AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Dadah ma kaman zata Bata nono haka takeji sbd sunyi kewanta.
Arfat ma yayi kewan mommansa Dan haka duk suka dabaibaiyeta da kauna.
Hafiz Cikin mamaki ya Kallesu Shima ya sake sauyawa sosai kaman Wani lafiyayyan halfcast haka ya koma ga class da wayewa tareda kudi takoina da suka gama ratsasa Dan haka sake kallansu yayi da mamaki bayan angama dinner Suna zaune palon babban su duka yace
“Wai yanzu babbah wannan qatuwar budurwan kuke was wannan tarairaya kaman Wanda tayi tafiyan shekara baku ganta ba Gani nida nayi tafiyan kusan wata nawa ko kallon arziki na kasa samu.”
Kallansa babbah yayi Yana washe hakoransa gaba daya bayan ya sake kallan Ameeenatou yace
“Kai yanzu kake maganar qatuwar budurwa ake tarairaya baka Kalli kanka qaton gardi da Kai kake cewa a tarairaya,
Banason Saka Ido fa,ka dawo zakabi ka Saka mata Ido ka dameta har sai yar qibar datayo ta tsiyaye sbd surutunka.”
Yasan babbah bazai taba sauyawa akan Ameeenatou ba komai tsufan da zaiyi da girman da itama zatai Dan haka murmushi kawai yayi Yana kallan dadah da itama Idanuwanta basa gajiya da harara indai akan maganar Ameeenatou ce to zata iya wuni Bata gajiba tana hararar mutum.
Ashly dataga haka sai ta shigarwa Hafiz tana cewa
“Babbah Hafiz fa ma gaskia yakamata ayi tarairayansa sbd nidai idan kowa baiyi kewansa ba to ni nayi sosai”
“To ai saikiyi tarairayansa shekenan an huta da Saka idonsa”
Babbah ne ya fada hakan Yana kallansa cikeda kaunarsa Shima.
Fira sukai sosai harma da Didi data taho Nan din suka sake bajewa a palon Suna fira sai dare sosai kowa ya nufi dakinsa.
Suna hayewa sama wayarta ta tararda misscalls dinsa harma da txt sai kawai ta share ta wuce toilet tayi wanka ta fito tayi shirin bacci ta shige Cikin jikin Arfat da zai kwana dakinta.
Bacci me karfi ne ya dauketa sedai da tsakar dare tashinta biyu tana sauya gurin kwanciya sbd haka kawai takejin gajiya da baccin.
Washe gari da safe ma Bata tashi da wuri ba sbd bazata fita Aiki ba Dan haka kawai batason fita koina.
Gida suka wuni tareda kowa da kowa Dan babu wanda ya fita Aiki Suna hutawa luxury life kawai.
Jamaal ma Bai fita koina ba hutawa yayi gida tareda nasa familyn daya hada sbd Maman fadeela Kam tini ta zama tasa hakama Ayesha ta saki jikinta tinda dai tsakani da Allah Taga Suna kauna da kulawa da ita hakama tin farko ba halin Mum dinta Allah ya Bata ba Dan haka ta sake
Mum Aleena ma sbd kaunar da Ayesha tayiwa Haroon da Yana Raye ya sakata kaunarta da gaskia daga zuciya Dan haka tini suka zama family hankali kwance.
Dr Aleena na son zuwa duba Arfat da Ameeenatou data dawo Amma Sam batason zuwa su fuskanci juna da Nur wadda tasan da auren Kuma Bata damuba sbd Omar bai boye mata ba Kai tsaye ya sanar da ita maganar daura auren wanda Yana can Jamaal Kai tsaye ya hada auren Kuma aka daura.
Daga ita har Nur har Omar Babu wanda suka hadu a face to face tinda aka daura auren.
Ita Nur Bata damu ko kadan da auren ba sbd tasan tarihin son dayake tsakaninsu Dan haka ko Bata yadda da aurenba ba Dena son Aleena Omar zaiyiba kaman yanda itama ta manyanta ba auren kowa a kanta tin rabuwarta da Mam sbd Omar ne Dan haka ba amfanin tada hankali hakama Suna Cikin arzikin da idan kaso Damar da kanka ne zaka sakawa kanka kishi da tashin hankalin da bazaka sake Jin dadin rayuwar da Allah yayoka a Ciki ba bare kaman yanda tasan bazata bawa Aleena da Omar ciwon Kai ba Suma bazasu taba Bata ba hakama nata kalar tsananin son da Omar yake mata daban da wanda itama Aleena yake mata hakama itace farkon matarsa a duniya girmanta daban yake har abada so ba abin damuwa gareta take ta amincewa auren wanda baa daura ba Saida ta amince din and ta samu girman da batai tinani ba a idon Jamaal da shi kansa Omar din harma da Dr Aleena da Uncle Ahmed da babbah wanda Shine yayi wakilcin Omar Jamaal yayi na Aleena sedai har akai aka gama ba fuska daga babbah zuwa ga Jamaal Wanda murmushi kawai abin yake sakasa sbd kauna da tausayin babbah Dan tsananin son dayake wa Ameeenatou ya Saka Jamaal kaunarsa me girma da tsafta sedai Yana tausayinsa sbd yasan ya gama lalata masa Aiki.
#MAMUH#*_Arewabooks@Mamuhgee_*
138
Da daddare Suna zaune Suna fira a palon Babbah bayan sun gama dinner tana jikin dadah kwance bacci me dadin gaske ne takeji ya dauketa.
Wayarta na dakinta ta baro yayita kira Bata dauka ba Dan haka ya taho Kai tsaye gidan.
Hafiz ne da sukai waya yayi masa iso har palon Babbah Dan gaidasa.
Suna shigowa babbah ya Dan kame fuska Yana amsawa batareda sakewa ba harya gama gaisuwansa a taqaice Shima Idanuwansa na kan Halal dinsa datake kwance jikin dadah bacci takeyi hankalinta kwance kaman baby.
Yanda yake mata Wani kallo ya Saka babbah cewa dadah ta tadata su tafi itada Ashley su wuce sama.
Ahankali dadah ta tadata cikeda kulawa.
Tana Bude Idanuwanta akansa suka fara sauka haskensa ya sake mata yawa hakama yau kamanninsa da Arfat take ganin Suna bayyana.
Wani sanyi da tsananin sonsa ne taji Yana taso mata Yana kashe mata jiki Babu abinda takeso kaman jinta kwance jikinsa tana shaqar qamshinsa me sanyi da sanyaya zuciyarta.
Ashley ce ta zungura kafarta da hannunsa daya Cikin fuskewa sbd yanda ta lafe tana yiwa Jamaal din kallan da kana kalla kasan tsananin sonsa takeyi.
Tashi tayi zaune tayi Taga Idanuwan babbah akanta Yana jiran tashinta da ficewanta.
Batace komaiba ta miqe tareda zira slippers dinta masu laushi ta nufi kofa tana mantawa da yiwa su babban Saida safe Shima babban Bai damu da hakan ba sbd tafiyanta kawai yake buqata.
Hafiz murmushi kawai ya sake sbd yasan abinda yake faruwa tinda ita dashi din Babu abinda suke boyewa juna tini yasan tin a Macau Suna tare har zuwanta Abujan Kuma Shima Bai fadawa kowaba shiru yayi abinda shiyasa Shima ya zama Dan hannun Damar JAMAAL SEELAH.
Suna ficewa Shima Jamaal sanyayyar ajiyan zuciya ya sake a boye Yan sauke wani kyakkyawan murmushin daya Saka gaban babbah mummunan faduwa sbd ganin kamar kamanninsa da Arfat wanda baitaba lura ko kadan ba.
Ganin dukkaninsu kaman turawa haka suke ya sakasa tinanin kawai hakan ne ya Saka sukai kamannin bawai Dan hadin jini ko Wani abin b daban.
Shima sallama yayiwa babbah din tareda ajiye masa envelope dayake dauke da Yan 100 100 dollars wanda babban baima lura da ya ajiye masa din ba Saida ya fice tukuna Kuma yace bayaso mayarwa zaiyi
Dadah ce da Hafiz suka Hanasa sbd rashin dacewan hakan.
Shi kuwa Yana fitowa daman Basu qarasa part dinsu dinba Dan haka Yana kawowa daga bayansu ya rungumota Yana sauke ajiyan zuciya da cewa
“Ya Rabb have mercy on me I love babyn Babbah fiyeda yanda zuciyana zai iya dauka”
Kissing din gefen fuskanta yayi Yana sake cewa
“I can’t take ths anymore baby aban Halal Dina kawai”
Ashley Dake gefensu cewa tayi
“Wlh Nima na gaji da karyan Nan da kame kame da gadin zance a baka na huta Dr”
Dariya yayi mara sauti Yana sake rungumeta yace
“Me kikace matar Jeey??
Kallansa ta dago tayi tana zamewa daga jikinsa tabar hannunsa Dake sarqe kawai tace
“Sai abinda babbah ya ce nakeyi ni”
Wata dariya me Dan qarfi Ashley ta sake tana toshe Baki sbd kada babbah ya jiyota zatai magana JEEY ya kalleta tareda gigiza mata Kai Cikin fuskewa batareda Am din ta lura da hakan ba Dan haka Ashley ta hadiye zancenta tana dariya kawai.