Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Diddigar Kaya Complete Hausa Novel

Yace
“ni dae ki san yadda zaki yi, Haba sweetheart in taso tun daga Abuja in zo har Adamawa don ke kaɗai abinda zaki saka min da shi kenan? Ganinki ma yayi min wuya?”

Tace
“kayi hakuri! Zan san yadda za’a yi na fito”

Yace
“ko ke fa, ina Green land”

Tace “Toh”

Tsab ta shirya cikin wando jeans crazy da wani armless shirt, ta gyara gashinta sossai ta feshe jikinta da turaruka kan ta ɗauki karamin jacket ta ɗaura saman Rigan ta zumbula hijab ta fito, duk an shiga sallar isha masallaci ga muryar Faizan na tashi cikin nataatsiyar karatunshin nan haka ta fice babu wadda ya lura.

Napep ta tara tayi Jimeta, kai tsaye ɗakin da ya faɗa mata ta wuce, tayi knock ya zo ya buɗe mata tana shigowa ya rungumeta
“oh my babe, I really miss you wlh”

Ta zame tana furta
“miss you more”

A kujera ta zauna tana zare hijab ɗin jikinta, shishar da yake sha ya mastar mata dashi gabanta ba tare da yace komai ba.

Ta karɓa ta ɗan zuƙa kan tace
“Wow the flavor is giving.. Wanne da wanne ka Haɗa?”

Ya mata bayani yana karawa da
“karki damu ba wai bugarwa yake ba kawai dae zaki jiki fresh out of ko wani irin tunani na damuwa ko kunci”

Tace
“kaman ka san bana cikin daaɗin rai wai yarinyar nan Fatima tun fa da ta sa na bar sashenmu ban sake mata magana ba haka itama, shine yau na shiga wurin Ammi ina fitowa kawai naji tace min wai ina kwana Fauxa, ashar na lailaya mata kawai na ji rankwashe babu faɗar da Baba Alhj be min ba, harda zata bar mini gidan in jika a ruwa in sha, wlh na tsani abu da munafuki in ba don ta kalli baban ba na tabbatar haka zata goge ni mu wuce juna”

Yace
“Ki kwantar da hankalinki ina ce jibi ne zata bar miki gidan kowa ya huta?”

Kai ta gyaɗa tace
“bana fata har abada mu sake haduwa in ta tafi kai daga ita har mijin nata ma”

Tana sha ne take ta wannan masifar, lallaɓata yayi tayi da kalamai, daga karshe se gata jikinshi dukda yadda take nuna mai bata so, haka yayi ta rinjayarta, da gasken gaske shedan ke shirin tasiri wurin, tayi saurin mikewa tace
“bari na zo na tafi kar a kula bana gida”

Yace
“mu je dae mu ɗan ci abinci kan ki wuce ko?”

Hijab ta dauka yayi saurin karɓa ya ajiye yace
“me haka? A ganni ni Zubair turaki dake da wannan zumbuleliyar hijabin? Inaaa”

Gashinta ya gyara mata ya riƙe hannunta suka fito, da gaske Fauza na da kyaun fusgan hankalin jama’a, shigar ta kuma ya sa kowa ya kalleta se ya sake kallo, kaman ba ƴar musulma ba.

Restaurant suka shiga, yayi musu order har da su fine whiskey, sun yi nisa a cin abincin kaman daga sama taji wata razananniyar murya ta Furta

“FAUZIYYA!!!”

DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba

Karku sake a baku labari.

Gureenjoh

13

Kamar yadda rugugin aradu ke sauƙa haka sunan nata ya saukar mata barin ma a sadda idanunta suka gane mata wadda ya ambaci sunan, wani irin razana da tsorata tayi har bata san ta miƙe kan kafafunta ba, sake ambatar sunan nata da yayi da irin yadda jikinta ke rawa yasa Zubair mikewa yace
“wai waye wannan ɗin ne?”

Takaici ya hana Faizan cewa komai, wani irin fisga yayi mata da saida ta buge da jikinshi ya janye ta suka yi waje saboda idanu dake kansu, motar shi ya karasa ya buɗe ya cillata ciki har Seda ta bugu ta saki kara, be damu ba ya sawa motar key, ya juya ya koma cikin hotel ɗin Zubair dake tsaye yana kallansu zafin ran dake kan fuskan Faizan kaɗai ya hanashi fuskantar shi Dukda kasancewar shi shima namijin ne, amma an ce wargi ma wuri yake samu.

Shi kuwa Faizan wurin abokananshi ya nufa dama abunda ya kawo shi hotel ɗin kenan, abokananshi da suka zo ɗaurin aure duk a hotel ɗin ya kama musu masauki shine ya zo ya ɗan rage dare yaji kuma if they are comfortable with the suits se idanunshi suka mishi mummunar gani, don mummunar gani zai ce dama ya riga ya ɗaura alamar tambaya akan wannan yarinya don fitsararta ma kaɗai ya ishi ta fara bin maza, in ba ta san maza ba babu yadda za’a yi ta bushe idanunta akan kowa har uban da ya kawo ta duniya, amma bata yi a wurin da ya kamata ba don yau kakkanninta zata ci.

Runtse idanunta tayi gam gam, gumi na tsatsafo mata na laifin da ta aikata da kuma na rufe ta a motar da yayi babu iska don be sauke window ba, dunkulewa tayi wuri guda kaman sardine ga kanta dake sarawa na abun maye da ta sha wadda ta sha ne don ya ce mata ba wani bugarwa yake yi ba.

Yau dae ta san me kwatarta a gidansu se Allah, dama an ce kwana 99 na ɓarawo kwana 1 na me kaya yau dubun ta ya cika, ta maimaita innalillahi wainna ilahi rajiun ya fi cikin chasbi.

Saida ya shafe mintuna sama da hamsin kan ya fito lokacin har bata iya jan numfashi me kyau don azabar zafi, wayanta ne ya fara ruri, ɗauka tayi tace

“Zubair ka kasheni! Na shiga uku”

Yace
“Babe wanene wannan ɗin? Ya za’ayi ya barki cikin mota window a dage mota a rufe?”

Se a lokacin zazzafar hawaye ya sauko mata tace
“yayana ne! Kuma wallahi baya ƙaunata ko na sulen kwabo ba rufamin asiri zai yi ba, kashina ya bushe..”

“Yaya zamu yi kenan babe? Ko na saka hukuma?”

Ta zaro idanunta gabaɗaya tace
“whattt? Ka rufamin asiri ka barni da abunda ka ja mini Zubair… Na shiga uku! Gashinan zuwa.”
Tana kai nan ta kashe wayar tare da makalewa a cinyoyinta.

A jikin motar ya tsaya ya fara kiran Baba prof.

Bayan ya ɗauka cikin ladabi yace
“Baba akwai wata gagarumar matsala ce da ta tunkaro rayuwarmu wadda dole ce ta sa zan bayyana muku don idan na rufe ma na ha’inceku”

Baba prof yace
“Kowani bawa da kalar tashi kaddarar da jarabawar, ruwanmu ne mu karɓa ruwanmu ne kar mu karɓa amma idan muka karɓar mun cika wani sashe ne na imaninmu kaman yadda in muka saɓa ya zama kaman saɓawa ubangiji…. Menene?”

Yace
“baba ku zauna a parlornka ku jirani don fa idan na faɗa a waya ba lallai na gamsar da ku ba.”

Kashe wayan kawai baba yayi dama yana zaune da Baba Alhj da Jaddah ne, yana sauke wayar ma se ga mammi ta kawo musu tea kasancewar su akwai kaunar sha’i musamman wadda yaji kayan haɗi.

“Kai da waye haka? Allah ya sa dae lafiya”
Jadda tayi tambayar.

Cikin nazarin abunda ze faru yace
“Faizan ne kuma dae kaman ba lafiya ba”

Tea ɗin Mammi ta zuzzuba ta miƙawa kowa, suka fara sha suna ɗan tattauna abunda ze iya kasancewa don duk tsumayin abunda Faizan ke tafe dashi suke.

Parking motar da aka yi dab kofar baba prof ɗin shi ya sa duk suka maida hankali kan kofar gabansu na faɗi, kaman an cillo kayan wanki haka ya watso ta ta faɗi a ƙasa gashinta ya rufe mata fuska, duk tsaye suka miƙe suna kallonta.

“Faizan menene hakan? Wacece wannan ɗin”

Runtse idanu baba Alhj yayi ya sake buɗewa jiri na shirin yarda shi yace
“Fauziyya???”

Duk kallonta suka yi daidai lokacin ta miƙe tsaye tare da janye gashinta tace
“Na’am”

Da gudu Farhan da shigowanshi kenan ya tare Baba Alhj dake shirin faɗuwa amma ya fusge yayi kanta, ya fara dukanta yana cewa
“ni kike amsawa idanu a sama don tsaurin ido? Fauziyya kasheni kike son yi ki huta? A ina ya samo ki? Kalar tarbiyar shigar da muka koya miki kenan? Innalillahi wainna ilahi rajiun..!!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected