AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Ameenatou rayuwarta tayi raunin data Saka kowa Maida tattalinsa da kulawansa Akanta sbd su samu t dawo daidai Dan abin ya fara taba mental health dinta Kuma,.

Babbah ma tinda ya dawo gida ya ringa jan abarsa a jiki Yana tattalawa sbd Jin bashine asalin mahaifinta ba ya tabata sosai tareda qara rikita rayuwarta.

Hankalinsu tashi yafara ganin tana Neman komawa haukar data fito
Dad dinta ya tashi tsaye suka ringa kulawa da ita tareda kaita Greece Taga wani likitan cikin ikon Allah suka fara samun kanta tafara dawowa daidai.

Arfat kuwa kauna da kulawan da ake masa yasaka baka ma Wani gane waye Asalin wadda ta haifesa a tsakanin Ameenatou din da aunt matar uncle Ahmed Didi da Fatmah babbar ‘yarsa.

Dad Omar baiyi Wani sake ba ya Saka Ameenatou din makaranta sbd a yanzu da zai bayyanarwa duniya ‘yarsa tareda familynsa na Jden Yanada buri akan ‘yarsa ta zama cikakkiyar mace Mai ilimi da yanci,
Yanason duniya tasan AMEENATOU OMAR JDEN a matashiyar da zata zama magajiyar dukkanin JDENS dayake dasu a kowanne qasa Dan haka ya Sakata makaranta Dan bazai qara bawa maqiyansa damar cutatar da ko dabbar gidansa ba bare familynsa uwa Uba Kuma ‘yarsa.

Hafiz ma tini yafara karatu da fara zuwa Aiki kamfaninsu Dan kafin ya kammala karatun yafara sanin kan aiki.

Babbah da dadah kuwa Hutu da Jin dadi ne kawai nasu shiyasa Babbah ya Bude Babin rayuwar dayake so cokali cokali ba damuwa komai saita jiran su koma Nigeria yayi sanadin rufe asibitin da Ameenatou tayi zama.
AFTER 3 YEARS.
#MAMUH#

###MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
99

*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

************
*_Three years later_*
A natse take saukowa daga stairs tana Saka wayar hannunta cikin tsadaddiyar Lv handbag dinta datake hannunta sbd lokacin ne ta kunna wayar batareda ta tsaya duba sakwannin da zasu shigo ba Kokuma kira duk da Babu wani Wanda zai kirata a daidai wannan lokacin sbd lokacin hutunta ne idan ba irin yanzu da dole take butqan fita Office ko final exams dinta datakeyi.

Sanye take da doguwan rigan Abions black kala data fito da haskenta sosai tareda sauyinta daga Ameenatou Babbah zuwa AM JADEN datake amsawa a yanzu Dan duk Wanda ya Santa France din da AM Jden ya Santa.

Lafe rigar take a jikinta batareda ta matse ta ba daidai shape dinta,
Versace silk scarf ne a kanta daure sai agogon kawai da takarman jimmy choo,
Fuskanta Wani irin haske da glowing yakeyi na asalin Hutu,Jin dadi, Kwanciyar hankali tareda Arziki Daya ratsata,
Karatunta ne kadai damuwan datake gabanta a yanzu,
Batada damuwa ko kunci ko Wani abu rashi,
Arfat shine hasken idaniyarta Kuma hasken zucuyarta fiyeda komai,
Tana masa Wani irin tsananin so Mai cikeda tsananin tausayin rashin sanin Asalin mahaifinsa,

A farko tashiga depression,
Ta shiga hauka,tashiga masiffen tashin hankali da damuwa da qunci me tsananin zurfi akan halinda ta tsinci kanta na haihuwar ‘dan da batasan da cikinsa ba,batasan waye ubansa ba,
Batasan ya Akai ta samesaba.,

Amma familynta,ahalinta,iyayenta,danginta abin alfaharinta sun taru sun hada karfin zuciyarsu da karfin tsananin son da suke mata sun hanata shiga dawwamammiyar haukan da zata mayar da ita mahaukaciyar data fito,

Sun tsayu sunyi yaqi da Hakan soyayyarsu ta rinjayi mummunan qaddarar dataso afka mata ta dawo daidai,
Sune suka nuna mata ARFAT a yanzu shine dukkanin abinda suke tsananin so da kauna tareda buqata Dan haka itama Hakan ya zauna ranta batada kaman ‘danta,
Tana sonsa,Dad Omar Yana tsananin sonta da ARFAT fiyeda duka abinda ya mallaka a rayuwarsa Shima,

Babbah Yana musu Wani irin tsaftacciyar kauna da so Dan bayama Tina ARFAT baida Uba,tini ya kashe ya binne zancen a zuciya da rayuwarsa kaman yanda kowa yayi Hakan,

Hafiz shine Uba,uncle,Yaya,Aboki Kuma Abokin wasansa,
Yanawa Arfat Wani irin so dayake Jin tamkar shine ya haifesa,Jinsa yakeyi kaman tsatsonsa,
Bai hada mahimmancin duk wani abu Daya shafi Arfat da komaiba,
Dan kusan Hakan ne ya Saka duka tsaddadun designers na kayan dayake sakawa harma Dana amfaninsa kusan set ne na father and son Dan haka kusancinsu na musamman ne,

Ta bangaren Mom Nur da aunt Didi kuwa kwata kwata basa wasa da duk lamarinsa hakama komai yakeso a gidan shi akeyi baa barinsa Kuka baa barinsa duk abinda zai ji masa ciwo,

Fatmah ma sosai take Ji dashi duk da Bata cika son Yara ba Amma Kuma Arfat na musamman ne hakama a yanzu indai a karkashin Dad Jden kake to so da kaunar Ameenatou da Arfat tamkar dole ne Kokuma ace farilla ne Dan haka suka Bada himmar sonsu Babu kakkautawa duk da lokutan da dama tsananin kishi da qyashin Ameenatou da Arfat Yana cin zuciyar Fatmah din Amma Didi na mata nasihar karma ta yadda ta bari shedan da son zuciya ya rinjayeta sbd Sune tsawon shekaru suke cikin daular dukiyar Dad Omar jden din suna rayuwarda bazaka taba cewan su din ba asalin jininsa bane kuma baitaba damuwa ba saima sake sakar musu da dukiya akeyi suna yanda sukeso amma ‘yarsa ta cikinsa tana can cikin ukuba da masifar data Kaita harga samun haihuwar ‘da mara Uba sai yanzu ta samu shiga rayuwar mahaifinta dan yana bayyanarda sonta da ‘danta fiyeda komai shine zataji haushi.

Wannan maganar ce take Dan danne Fatmah wasu lokutan da dama Amma Kuma zafi da kishin Hakan Yana cikin ranta sbd kusan a yanzu kowa girma da matsayin dayake bawa AM daban dana kowa,daga Dad omar din da kansa sai kuwa ita da ‘danta kafinma ita mata daddy din wato Ahmed ya biyo baya,
Hakama tsananin son da daddy Ahmed yake yiwa Ameenatou da Arfat ganin takeyi kaman ita yarsa ma baya mata irinsa sannan duk yawon kasashen datakeyi ta kasa tsaya guri Daya tayi karatu gashinan daga zuwan Ameenatou din ta tsayu su Dad din sun tsayu,su Babbah ma sun dage sun tsayu tayi karatu gashinan tana kokarin gamawa daga wannan exams din datakeyi hakama tini tafara shiga office a matsayin ‘ya Kuma Magajiyar Jden Daya kwal ita da ‘danta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected