AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Siddeeq daman Bai gezu ba sbd yasan wa ake maganar Jamaal ya rabu da ita,
Tabon raunika biyu ne a jikinsa daya qi barin su goge sbd nata ne,
Dayan a wuyansa wanda baisan Yaya tai masa shi ba sai wani a hannunsa daya zagayesa da tattoo tareda kalman sunanta.

Rashinta kadai a duniya ya jijjiga rayuwar JAMAAL SEELAH wanda dashi da Mum dinsa kadai ne suka San azabar rayuwa da tashin hankalin da suka shiga kafin dawowansa Sabon JAMAAL ba Dr Jamaal ba Amma yanzu Rana tsaka ace wai ya saketa,hmmmm.

*****Fes ya tashi yau Babu damuwan komai a Cikin kansa bayan jinsa a natse,

Saukowa yayi a shirye Cikin kaftan din original cashmere me tsadan gaske daya nutsu a jikinsa navy blue da hular data sakasa yin Wani irin sbd kaftans ba qaramin kyau suke masa ba sbd kasancewansa ruwa biyu.

Qamshinsa ne ya ankarar da Mum dinsa dake zaune Palo tana waya a natse itama hankalinta a kwance kaman na danta dagowa ta Kalli hanyar saukowansa.

Siddeeq ma dayake dining zaune Yana cin abincin dagowan yayi Yana kallan hanyar.

Fuskan Mum din ya shafa ahankali kawai Yana cewa “Love you Mum”

Ya wuce dining din inda Shima siddeeq ya Kallesa yace

“Barka da fitowa”

“Barka,Yaya maganar Bellamy??

“Ya sauka Yana qasar Amma Abuja ya sauka but gobe da safe zai biyo flight din Lagos”

“Ok, Maganar Ashley fa akwai Wani bayanin??

“No but inshallah ankusa”

Kallan siddeeq din yayi ganin Yana masa Wani kallo ya ajiye cup din milkshake dake hannunsa yace

“Karma ka fara nasan me zaka fada.”

Dariya siddeeq ya sake Yana cewa

“Zan fada Amma ai ba yanzu ba sai lokacinda……

Miqewa yayi
Siddeeq yayi saurin hadiye sauran maganar Yana cewa

“Nabarta nabar maganar”

JAMAAL Wani kallan ya sake watsa masa Yana zaunawa yace

“Kaci gaba kaga idan bamu tattara muka koma gidan Dad Omar din ba sbd indai a gidan Dad Omar ne zan iya zama living son-in-law,
Dare nayi naje palon Babbah bacci”

Dariya siddeeq ya sake Yana cewa

“Hmmm ka sani ko babbah nada tsohuwar bindiga Dan da alama babbah aka takura Dan tawayensa dayake fada zai zama, Kuma akan wannan auren kasan tsaf zai fara da qafafunka”

Murmushi Jamaal din yayi har hakoransa na bayyana yace

“Ba yin bindigar tasa ba wataran yaje ya harbe qafafun ‘dansa idan ya dauka nine a gurin budurwan tasa kaga an huta da rawan kan ‘dan nasa ya saukakawa kowa Aiki”

“Dariya siddeeq yayi harda Mum dinsa Dake tahowa itama dariyan tayi sbd da turancin suke firar Kuma tasan sarai a yanda tasan Jamaal yaga AM da Hafiz din zai iya kallo babbah ya harbe qafafunsa idan yaso daga baya ya taimaka masa a amtsayin likita bayan barnar ta afku.

Zaunawa tayi suka qarasa breakfast din da ita Dan ita yau farin Ciki takeyi maman fadeela zaa dawo da ita gidan kwata kwata sbd su debewa juna kewa hakama hankalin siddeeq ya rabu sbd maman fadeelan tana can Dan haka aka ware mata Palo da bedroom dinta lafiyayye Babu abinda Babu,kayan sakawanta kadai zaa daukota dasu Suma ba duka ba sbd hatta wardrobe Saida aka sauya mata Kuma daman ba laifi sun Saba da Dr Aleena din Tin fadeela na Raye.

Suna gamawa suka fice Mum nai musu addua.

Kai tsaye mansion din JDENS suka nufa Suna isa securities dayake sunsan waye JAMAAL din suka Bude masa gate lafiyayyar motarsa ta kunno Kai daidai lokacinda da Hafiz zai fita tareda Arfat Yana riqe da hannunsa sanye da fararen kayan Nike sun masa kyau harda fcap da nosemask na Yara aka Saka masa da glasses na Yara duk dan kada agansa a gane bature ne bayan ansan basuda turawa a fmlyn.

Kallan Arfat siddeeq yayi
Shikuwa JAMAAL Idanuwansa ya zubawa Arfat din batareda sun fito motar ba Yana kallan komai nasa a natse daki daki Yana Jin zuciyarsa na kasa nutsuwa tareda shiga damuwan kallansa kawai.

Hafiz yaga motarsu Kuma Kai tsaye yasan JAMAAL dinne Amma Bai nufesu ba Saiya Kai Arfat Cikin mota yakeso tukuna su gaisa Dan haka mota ya nufa da Arfat din.

JAMAAL Bude motar yayi ahankali Cikin nutsuwa da class qamshinsa na bin iskar gurin Yana kamawa ya nufi Arfat din Kai tsaye.

Siddeeq ma fitowa motan yayi ya nufesu sbd wancan Karan baiga fuskan babyn da kyau ba ranar daya gansu airport.

Yana nufarsu Idanuwansa akan fuskan babyn Amma sun rufesa da kyau baka Wani gane kamanninsa.

JAMAAL na zuwa sake kyakkyawar fuskansa yayi kadan tareda ambatar sunansa Yana cewa

“Arfat is that you??

Juyowa Arfat yayi da sauri Yana ganin Jamaal ya sake fuskansa Cikin murna yace

“Hey Handsome”

Hannu JAMAAL ya miqa masa da gudu ya taho ya miqa masa nasa Jamaal ya kama hannunsa tareda Dan ranqwafowa yana zare masa fcap dinsa ahankali Yana kallan tsakiyar blue eyes dinsa.

Qamshin AM ne da jiya ji daya yayi masa ya riqesa ya shiga hancinsa Yana fitowa daga jikin Arfat din.

Jikin Arfat din ya kalla kafin ya dago ya Kalli fuskansa qamshinta na sake shiga hancinsa dakyau.

Mayar masa da hulansa yayi Yana cewa

“Zaku fita ne??
Ina Mum Dinka??

Tambayar yayi masa sbd son sanin waye mum din tasa ko Dad dinsa.

Hafiz ne da Siddeeq ya riqesa da fira yayi saurin kama hannun Arfat din batareda ya bari ya amsaba Yana cewa

“Son muje Kar muyi latti”

Dagowa yayi ya gaida Jamaal din da Idanuwansa akan fuskan Arfat dayake Jin zuciyarsa na qara kunnuwa gameda fuskan dayake Gani akan ta Arfat din sbd fuska ce d duk duniya itace fuskan datake haskaka rayuwarsa,
Ako yaushe Cikin adduar dayakewa mahaifiyarsa Cikin sallansa sbd tsananin son dayake mata adduarsa Allah ya basa ‘yayan da zasu dauko fuskan mahaifiyarsa sbd ko tsufa ya kamata yaringa kallan fuskan data haifesa akan nasa ‘yayansa.

Fitowan Ameeenatou ne daga bayansu sanyeda doguwan fitted lady cashmere datake dinkin kamfani crystals ne kadai ke motsi a jikin rigar hakama ta zauna daidai jikinta Cikinta a lafe kaman baby Bai taba zama gurinba.

Nadin Veil ne akanta sai handbag dinta ta Louis Vuitton da shoes dinta.

Fuskanta sanye Babu makeup din komai bayan eyeliner daya fidda hasken Idanuwanta sosai.

Hafiz ne ya Kalli bayan Jamaal din inda take tahowa kafin ya dawo da Idanuwansa kan Jamaal da Bai amsa gaisuwansa ba Dan kaman ma baijisaba.

Siddeeq ma kallo daya yayiwa AM din ya dauke Kai Yana dawowa da kallansa kan Jamaal da ko Basu fada ba yasan itace din sbd qamshinta daya shiga hancinsa Kuma bai juyoba Saida ya tabbtarda ta kawo ya juyo ahankali Cikin nutsuwa.

Cak ta tsaya tareda dauke kallanta daga kansa zataiwa Hafiz magana sai Kuma ta fasa sbd ko muryanta bata buqatan yaji Dan haka Arfat kadai ta kalla ta daga masa yatsunta biyu alaman bye.

Shima hannun ya daga mata Hafiz Bai bari yayi magana ba ya daukesa ya Saka mota y rufe Shima y shiga sabuwar motocin da Dad Omar ya siyo musu masu shegiyar tsada su ukun,shi Fatmah da AM sedai ita bayan motar Dad Omar din Mum Nur ta Siya mata fitinanniyar beymach ta hada biyu.

Motar Hafiz na fita harabar mansion din ta juya Kai tsaye zuwa motarta ko siddeeq bata kalla sbd tasan bazai kalleta ba suyi magana idan ubangidan nasa Yan tsaye.

Tana isa motar ta miqa hannu xata Bude kyakkyawar hannunsa ya Riga nata sauka akan motar.

Dakatawa tayi batareda ta Dora nata b sbd kada hannuwansu su hadu hakama kasa motsawa tayi bare juyowa sbd hasken hannuwan kadai ya tabbatar mata da waye Kuma Babu wanda ya isa yayi mata hakan idan ba shi dinba dayace da aurensa akanta..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected