AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Numfashi bullet ya sauke tareda Dan gyara tsayuwansa yace

“Ranka ya Dade haryanxu dai ban tabbatarda abinda yake tsakaninsu ba Amma dai Dr Dee din likitan asibitin mahaukata ne kaman yanda kake zargi tin farko Kuma Ina kyautata zaton acan ne Ameenatou take hakama Ina kyautata zaton duk da JEEY Baya kasar shine ya daukesa daga asibitin”

Wani murmushin kwanciyan hankali Mam ya sake Yana dauke kallansa daga bullet yace

“Sunan Dr Dee Dana Gani a kallo Daya daga wayar Lameenu a ranar Daya kira ban kwana ba na San likitan asibitin mahaukata ne Kuma daga ranar Babu abinda yake faruwa a cikin asibitin Wanda ban saniba ciki harda JAMAAL dayake asibitin,

Akwai Abu Daya danake son Sani tak Wanda ya Saka Lameenu fara yin Abu batareda sanina,
Dole akwai abinda ya jagoranci Hakan,dole akwai abinda yayi Daya basa qwarin gwiwan Hakan hakama akwai abinda dole dole yasaka BB zaban aikata Hakan batareda shakkan idan ya sani Mai zai biyo Baya ba,
Wannan abin nakeson sani koma Menene shi,

Ta bangaren Ameenatou Omer Jden Kuma inason ka tabbatarda Jamaal yasan komai gameda abinda ya faru asibitin da baya nan sbd inason ta wannan bangaren Lameenu yasan jinina jininane da gaske dan kuwa da alama ya manta JAMAAL ni ya dauko sak ba kamar haroon bane daya dauko sanyin halin uwarsa,

Idan zai iya yi a boye to tabbas zan Saka ido na Kalli yanda JAMAAL zai kifarmun dashi batareda na Bata lokacina ba kafin na gama abinda yake gabana na waiwayosa.”

Numfashi bullet ya sauke Yana gyara tsayuwansa yace

“JEEY ya gama sanin komai kaman yanda kace a sirrance”

Gyada Kai Mam yayi tareda sallamansa suka fice daga gidan,

Saida sukai kusan awa da fita kafin bullet din ya fice daga gidan ya tafiyarsa.

Kai tsaye office suka nufa suna Isa Dad Lameenu ma ya fito zuwa office din Mam din da duk a tsarge yake da yanda labarin mutuwan idan tajewa Mam din da Kuma yanda zai daukesa Kokuma lura da wata sheda ko alaman kwayoyinsu ne Akai amfani dasu.

Tare suka Isa office din Mam din suna gaisawa da tattaunawa akan tafiyan da Mam din zaiyi a satin zuwa Greece,

Mam a natse yake sake yiwa Lameenu bayanin yanda zasuyi da baqinsu da suka iso ranar Yana qarawa da zancen a tabbatarda an shigowa da sauran kayansu daga Ashalawa.

Daddy lameenu Dake tsarge ganin Babu alaman ma Mam ko a labari yaji ko ganin mutuwan Dr Dee take ya sake Shima Suka shiga harkokin gabansu gadan gadan kawai ba damuwa ko tinanin komai.
#MAMUH#
#AMEENATOU SEELAH
#JEEY SEELAH
#MAM SEELAH
#LAM SEELAH
#OMAR SEEELAH
#THE SEELAHS

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
75
Dr JEEY kuwa sai kusan karfe daya ya fito daga bedroom dinsa a shirye cikin qananun kayan Paul Smith navy blue marasa nauyi kafafunsa sanye da slippers wayarsace a hannunsa sai alokacin ya kunnata yake ganin mutuwar dr Dee wanda ta sakasa zaunawa kan dining din da zaici abinci yana karanta sakon da kyau.

Siddeeq Dake dayan bedroom din Yana Wani conference meeting Shima lokacin sallah ne yasa shi sallama dasu yayi Sallah ya fito Jin motsin fitowan JEEY din.

Qarasowa yayi gurinda JEEY din yake zaune bayan ya ajiye wayarsa ya dago idanuwansa da sukai fes sun sake sosai ba kaman yanda ya dawo gidanba.

“Barka da fitowa Dr”

“Barka,thank you,
Dr Dee a binciken da kayi a rayuwansa na Baya ya taba Shan kwayoyi ne Daman??

“No Bai taba ba and banajin zaiyi Hakan da manyancinsa,
Amma dai zan bincika da kyau naji sbd idan har kashesa Akai to tabbas Hakan nada alaqa da sauyin gurin da kasa Akai masa Dan yaje ga Wanda yakewa aiki yayi magana a mayar dashi Muji ko waye ta hanyar Hakan so Ina Saka ran ko daga inane sun tabbatarda suna Saka bakin a Maidasa zaa San daga Ina zancen ta fito.”

Sake kallan Hoton gawar dr Dee din da siddeeq ya ajiye masa yayi Ya qurawa jinin hancinsa da kunnuwansa ido Yana tino ranar daya ga Dan uwansa a cikin irin wannan halin a lokacinda suka samesa dinnan batareda sunsan meya samesa ba harya kusan mutuwa.

Wannan tinanin ne Daya fado masa ya Sakasa daukan iPad din Yana sake kallan Hoton gawar da kyau.

Shiru yayi tsawon mintina kafin ya dago ya Kalli siddeeq yace

“Ko Ina ake siyar da wannan qwayoyin inasonsu,
Inason sanin Wani abu a kansu,
Kuma zanyi gwajinsu akan Wanda ya dace ayi gwajinsu dasu,
Ko nawa ake siyanta a nemomin ita Ina buqatan”

“In 1 week inshallah”siddeeq ya fada Yana daukan iPad din Shima ya zubawa gawan da hoton kwayoyin ido Yana tinanin da JEEY keyi hakama Yana shakkar Wanda tsautsayi zai Saka ayi gwajinsu dashi ta bangare Daya Kuma Bai sanar masa yaga su BB a anguwan da aka rubuta a labarin an tsinta gawan dr Dee dinba sbd son bincikensa ya gano abinda zai baqa jeey din cikakkiyar bayani.

Abinci sukaci a dining din Wanda shine breakfast dinsa Kuma lunch Dan shi da wani abincin Se dare Kuma ko yamma.

Suna gamawa Poland ya zauna a palon ya kira yaji bayanin komai tareda duba Mum dinsa sun jima sosai kafin yayi sallama dasu ya kashe.

Sai la’asar nayi suka fice sallah daga can JEEY Kai tsaye asibitin ya wuce sbd sister Ashley data kirasa Ameenatou din taqi cin komai fushi takeyi tin safen.

Yana Isa Kai tsaye office dinsa ya wuce ya ajiye key na motansa da laptop ya fito ya nufi gurin patients.

Ya Duba kusan patients biyar tareda Yan rubuce Rubuce a files nasu kafin ya nufi dakinta.

Tin a kofan dakin dayake Bude yake jiyo rarrashin da sister Ashley ke mata akan ta tsaya a gyara kanta Amma Sam taqi saima Neman rikice mata datake Neman yi tana Kiran sunan Haroon shi kadai takeson Gani.

Tsayuwa yayi daga bakin Kofar Yana kallanta a kame cikin nutsuwa,

Itace tafara ganinsa a bakin Kofar a tsaye Yana kallanta da idanuwansa Dake kasheta duk da Bata hayyacinta.

Zubawa kofan ido tayi tana ture hannun sister Ashley daga kanta ta ziro kafafunta zata sauko kasa ya girgiza mata Kai ahankali Yana kallan kafafunta Dake farare fes sbd rashin yawo da rashin qazanta harma da rashin lalle ga uwa Uba yawo da takarmi har acikin daki.

Kallan kafafunta Daya nuna mata da idanuwansa tayi tana kokarin cigaba da saukowa sister Ashley tayi saurin tareta tana juyawa kofan ta Kallesa tana cewa

“Barka da zuwa Dr”

Gyada Kai yayi Yana cewa “thank you”

Riqeta tayi Amma Sam taqi bari a Saka takarmi saukowa kawai takeson yi Dan haka dole ya Tako a natse ya iso cikin dakin har bakin gadon ya tsaya a kanta kafin yayi motsin komai ta miqe masa hannunta.

Numfashi ya sauke ahankali kafin ya Ciro hannunsa Dake cikin aljihun wandonsa ya miqa a natse ya kama mata din sai alokacin ta sake Wani murmushin da tinda yake Bai taba Gani daga gareta ba.

Murmushinta yake kalla hannunsa na riqe da nata sai a lokacin ta Kalli sister Ashley tace

“Ashley,Ameenatou’s Haroon”

Sister Ashley ce tayi saurin kallanta kafin ta Kalli Dr JEEY din Wanda tamkar ma baiji abinda ta fada din ba hannunsa Daya ya dago Yana kallan time din wata tsadaddiyar ogogon hannunsa sbd magrib data kusa sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected