tar kaman rana har ta isa babban parlorn na Baba prof dake gefe da shiga kofan sashen nashi da na matanshi, akwai hanya da ze kaika ɗakunan baccinshi kuma akwai wadda ze kaika cikin gidan nashi ta cikin parlorn.
Da sallama ta shiga, babban parlor ne me ɗauke da kujerun alfarma, carpet ne me taushi da tsananin kyau malale bisa parlorn duk girman parlorn Seda ya ɗauke tsab, ga kujerun alfarma na asalin royals, chan gefe shelf ne na littatafai har ba zasu kirgu ba.
A tsakiyar kujera ta ganshi zaune yana nazarin wani littafi, ta karasa kusa da kafafunshi ta zube tace
“Barka da dare baba”
Ya kalleta kan yace
“yauwa Fauziyya”
Fuskanshi ba alamun wasa yace
“me ya hana ki zuwa Islamiyya yau?”
Wuri wuri ta fara yi da idanu cikin in ina tace
“baba… Am dama.. Dama tunda na dawo makaranta ne na fara ciwon ciki shiyasa ban je ba”
Yace
“kin san Allah yayi mana hani da karya? Ya kuma kwaɗaita mana riƙe gaskiya a kowanni hali? Karki kasance cikin makaryata sbd daga furucinki zan iya cewa kai tsaye ba gaskiya kike faɗi ba, me yasa baki son karatu daga na boko har na Arabi?”
Kanta dake kasa ta girgiza tana forming hawaye tace
“kayi hakuri”
Yace
“na haƙura, na san ki da tsanar karya hakan yasa farar ɗaya na gane ki, Fauziyya karatu na da wani irin muhimmanci a rayuwarmu daga boko har arabi, barin ma arabi da ya zama dole wajibi a garemu mu nema, duk girmanka da tsufanka dole ne ka cigaba da neman ilimi sbd shi ze zama haske a rayuwar duniyarka da lahirarka, Allah SWT yace ku sanni kafin ku bauta mini idan har baku sanni ba to ta yaya Zaku bauta mini? Haka kuma Ayar farko da ta fara sauka da Kalmar ‘Iqra’ ta fara to meyasa bazaki dage wurin gyara gobenki ba?”
Nasiha ya cigaba da yi mata da misali da ayoyi da hadisai masu magana akan neman ilimi musamman Addini, tana shiru bayan ya gama ya sallameta ta miƙe ta fice ba wai don ta ɗauki ko abu guda da yace a cikin nasihohin shin ba.
Ya kamata ku san wani gida ne haka?
Wannan gida da mutane suka mata laƙabi kala kala wasu su ce
“GIDAN F” dalili kuwa duka yaran da suke cikin wannan gida sunansu daga F ya fara.
Wasu su ce
“GIDAN PROF KAKA” dalili kuwa babu wadda be san waye PROF Ibrahim KAKA ba a faɗin Nijeriya da ma kasashen ketare.
Dalilinshi ne ya sanya gabaɗaya unguwan tasu ta tashi daga ainihin sunanta ta koma
“UNGUWAN ƳAN BORNO”
Wannan unguwa na kafe ne a tsakiyar garin Yola na Adamawa state, zagaye yake da barebari Albarkacin dattijon arziki Baba Prof, asalin su ƴan garin Maiduguri ne na jahar Borno, daga uwa har uba barebari ne, a garin Borno Zulaikha wacce yara suke mata laƙabi da Jaddah ta haife su, su biyu ne rak wurin Mahaifinsu Abubakar Kaka, Baba prof wadda Asalin sunanshi Ibrahim Abubakar kaka da kuma ƙaninshi Sulaiman Abubakar Kaka.
Mahaifinsu mutum ne me nagarta kuma babban malami a jahar Borno, karatu da karantarwa gadon su ne sbd abunda suka taso suka samu Mahaifinsu da shi kenan, a wurinshi suka fara karatu na addini ya basu ilimi me nagarta musamman ibarahim da kullum karfe biyun dare haka ze tashe shi ya makala mishi redio yana sauraran karatuttukan malamai tun yana gyangyaɗi yana farkawa har ya dawo daga baya idan ze kwanta da kanshi ze cewa Mahaifinsu idan lokacin karatu yayi a tashe shi fa kar a manta.
Wani irin buɗewa kwakwalwanshi tayi da Alqur’ani wadda har ya iya qira’o’i da riwayoyi iri iri, a tsakanin ya shiga boko wadda be hana shi yin karatun shi ba, duba da iyayensu girma ya fara kama su gashi shine ɗan su na fari dayake Jaddah tana yawan haihuwa ne suna komawa, haka ta cigaba ko da bayan ta haifi Ibrahim ya tsaya.
Shi kaɗai ya buɗi ido ya gani a gidan hakan yasa ya ci alwashin gadar Mahaifinshi, wadda karantawar tashi wata rana yake fata ta zama sadakatul jariya ga Mahaifinshi, yana da shekaru goma sha biyu ya haddace Alqur’ani, hadda marar gargada bare kame kame, be dena karatun littatafai ba har ya shiga jss3 anan ne Jadda ta sake haihuwa bayan shekaru masu yawa inda ta haifi Sulaiman.
Shekarar su uku da Sulaiman ya samu scholarship sbd irin kwazo da ilimin shi da ya baza ko ina a cikin garin na Borno, har wasu state ɗin da idan be je musabaqa ba to ze je su debate, quiz, spelling bee da sauransu be kuma taɓa ɗaukan na biyu ba.
Madina yayiwa tsinke inda ya dage ya maida hankali yayi degree ɗinshi na farko har kuma lokacin be dena neman ilimin addini ba, bayan shekaru huɗu ya dawo Nijeria.
Alhamdulillah be bar iyayenshi haka ba ko da yake chan, ko da ya dawo ya cigaba da taimaka musu da karfinshi, yayinda Sulaiman ya fi maida hankali a boko Dukda dae ba laifi shima yana da iya nashi karatun na addini sede ba kaman Ibrahim ba.
A haka ya koma Madina yayo masters fannin kasuwanci, bayan ya dawo ya tafi America yayi degree ɗinshi na uku fannin halayya, anan ne ya dawo Nijeria lokacin Mahaifinsu na cikin hali na ciwo Sulaiman yana jami’a.
Wasa wasa Dr Ibrahim KAKA ya zama sananne a harkar musulunci, karantarwa da da’awa babu inda kafafunshi basu taka ba a Nijeriya, wani wurin har jifa suke sha, ruwa, rana, zafi, iska duk ya ƙare a kansu amma basu karaya ba.
A haka Allah ubangiji ya karɓi ran Mahaifinsu yana me alfahari da kaɗan da Allah ya bashi masu albarka sede kuma da takaicin rashin ganin auren Ibrahim sbd har lokacin be maida hankali kan mace ba, ina ka fito karatu ina zaka karantarwa, me kaci karatu, me ka sha karatu haka Ibrahim yake.
Sulaiman na Bautar ƙasa a Adamawa aka fara hare haren boko haram tashin farko kuma da matukar zafin su hakan yasa Sulaiman ya nemi Yayanshi Ibrahim da ya riga ya zame mishi uba sbd irin respect da yake bashi ya wuce na wa, akan su zo yola da Jaddah tunda apartment da shi baba prof ɗin ya kama mishi me girma ne.