AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Haroon da mum Atee ne suka ringa son lallabata Jamaal su fahimtar dashi ya hakura tinda mahaifinsa Baya son yarinyar
ga tarin mamakinsu daga karshe Jamaal zabar komawa yayi gurin mum dinsa.
Haroon rintse idanuwansa yayi cikin sabuwar damuwa Dan daman abinda yasan zai iya faruwa ne Kuma yaketa gudun ya faru din.
Mum Atee kanta sosai ta shiga fargaba ta ringa binsa da lallashi da son fahimtar dashi rashin kamatan Hakan Amma gaba Daya yaji zai iya aje komai na Seelahs ya koma Dr Jamaal din mahaifiyarsa ita data amshi fadilansa hannu bibbiyu.
Wannan shine mafi bacin Rai da tashin hankalin da Dad dinsa ya shiga ganin kawai Rana tsaka Jamaal ya zabi mace fiyeda su,
Kuma macen ma nakasashiya da zata Bata musu aiki da yawa tareda sauya musu Jamaal din gaba Daya Dan kuwa tin yanzu ya sauya fiyeda kashi 70 akanta ana auren Jamaal zai janye daga tarin companies dinsu da nauyin seelahs gaba Daya dayake kansa ya koma likita kawai Kuma me tattalinta shikenan su komai nasu ya rushe a banza bayan tin kafin ayi auren uwarta ma suka hada jini da majina da gumi suka hada dukiyar.
Dad Lameenu Daya tsani tsayawa lamari na basa ciwon Kai batareda ankai karshen matsalar ba ayita ta wuce Jin yayi zai iya komai akan Hana Jamaal tafiya yabarsu hakama bazai iya barin ayi auren ba tinda auren Jamaal din kaman downfall dinsu ne abubuwa da yawa zasu biyo Baya,
Na farko saisun wayi gari Jamaal ya tattara komai ya ajiye ya koma asalin Dr dinsa kawai,
Na biyu mahaifin yarinyar Daketa son dorasa akan wata turban dazai haddasa babbar fitina a tsakaninsu da babu Wanda yasan ma Ina zata tsaya,
Na uku auren Nan rabasu da Jamaal zaiyi kwata kwata zai koma kaman mahaifinsa fadilan shine mahaifinsa hakama yanda yakeson yarinyar Babu abinda zai hanasa tattara kulawansa akanta.
To duka idan Hakan ta faru su meye matsayi Dan makomarsu?.
#MAMUH#
#DR JEEY
#AMEENATOU BABBAH
#HAROON SEELAH
#THE SEELAHS
#LIFE
#HOTLOVE
#TOOHOT
#ROMANCE
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
22
Fadila da tinda aka fara wannan tashin hankalin ta shiga nata tashin hankalin Mai tsananin gaske da damuwa tareda janyewa daga kowa Dan kuwa tasan bama zata taba samun Jamaal ba yaudaran kanta takeyi data bari ta jefa kanta a duniyar da Bai kamata ace ta jefa kanta ba.
Ummanta da baban damuwa suka shiga Suma gashi damuwan yafara tabata yau lafiya gobe ciwo harta Kai oxygen ma wasu lokutan da dama tana zarewa kanta batareda saninsu ba saidai su sameta tana kokarin rasa rayuwarta suyi gaggawan Kiran Dr Jamaal din Wanda Shima tini kansa ya fara daukan caji Dan kuwa sosai take kokarin rasa rayuwanta a lokuta da dama idan Hakan ta faru.
Zafi sosai kansa ya dauka kaman yanda iyayenta Suma kansu ya dauki zafi daga karshe batareda sanin Jamaal din ba baba yaje har office din Alh Lameenu seelah yayi magana dashi bayan dogon jiran Daya Sha da bin dokoki sbd baida appointment dashi.
Bayani da nasihu yayi masa akan su hakura subar yaran suyi aure tinda suna son juna Kuma ya sake Basu tabbacin yarsa batada wata tarbiya mata kyau ko halayen da zasu sakasu Jin Dana sanin barin dansu ya aureta ciwonta Kuma kaddara ce da Allah yafi kowa sanin dalilinsa na yinta a Hakan.
Harya gama bayaninsa da nasihunsa Harma da waazinsa Dad Lameenu baice komaiba sai daga karshe yayi masa Godia fuska a sake Yana nuna ya gamsu da bayaninsa Kuma insha zasu tattauna da Dan uwansa zasu taho da jamaarsu maganar neman auren.
Bayan tafiyar baban numfashi Dad Lameenun ya sauke Yana Jin gwara su bari ayi auren idan har sunason riqe Jamaal a hannunsu batareda ya barsu ba.
Da daddare suna tareda Mam a office dinsu na gida yayi masa bayanin komai Wanda kusan Shima Mam din shawarar Daya Yanke kenan ganin Jamaal din yafara Shirin barin kasar da gaske barinsu zeyi Wanda yafison ya rasa wani bangare na dukiyarsa me yawa Daya rasa Jamaal a bangarensa.
Ranarda Jamaal yagama samarwa fadila Visa auren kawai za’a daura musu ya tafi da ita Dad dinsa akan dining gurin cin abinci ya sanar dashi ya amince da auren idan har zai zauna dashi bazai barsa ba har abada sedai mutuwa.
Wani sanyi ne ya fara cike zuciyar Haroon kafin mum Atee data sakin hamdalan farin ciki hakama Ayesha data shiga damuwan tafiyarsa.
Shikuwa dagowa yayi ya zubawa Dad din fararen idanuwansa batareda yayi masa alkawarin dayace yayi masa dinba Dan kuwa baiyi alkawarin barin mahaifiyarsa har abada ba haka Kuma idan ya daukota daga qasarta ya dawo da ita kusa dashi baiyi mata adalciba shiyasa Bai taba gwada cewa zai dawo da ita kusa dashi ba kwata kwata duk yasan idan yace ta dawo kusa dashi din zata dawo Amma dai bayason yi mata Hakan Dan qasarta itace Kwanciyar hankalinta da nutsuwanta.
Murmushin yaqe Dad din ke sakewa na yake Yana nunawa Jamaal din ya amsa fadilan dari bisa dari.
Numfashi Jamaal din ya sauke Yana Dan lumshe idanuwansa tareda Jin wani nauyi dayake kirjinsa ya sauka Dan kuwa Koda ya tafin zuciyarsa bazata taba samun wannan nauyin ya sauka ba tinda bawai baya kaunar mahaifinsa bane Yana tsananin kaunarsa fiyeda tinani kawai dai shi ya iya boye Abu ne dakuma yawan samun sabanin raayin dayake samu da Dad din ba kaman Haroon ba da duk abinda Dad yafada masa yayi me kyau da mara kyau to ya zauna.
Cikin farin ciki me tsanani da Jin dadi Haroon yayiwa Dad din Godia Yana bayyanarda Jin dadinsa ga sulhun da aka samu tsakanin Dad da Jamaal din Dan idan Jamaal ya tafi ya barsa baisan wace rayuwar zai fuskantaba a gurin Dad din idan Jamaal Baya nan hakama yasan bazai taba iya musu ayyukan nasarorin da Jamaal yake musu ba musamman bangaren manyan harkoki da baida sani ko kadan akansu.
Jamaal ma Jin yayi tausayin Dad din nasa ya shigesa sbd ya amince ne da auren yasani Badan har dari bisa dari din Daya fada ba Yanason auren sedan Yana tsananin sonsa fiyeda nasa farin cikin bayason rabuwa dashi.
Godia yayiwa Dad din cikin nutsuwa da kulawa tareda bayyanar masa da kaunar da Dad din ke tsananin son Gani daga garesa.
Hakan da yayi ba qaramin Saka Dad din farin ciki me girma yayi ba Wanda harya bawa Haroon tausayi sbd idan akwai abinda Allah ya jarabta Dad din dashi shine Jamaal da kaunarsa.
Ko Alh Lameenu lokuta da yawa shi kansa Yana tsoro da shakkar yanda Mam ke tsananin son Jamaal Dan haka yake gudun kada Hakan ya zama raunin Mam su samu matsala sosai me girma tinda Jamaal din kwata kwata ba page Daya suke dashi ba akan abinda suke aikatawa Dan ma Allah ya rufa musu asiri ba shine lawyer ba Haroon ne da kashinsu ya Dade da bushewa duk power dasuke riqe da ita suna juya sharia yanda suke so da sai Jamaal ya tabbatarda sun rasa komai.
A Daren ranar firan da suka jima a tsakaninsu basuyiba Saida sukai shida Dad ciki kulawa da kauna har tsawon dare kafin ya fito ya wuce part dinsa tareda Haroon da Shima ranar kaunar Yan biyunsa ta motsa a part din zai kwana.