AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Bedroom dinsa ya wuce Kai tsaye ya fada wanka zuciyarsa na samun nutsuwan dayake buqata wadda ya rasa a kwanakin sbd rigimansa da Dad.

Haroon ma Dayan dakin ya nufa wankan yayi ya fito Kai tsaye ya nufi bedroom din Jamaal ya Bude closet dinsa ya dauko kayan bacci black ya Saka ya fito yaje kwanta,sai a lokacin Jamaal din ya fito ya shirya cikin fararen kayan bacci ya kwanta tareda dauko wayarsa Yana Kiran fadila a natse.

*******Amincewan Dad shine babban abinda yayiwa kowa dadi da farin ciki har bangaren su fadilan wadda batada wani qwari ko kuzari Amma tayi murna sosai.

Babu Bata lokaci Jamaal ya buqaci ayi auren Dan kuwa a yanda yake sane da ciwonta yayi tsanani sosai Dan kuwa yanzu lungs dinta sunyi Nisa sosai oxygen ma Neman gagara riqesu yakeyi Dan haka yake buqatan auren zai fita da ita yaga wasu likitocin da zasu duba case dinta sosai tareda shi.

Bai sanarwa kowa ba har iyayenta matsalanta yayi muni sedai daga su har fadilan jikinsu yayi sanyi sosai Dan sosai kullum take sake zama weak numfashin ma ahankali ahankali take iya shaqarsa.

Hakanan suke lallabawa Dan asamu ayi bikin,

Fadila da kanta ta cire Rai daga rayuwa a yanzu Amma dai babban fata da burinta shine ta samu zama matar Jamaal kafin Allah ya dauki ranta,
Tanason cika masa burinsa na son ganinta a matsayin matarsa mallakinta kafin ta koma ga Allah Dan haka take fata Dan rokon Allah ya Bata qwari da qarin kwanakin da zata cika masa wannan burin.

Su kansu iyayenta duk yanda jikinsu yayi sanyi ga yanayinta a yanzu ta Basu qwarin gwiwan karban kaddararsu,
Suma a yanzu fatansu ta zama matar Jamaal kafin Allah ya dauki ranta
Idan hakan ta faru zasuyi farin ciki ko bayan ranta sbd burinta ya cika Kuma Jamaal ya zama sirikinsu baiyi musu wahalar banza a banza ba.

Jamaal kwanakin auren na sake kusantowa Amma kwata kwata kansa ya dauki zafi baida lokacin komai bayan tattaunawa da Neman yanda zaiyi ya kawowa fadilan sauki ta samu shakar numfashi me dadi da nutsuwa Dan lamarin yafara karya masa zuciya Amma Koda zaiyi yawon duniya da kasashe ne zai Nemo mata lafiya idan har Allah yayi zata warke din.

Kwanaki na sake kusantowa na auren fadila na sake zama weak sosai Dan yanzu gaba Daya tayi fayau kaman Babu jini a jikinta hakama sai qanqancewa takeyi tana rama da komawa karama.

A daidai wannan Gabar iyayenta sunyi kuka harsun godewa Allah sbd tinda take fama da ciwon tsawon shekaru Bata taba komawa Hakan ba sai yanzu gashi ita kanta wannan Karan ta fidda Rai daga rayuwa adaidai lokacinda taso ace ta rayu Dan bawa Jamaal farin ciki.

A rayuwar seelahs Babu Wanda ya taba tinanin zaa samu Jamaal a hali na fita hayyaci sbd kwallafa Rai a Abu sai yanzu.

Duk yanda su Dad suka dauki matsayi da girman yarinyar a zuciyarsa abin ya wuce Nan Dan haka hankalinsu yasake mummunan tashi akan lamarin auren.

Gaba Daya Jamaal ya aje komai ya tattara hankalinsa gaba Daya akan Neman mafitan ciwon fadila,
Kai tsaye ya ajiye komai har aikin asibiti sbd gaba Daya ta koma a kwance take rayuwa a kwanakin ga oxygen din kwata kwata kaman ya Dena mata aiko Dan haka take ya fasa jiran sauran kwanakin auren yace a daura kawai zai fita da ita waje mum dinsa ma tana Jira zasu taru da wasu likitocin su duba matsalanta Daya kasa Ganowa.

Babu Wanda yayi musu da maganar auren nasa dayace a matso dashi Dan Babu wani biki ko hidiman ma da zaayi tinda amaryan a kwance take tana Neman numfashinda zata shaqa ma ta rayu.

Haroon baitaba sani ko ganin haka asalin so yake ba sai akan Dan uwansa Wanda Bai taba Ganin abinda Jamaal yaso fiyeda komai ba bayan iyayensa dashi sai Fadila,

So ne me tsafta da karfin gaske da Allah ya jarabcesa dashi na yarinyarda ba lallai ta rayu ba Dan koshi da ba likita ba baiga alaman tashi ga fadila ba sedai kwata kwata Jamaal ya kasa yarda da fadilan bazata warke ba ta tashi ta basa ‘yan biyun datai alkawarin basa Shima yayi alkawarin ita kadai ce zata zama uwar yayansa,
Ita kadai ce macen dayake son ta Haifa masa wasu Jamaal and Haroon Kokuma Mamman da Omar.

Tausayinsa sosai Haroon yakeyi tin yanzu Daya kasa gane komai ya jinginar da rayuwansa kwata kwata akan fadila da iyayenta da suka koma sune masu basa hakuri da qwarin gwiwa.
#MAMUH
#SEELAHS
#AMEENATOU BABBAH
#LOVE
#HOTLOVE

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
23
Mum dinsa ya buqaci zuwanta a kasar sbd ta tayasa duba yanayin na fadila dayake tsananin basa faduwan gaban da Bai taba samun kansa da tsoron wani abu ba sai yanzu Dan kuwa ko chances na surviving nata yaqi yadda ya duba sbd Bayason Jin ko kalaman rasawa.

Duk wani ayyuka Dake gaban Dr Aleena ajiyesu tayi tayi shirin zuwa Nigeria cikin damuwa sbd Jamaal da gaske ya Saka damuwan da tsoron matsalan fadila sosai.

A daidai gaban dayake yanzu shine ko dubata Baya iya yi da kansa saidai sauran likitoci su dubata.
Da kanta take kokarin bawa kanta kuzari da karfin hali Dan basa nutsuwan cewa tana samu sauki duk da Babu saukin datake samun saima tsananta da abin yakeyi.

Ranar da mum dinsa ta sauka Nigeria
Tareda Haroon sukaje daukota airport.

Kyakkyawar baturiyar da bazaka taba cewan itace ta haifi manyan zaratan matasan Dake tsaye suna jifanta da kallan tsananin kauna da kewa musamman jamaal da ganinta gabansa ya Saka dukkanin rauninsa Daya kasa bayyana gaban kowa bayyana a gaban mahaifiyarsa.

Itama kallansa tayi tareda zuba masa idanuwanta masu haske irin nasu tana kallansa zuciyarta na karyewa da tausayin abinda take hangowa acikin idanuwansa.

Hannuwanta ta ware daidai lokacinda ya ranqwafo yayi mata kyakkyawar runguma Yana lumshe fararen idanuwansa dasuka Dan sauya Yana Jin nauyin Dake zuciyarsa Yana rabuwa sbd ganinta
itama rungumarsa tayi dakyau tana Jin inama zata iya cire ciwon fadilan ta dawo dashi kanta Dan kawai bawa Jamaal din farin cikinsa.

Sun jima ahakan tana fada masa magana me sanyi cikin kunnuwansa tana shafa bayan kansa kafin suka saki juna ya riqe hannunta Daya Yana Jin nutsuwan Daya rasa tsawon lokaci na shigarsa kadan kadan.

Rungume Haroon tayi tana Jin kaman zata hadiyesa Shima kafin suka juya zuwa mota hannunta na cikin na Jamaal Wanda ke sanye da guntun wandon Dior da rigarsa ash sai fcap da sunglasses fuskansa Babu wani walwala sosai sai daukan ido yakeyi acikin Rana shida mum dinsa harma da Haroon da baiyi haskensu ba.

Mota suka shiga Kai tsaye Haroon ne me tuqin mum na Baya sai Jamaal din a gaba.

Kai tsaye gidansu fadila mum ya buqaci a fara zuwa tafara dubata tinda shine abinda ya kawota kasar.

Suna Isa kofar gidan babanta na waje tareda siddeeq ‘dan kanwarsa data jima da rasuwa itama Yana karatu a Lagos din a hostel yake zama Amma tinda ciwon fadila yayi tsanani ya dawo gidan dole sbd baban yakai baida cikakkiyar lafiya Shima sbd zuciyarsa Dake kasa daukan rashin yarsa duk ya Tina da Hakan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected