Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Da sauri ta fito tana layi, dishi dishi take ganin mammi tsaye tana kwala kiran sunanta, Sam bata san ma da wani a gefen mammin ba ta de ji tana cewa
“kama min ita… Yi sauri kama min ita, innalillahi me zan gani haka?”
Yanke jiki tayi sbd yadda duk garkuwar jikinta suka karaya suka gaza ɗaukar gangar jikinta a hannun mutum ta ji ta kan ta karasa ficewa hayyacinta.
DIDDIGAR ƘAYA…(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira ɗari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
15
Yana durkushe kan kafan shi ɗaya, ɗayar kuma kanta ne a kai hannunshi na patting kumatunta yana cewa
“ke! Ke!!”
Sede ina bata ma san yana yi ba.
Mammi tace
“yi sauri ɗauko ta mu tafi asibiti Faizan Farhan na da hannu a wannan abun kuma wallahi se sun ga bacin rai da basu taɓa gani ba, wani irin shashanci ne wannan?”
Da sauri ya ɗauke ta yadda yaga ran mammi ya ɓaci be so ta bi su asibitin ba don yanzu suka dawo sbd kafar ta da ya matsanta mata se kuma suka tarar da wannan, haka ta ƙi shiga gida suka juya asibitin tana kiran Baba Prof a waya.
Ba irin faɗan da likitoci basu yi ba, aka samu aka shawo kanta aka yi mata dressing ciwukanta, lokacin baba prof da Baba Alhj da jadda suka iso.
Tana kwance kaman wata innocent, sossai Jaddah ta zub da hawaye tana zagin su Farhan inda take shiga ba ta nan take fita ba, Baba Alhj bazaka ce ya wani damu ba haka nan oga kwata kwata Faizan tunda nurses suka karɓeta ya samu wuri yayi zaman shi ba don mammi da tayi magana ba ma wayanshi yake ta operating, Baba prof ne yace
Duk su koma a kawo ko zaliha ne ta kwana da ita tunda allurar da aka mata ze jima be saketa ba.
Tun suna kan hanya ya kira Farhan da Faraj akan su same shi parlornshi, suna isowa duka nan suka yi, tun kan su zauna babu zato ba tsammani ya saukewa kowannensu zazzafan mari, duk a razane suke Kallonshi ranshi sossai ya ɓaci yace
“baku da hankali ne? Kuna Tunanin duk rashin hankalin Fauza ya kai wadda kuka yi? Irin wannan duka ko a hannun hukuma iyaka tana mace in kuka yi mata illa fa? Ina ce seda na ce muku kar kowa ya taɓa ta sbd abunda ya faru? Kun tambayi dalilinta? Ko don tana da yawan neman tsokana se aka ce a komai ma ita ke da laifi?”
Babu wadda ya taɓa ganinshi yana faɗa haka, yayi sossai da sossai sbd yadda ya ga Fauxa, jadda ma ta karɓa harda Allah ya isa tayi musu, mammi ma Seda tayi nata sossai ta kuma ɗauki fushi da dukkansu, Faizan dae da Baba Alhj en kallo suka zama se daga baya baba Alhj yayi ta ba jadda hakuri.
Tace
“me ya faru ɗazu ɗin?”
Baba prof da ya zauna ya ɗan yi shiru yana Samarwa kanshi natsuwa kan yace a tausashe
“Duk abunda ya farun laifin Fauziyya kaɗan ne Dukda dae ni shi ya fi daga min hankali ba wani faɗar da suka yi ba, da farko dae ni na janyo don na san halin Fauxa na Haɗata da wata yarinyar makota a nan farkon layin ganin kullum tana wahalan samun abun hawa, to wai Fauziyyar sau biyu bata rubuta paper ba tana fita wani ke rubuta mata a madadinta, to ranan sai bata dawo da wuri ba shine yarinyar ta fara zagin ta har ta kai kaina se fauziyyar ta fasa mata baki a mota kaman yadda driver ya bada nashi bayanin, to bayan nan ne suka haɗu da ƙawayen ta wai zasu dake ta shine tayi musu dukan kawo wuƙa iyayensu kuma suka kawo min hukuma sun kuma aibata ni sun yi min kazafi wadda na Barsu da Allah zasu bada shedar shi ranar gobe”
Shiru parlorn ya ɗauka kan Jaddah da ta zabga tagumi tace
“yau na shiga uku da yarinyar nan, to ina take zuwa? Da wa take fita kuma?”
Baba prof ya kalli babanta da yayi shiru hawaye na shirin zuba mishi yace
“kar ka yi mata kuka Sulaiman, da ni da kai duk ɗaya ne haka yaranmu don an zo kamani a madadin mahaifin Fauziyya ba’a yi kuskure ba, a yinin yau na yanke hukunci akan Fauziyya wadda nake so duk ku sheda, bana bukatar shawarar kowa bayan na mahaifiyata, na yanke nan da watanni biyu zan ɗaurawa Fauziyya Aure da Faizan…”
Ɗib haka parlorn ya ɗau shiru, Faizan dae yi yayi kaman be ji ba don ya san kila karan jirgi ya fara taɓa mishi kunnen shiyasa ba ya ji da kyau, ko a imagination baze taɓa kawo wannan hadi ba bare a zahirin gaskiya.
Mammi tace
“Allah ya sanya Alkhairi, wannan haɗi shine daidai”
Baba Alhj yace
“A’a yaya, ya zaka fara wannan kwamachalar? Taya zaka fara Haɗa nitsaste kaman Faizan da fits….”
“Akul Sulaiman, in dae ba kana so ka nuna min bani na haifi Fauziyya bane babu ruwanka naka idanu, Faizan na ba Fauziyya kuma ya riga ya zauna..”
Ba don kar ace yayi rashin kunya ba da se ya tambayi baba wai wani Faizan ne yake referring to, kanshi gabaɗaya ya dau hayaƙi in kuwa baba yayi hakan ba karamin cutar shi yayi ba, me ze yi da sauran wasu? Me ze yi da ƴar giya?
Jaddah sossai ta nuna amincewarta da shawaran a haka suka tsayar kan su Faraj suka yi ta ba baba hakuri yace ba shi zasu ba wa ba Fauza zasu ba kuma biyar da Faizan ya kashe a asibiti su tabbatar sun biya shi, a haka aka watse aka bar Faizan a zaune a wurin.
Seda baba ya kula da Sam kaman baya hayyacinshi ne ya tashi yaje ya ɗibo ruwa masu sanyi ya kawo mishi
“karɓi ka sha!”
Ya kalli kofin kan ya ɗaga ya kalli baba da rinannun idanunshi yace
“na koshi”
Baba yace
“karɓi mana ai ruwa rayuwa ne”
Karɓa yayi ya kafa kai ya shanye tas kan ya ɗago ya sake kallon baban, murmushi shimfiɗe a fuskanshi yace
“karka ɗaga hankalinka Faizan, a yadda na sanka da natsuwa, kawaici da hangen nesa kaman mahaifiyarka ina so ka cigaba a haka, na zaɓa ma Fauziyya Kaine sbd Kai ne Allah ya sha nuna min a duk istikhara na, da kai hankalina ya fi kwanciya, na san bazaka taɓa tozarta abinda na baka ba”
Faizan yayi shiru kaman ruwa ya cinye shi
“baba fa watana kwata kwata uku ne da aure”
Yace
“na sani, Fatima da mahaifiyarta masu fahimta ne na san zasu fahimta”
“baba mahaifiyarta bata taɓa ƙaunata ba, ko gaisuwata bata taɓa buɗe baki ta amsa ba”
Yace
“na sani wannan duk ba wani abu bane ba lallai kowa ya so ka a duniya ba, daga kan Annabawa har Sahabai zuwa malamai babu wadda bashi da maƙiya”
Yace
“Baba Fauziyya da Fatima basu taɓa shiri ba taya zan iya haɗe kansu su zamar min tsintsiya madaurinki daya kaman yadda ka zamarwa iyalan ka?”
Yace
“kai ɗin jarumin namiji ne wannan me sauƙi ne a gareka, ina me tabbatar maka zaka yi alfahari da wannan haɗi watarana, ka je ka kwanta karka yawaita tunani instead ka raya daren idan ba zaɓin Allah ba ce se ka ga Allah ya musanya mata da alkhairi in kuma ka ga an ɗaura to kaddarar ku a sarƙe take da juna tun fil azaal”
Mikewa yayi yace
“Na gode, se da safe”
A ladabce kan ya juya ya fice.
Wannan dare haka ya zamarwa Faizan daren tashin hankali don ya kwana yana rokon Allah akan wannan abunda baba ke shirin tinkarar rayuwarshi dashi, duk mazan gidan a rasa wadda za’a lakabawa wannan fitananniyar yarinyar se shi? Yayi nadamar zuwa yola a ranar ya fi sau dubu kila da be zo ba baba be ganshi ba da wani ya zaɓa ya baiwa ba shi ba.