Diddigar Kaya Complete Hausa Novel
Karku sake a baku labari.
Gureenjoh
DƘ
19
“Ayya don Allah yaaaya su bar mana ita anan pls!”
Yadda tayi maganar yasa dole ya kafeta da idanu yana kallonta, ta wani narke fuska se yaji wani abu ya mitsini zuciyarsa, ya lumshe idanunsa ya buɗe.
“Da nan ɗin da wurinsu duk ɗaya ne tunda mu ma iyayenta ne”
Ya faɗa yana zama, da kallo ta bishi babu laifi ta fahimci guy ɗin ta ko ina ya haɗu, komai nasa me kyau ne, kuma ko wani irin sutura ya sa ta kan zauna daidai da tsarin hallitarsa, ɗauke kai tayi ganin ze kalleta ta dubi husna tace
“zamu zauna ko husna?”
Kai yarinyar da bata wuce six years ba ta gyaɗa tana dariya.
Su fadyaa ma fuskansu cike da murmushi Alhamdulillah ko gobe ne yanzu kam zasu iya tafiyar su, Gaisawa suka yi da Yayan nasu, kiran sallahn azahar ya sa mazan suka fice sallah yayinda su kuma suka shige ɗakinta bayan sun yi sallah fadyaa ta dube ta tace
“Fauza ba wani matsala ko?”
Fauxa ta ɗan yi kasa da kai kan ta ɗago tace
“ya fadyaa dama can kin san ni da Fatima Bama shiri to dae har yanzu bata sauya zani ba, ta ɓangaren shi kam ba wani matsala, matsala ta ɗaya ne”
“Uhm”
Fadyaa ta faɗa jin ta ɗan yi shiru
“me yasa nake jin Ammi ta sauya min daga wacce na sani? Meyasa bata so na zauna lafiya a gidan nan kaman yadda kowa ke buri? Duk yadda zan duba na kasa fahimtarta Ya fadyaa”
Shiru fadyaa tayi na mintuna har saida Fauza ta sake kiran sunanta ganin fuskanta ya bayyana damuwa tace
“Fauza babu abunda zan iya ce miki saide kiyi haƙuri da ita, uwa ta wuce gaban wasa amma ina me tabbatar miki ni kaina tun daga randa na amsa auren ya Faahim Ammi bata sake sakarmin fuska kaman yadda take yiwa su Fadeela ba, ban sake jin daaɗinta a matsayin uwa ba, ban sani ba ko tsanar da take yiwa Mammi da ahalinta ne ya shafemu ko yaya”
Ajiyar zuciya Fauza ta sauke gaskiya halayyar Amminta na ɗazu ya dameta, jin motsin mazan yasa suka miƙe suka fito.
Yana kallonta yace
“Fatima fa?”
Tace
“bari na duba ta”
Karasawa kofan ta tayi tayi sallama shiru tayi knocking sau biyu shiru, juyowa tayi ta kalleshi shima ita yake kallo kan ta murɗa kofan da nufin shiga sede a rufe yake ruff da makulli.
“Baki faɗa mata sakona bane?”
Tace
“ban ji motsinta bane shiyasa”
Wayanshi ya fiddo yana shirin kiran Fatiman yayinda ita kuma tayi dining ta fara kwaso abincin tana kawo su tsakiyar parlor, gabanshi ne ya faɗi kardae ita ce ta kwaba musu abunda zasu ci? Ai da bari ma tayi ya saya a waje tunda bata samu Fatima ba da jagwalgwalontan nan. Amma kuma ina Fatima ta tafi ba tare da ta sanar dashi ba?.
Jin wayan na shiga ya sa ya tashi ya wuce ɗakin shi don kar su ji tambayar da ze yiwa Fatiman sanin ba girman shi bane taya za’a yi mace ta fita babu izinin miji?
Ita kuwa bayan ta gama ta kwaso plates da spoons da forks haɗe da tissue ta kawo, babban warmer me ɗauke da pineapple rice ɗin ta buɗe a take kamshi ya cika su nan ta ɗauki plate zata fara serving kawai taji hannunsa mai azabar sanyi da taushi cikin nata.
A razane ta ɗago se suka Haɗa idanu ya kauda kai yana zare serving spoon ɗin yace
“kama wani let me help with this”
Janyewa tayi tana jinta wani iri, basarwa yayi ya fara serving yana kawowa Faahim Hirar aikinshi da kusan akan zancen jirgi ne tunda shi Sojan sama ne.
Miƙewa tayi ta sauka kasa ta samo silver tray me Adon gold ta fidda zobon da ta yi ta ɗaura a kai ta jera cups ɗin jug ɗin a gefen tray ɗin kan ta dawo ta ajiye musu fadyaa na mata sannu.
Kifin ta yaye wa foil paper da ta Naɗesu dashi, shi kuma yana sanyawa kowa pepper chicken ɗin, fadyaa na kallon su da burgewa don ba karamin kyau suka mata a taren ba.
Bismillah yayi duk suka sauko, zuciyarshi dae a tsinke kar su sha kunya ya ɗibo abincin a spoon ya kai bakinshi.
Lumshe idanu yayi se ya buɗe a kanta maganganun su da su Faisal ɗazu a office ɗin Jafar ne ya dawo mishi.
Bayan ya sauke wayanshi a sadda ya faɗa mata su fadyaa na zuwa Faisal yayi dariya yana cewa
“kaga mijin mata biyu cikin wata biyar ba… Kai fa kana morewa ba’a fita a angonci ba an sake dulmiyawa sabuwa dalll me sirrin ne?”
Tsaki yayi yana furta
“kanku ake ji”
Jafar yace
“kaima za’a ji naka ne a sadda ka shiga hannun Fauza”
Wani dariya yayi na baka da hankali yana dawo da kwakwalwar shi baya wurin Tunanin suffar ta da har za’a ji kanshi, a ganin da ya mata na ɗakinshi, da ganin da yayi mata randa aka kawo ta ya san kwarai tana da cikakkiyar siffa da sura, abunda kuma ke kashe shi ba ƙarya sune idanunta waenda baya jurar kallon cikinsu ba tare da yaji wani yanayi da be san menene ba, ba karya yarinya ce me cikakkiyar suffa da daradaran idanu, hotonta rungume da Zubair a elevator ne ya dawo mishi wadda ya saka shi saurin kau da Tunaninta yana sakin tsiririn tsaki.
“Ya dae angon mata biyu? Yaushe ne za’a gayyacemu cin abinci ne kaga dae tun kawo Fatima kake mana haka haka, matar Faisal har ta haihu muna gari ɗaya baka bar matarka ta zo ba”
Cewar Jafar
“sannan ka manta Fatima tana rashin lafiya ne? Bari na zo na tafi kar baƙin mu su zo bana nan, amma karku damu kanku in shaa Allah nan kusa zan gayyaceku cin abincin ku maida kwalamarku Mayu kawai…”
Yana kai nan ya nufi kofa
Dariya suke yi Faisal yace
“eh mun ji, wlh ko me zaka faɗa se mun zo mun kwashi gara ah to”
Yana murmushin zancen ya karasa mota ya shiga ya dawo gidan.
Boyeyyen ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take ta ba husna abinci a baki suna hira da dariya da yarinyar, ta bashi tsananin mamaki guda biyu a yau
Na farko be taɓa kawo zata girka abincin da ya kai wannan daaɗi ba don ze iya rantsuwa bayan abincin mammi be taɓa cin abinci me daaɗin wannan ba, se kuma abu na biyu yadda ta tarbi su Faahim be taɓa zaton tana son mutane har ta ja su a jiki haka ba duba da yadda duk inda ta zauna se an samu hatsaniya da ita, kannenta karan kansu ba son zama kusa da ita suke ba don masifa da saurin hannu amma ji ta yadda take yi da su fadyaa ko don ta kwana biyu bata ga mutane bane?
Har suka gama cin abincin suka cika cikinsu da zobo be Daena mamaki ba, tattare kayan suke ita da fadyaa da ta mike tana taya ta suka yi kasa suka Barsu su biyu, don yaran sun biyo bayansu, wanke wanke Fauza ke yi fadyaa na daurayewa suna ƴar hira tsakaninsu.
Sun gama suna shirin haurawa saman kenan se ga Fatima, sake fuska tayi tace
“ya fadyaa kune a gidan ashe?”
Fadyaa tace
“eh wlh Fatima mun zo kin fita”
“eh na ɗan je na ga doctor na ne, Alhamdulillah kuma da sakamako me kyau na dawo”
Fadyaa na murmushi tace
“masha Allah, Allah ya jishe mu alkhairi”
Dukda ta so Fadyan ta tambayeta menene don ciki ne da ita na sati biyu kachal amma har ta bazawa mutane tana faɗin a taya ta da Adu’a, wai ko Adu’a ne ba’a yiwa cikin yasa baya zama ga saurin conceiving da take dashi.
Duk haurowa suka yi kanzil be Haɗa su da fauza ba, ta gaida Faahim ta shiga cikin su ganin Faizan be nuna komai a fuska kaman yadda ya Rufeta da faɗa a waya ba.
Har suka yi la’asar a gidan still Fauza taje ta dafo musu shayi sak irin wadda mammi kan yi mishi itama kuma wurin jadda ta koya don Baba prof na matukar so kaman yadda shima yake so, be taɓa sanin ta iya something like this ba, ya sha shayin sossai don kusan abunda yake matukar kewa kenan a duk sadda aka ce yayi nisa da yola.