AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Sai Daya gama wankan ya wanke bakinsa da mint mouthwash ya fito da towel dinsa da baya wani zama.

Shirin bacci yayi ba Riga jikinsa dagashi sai underwear da wata Riga mara nauyi gabanta duka a Bude ya haye gadonsa yayi kwanciyarsa bayan yayi addua.

 

Washe gari karfe goma na safe ya fito a shirye cikin Brown Paul Smith fit shirt da fit AG jeans sai agogon Bottega veneta black dayake hannunsa Koda ya fito siddeeq ya iso yana gidan a dayan palon yana aiki a laptop hakama cook tini ya iso yayi breakfast ya jere a dining.

Fitowansa kusan daga siddeeq har cook din qamshinsa ne kaman yanda ya Saba ya sanar dasu fitowansa Dan haka cook dinne yafara fitowa kallo Daya yayi masa yayi qasa da idanuwansa cikin girmamawa ya masa barka da fitowa tareda gaisuwa ya juya ya koma kitchen.

Siddeeq ma cikin girmamawan ya gaidasa Yana masa barka da fitowa.

Breakfast sukai sama sama kafin suka fice Kai tsaye fuskansa sanye da Black Prada goggles sbd ya saba Baya iya shiga Rana Bai rufe idanuwansa ba.

Siddeeq ne ke janye da sabuwar motar JEEY din mrcs Beymach Kai tsaye asibitin suka nufa.

Koda suka Isa asibitin Sister Ashley tagama fidda rai Allah yasa evening shift ne da ita Dan haka ma da safen taqi shigowa asibitin kwata kwata Amma tasan Ameenatou na can ko wanka Kila bazata yadda kowa ya kusantota ba idan ba ita din ta Gani ba Dan haka akwai yiyuwan tana can ko wankan Bata samu ba bare brush da sauran su.
##MAMUH#
#AMEENATOU
#JEEY
#SEELAHS

 

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
66
Kai tsaye inda ya kamata ya tafi yafara zuwa yayi reporting da komai yakuma gana sosai da duka manyan Daya kamata ya Gani din Dan haka Bai samu kansa ba sai guraren laasar Dan haka sallah sukai ya nufi lafiyayyar office din da akai gaggawan tanadar masa daga jiya zuwa yau aka sauyata zuwa daidai yanda ya Saba zaman offices dinsa Dan kuwa kwata kwata kaman ba acikin asibitin office din yake ba hakama siddeeq bayan gyaran da akaiwa office din da suna gurin meeting din da kansa aka sake yiwa office din gyaran daidai da rayuwan JEEY din sbd office ce babba datake da Lafiyayyan bedroom aciki ta Call(Night) idan ya kamaka musamman shi da zai kasance acikin asibitin kusan 24/7,
Daga cikin bedroom din cikin office din lafiyayyar toilet ce da itama Saida siddeeq yayi time dinta ya zuba mata kudi Dan duk abinda JEEY zai buqata a toilet dinsa da bedroom dinsa na gida ya zuba masa su din anan ma coz Idan kana cikin bedroom din bazaka dauka a office ne dayake cikin asibitin mahaukata ba saika fito waje.

Hatta shoes da zaiyi amfani dasu irin su slippers da sandals da covers da shirts Saida siddeeq ya kawo qwarori ya jere masa su a inda ya kamata Dan kuwa lafiyayyar gado ce a dakin dasu wardrobe su closets da sauransu.

Daga masallaci sallan la’asar Abinci Siddeeq yaje gida ya kawo masa a lafiyayyar basket da cook ya gama shiryawa kaman a 5star restaurant.

Bai wani ci abincin ba sosai sbd akwai gajiya a tattare dashi hakama Bai samu file din Ameenatou daga cikin files da aka fara gabatar masa ba Dan haka Kai tsaye ya buqaci ganin Sister Ashley Dan sanin wane block ko ward Ameenatou din take,

Ita Kuma sister Ashley din shigowanta kenan sedai Kai tsaye gurin Ameenatou tafara zuwa dan dubata kafin ta wuce gurin aikinta.

Ga mamakinta yanda tayi tinani Haka dinne Ameenatou nurses da ward attendence na block din sun taru anyita fama taqi yadda ko kusa da ita kowa ya taho Duk dubarunsu kuwa,

Nurse Fahat shine kusan a gaba duk yanda yaso ya kusantota taqi yadda San shi Yana motsawa take kokarin rikicewa gaba Daya Dan haka aketa fama da ita wuni Daya Amma kwata kwata lamarin yaqi yiyuwa.

Hakanan suka gaji suka kyaleta a dakinta rufe Babu Wanda ya sake bi ta kanta wuni Daya Babu ci Babu Sha Babu wanka bare tsaftacewa har Saida sister Ashley din ta taho.

Sister Ashley na Bude kofar dakin ta Sako Kai ko qarasowa batai gurin Ameenatou dinba ba ta dakata tsakar dakin tareda zubawa Ameenatou din idanuwanta jikinta na mutuwa da ganin yanayinta.

Ameenatou dinma Dake rakube karshen gadonta tayi laushi Babu kuzarin komai a tattare da ita sbd Alluranta daya Bai saketa kwata kwata ba da Kuma yunwar data cinyeta ga fitsari Daya matseta ga rashin ganin sister Ashley din tin jiya abinda Bai taba faruwa da itaba tinda tazo.

Dago idanuwansa da suka sauya sosai tayi ahankali tareda zubawa sister Ashley ta qura mata idanuwa batareda ta motsaba bare alaman motsawan.

Sister Ashley Christian ce data auri musulmi ta musulunta Amma Bata Wani jima da musuluntanba Dan haka ba Wani sosai tasan abubuwan addini ba hakama Bata taba haihuwa ba Amma zuciyarta me rauni da tsananin tausayi ce Dan haka take idanuwanta suka ciko da Hawaye Dan Allah ya sani kaman jininta take Jin Ameenatou.

Hadiye hawayen da suka ciko idanuwanta tayi tareda qarasowa gurin Ameenatou din ta zauna bakin gadon tareda warewa Ameenatou din hannuwanta ahankali tana cewa

“Come to Sister Ashley My baby kinji”

Abinda Bata taba Gani ba daga Ameenatou din yau ta Gani wato Hawaye na gangarowa bana azaban ciwon alluran da ake mata ba dake fitiwa dan kansu
Wainnan da kanta Ameenatou din suka fito mata alama ce ta fara samun kanta ko fara sanin dacin zuciya da rashin samun abinda takeson Gani ko kasancewa.

Ahankali ta motsa daga rakuben datake jiki ba kwari ko kadan a Sanyaye ta shige jikin sister Ashley din ta lafe
Ita Kuma ta rungumeta tana shafa gashin kanta dayake duk a hargitse alaman da safe ko cikin dare ciwonta ya tashi tayita fizgansa.

Shiru sukai na tsawon mintina Babu Wanda ya motsa kafin sister Ashley ta dagota tareda kallanta tace

“Babynah zata Sha tea??
Bread??

Zuba mata idanuwa Ameenatou din tai batareda ta iya cewa komaiba bare gyada Kai kanta yayi mata wani irin nauyi ne da tashewa.

Numfashi sister Ashley tayi tareda saukowa gadon ta kamota ta sauko da ita tareda Saka mata slippers ta jata suka nufi toilet.

Basket din kayan wankanta ta dauko suka shiga toilet ta zaunar da ita akan kujeranta na wanka Dake tsaftace hakama toilet din fes Dan so biyu clearners ke wankewa.

Kanta tafara wanke mata ahankali ahankali cikin kulawa da nutsuwa.

Yau ko hanawan datake a wanke mata Kai Bataiba a zaune take shiru har aka gama Akai wanka aka gama ta dauro mata towel babba suka fito.

Suna fitowa ta zaunar da ita ta goge mata jikinta da gashin fes kafin ta shafa mata Mai ta shafa mata turarenta me sanyin qamshi da ake siyowa tin Wani be qareba ake siyo Wani.

Undies ta Saka mata tareda uniform dinta Dake a wanke Dan kusan kowa uniform biyu ne zuwa uku yake dashi.
Gyara mata gashin tayi ta Dan kame mata shi ba sosai ba ta sake Kiran clearner aka sake gyara dakin ta hada mata tea tana kokarin fara Bata kenan Kiran siddeeq ya shigo wayarta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected