AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Su Babbah ma basusan da cikin ba sbd kunya bazata iya barin Amina fadawa dadah tanada ciki ba bare Babba Dan haka tayi shiru batareda ta iya fada din ba har ciki yanata Kara kusantar cike watannin haihuwarsa.

*******Mummunan tashin hankalin farko Daya fara ziyartar rayuwar Alh Omar jeden seelah itace wayuwar gari da Akai da mutuwar secretary dinsa Daya kwana Yana aiki a office,

Kisa ce ta tsafta wadda seda Akai aka Gano ba Alh Omar din bane Dan kuwa a office dinsa yake Yana aikin dasuke buqatan miqawa da gaggawa a washe gari.

Da farko baa dauka kisa bace sai da aka bincika abinda ya kashesa aka Gano allura Akai masa wadda ta tsayar da bugun zuciyarsa take tareda tsiyayo jini ta hancinsa da kinnensa Amma sun goge sedai anga sauran jinin.

Duk iya bincike baa iya Gano komai gameda Wanda suka kashesa ba Kuma duk tsananin securities Dake office din suna Nan Amma sun Bada tabbacin Babu wani baqo ko wani Daya shigo a Daren.

Hakanan case din Alh mam seelah ya kashesa tareda sallamar duka securities din ma’aikata ya zuba wasu sabbi sbd bawa Dan uwansu tsaro.

Hankalin Omar Bai tashi ba sbd Bai dauka shi aka kawowa harin ba Amma dai baiji dadiba sosai shiyasa ma ya Saka familyn secretary din nasa cikin wainda nauyinsu yake kansa Dan tallafa musu.

Alh Mam da lameenu ransu yafara tsananta Baci tareda tashi tsaye ga lamarin Dan kuwa basa son wankin hula yakaisu dare har a samu matsala a abinda sukeso Dan haka suka sauya taku tareda Yanke shawarar Kai tsaye gama komai ba Jira.

A hanyar omar jeden ta zuwa airport da daddare zaiyi tafiya suka samu accident na Kai tsaye da yayi sanadin rayuwar drivernsa da raunin Aron sosai shi kansa ya Dan samu rauni kadan Amma dai Allah ya Hana komai samunsa.

Asibiti Akai dasu aka dubasa gawar drivern Kuma aka miqawa Yan uwansa bayan an gama komai hakama Aron an dubasa sosai tareda Omar din suka dawo gida.

Hankalin Omar da Aron da Ahmed tashi yafara yi sbd wannan shine karon farko da suka samu accident a Yan kwanakin ba Wanda Babu ranar da basa duba lafiyar duk motan da Omar zai hau ba.

Basu sake shiga tashin hankali ba Saida aka kawowa motocin Omar din hari ba da Rana tsaka a hanyar zuwa office hadda Harbin da baa samesa ba aka samu Aron a kafada Wanda ya Sakasa zubar da jini sosai take Yan Sanda da jamian tsaro suka kawo daukin gaggawa Wanda duk kariyarda aka bawa Omar Saida aka samu harbinsa a gefen hannunsa Shima.

Attackers din kafin ayi yunkurin kama su Daya daga cikinsu ya harbe sauran Daya bayan Daya Kuma ya gudu baa kamasa ba.

Yan jaridu da media tini suka cika wajen ana daukan rahotanni,
Hakama tini gaba Daya familyn seelahs suka shiga tashin hankali da firgici musamman Alh lameenu da Mam Dan harsun qarasa asibitin da aka nufa da Omar din.

Amina ba qaramin tashi hankalinta yayi ba Dan haka tini tafara kuka ta kira Babba ta sanar musu,
Su kansu babban hankalinsu tini yayi mummunan tashi dajin kukan Amina Dan haka ya ringa rarrashinta da Bata tabbacin suna Nan tafe Inshallah.

Washe gari asubar fari babba ya kamo hanyar Lagos a babbar motar Lagos Yana fatan Allah ya tsare Omar ya basa kariya sbd rayuwar Aminarsa taci gaba da zama cikin Jin dadi da gata da Kwanciyar hankali.

Saida ya kwana ya wuni a hanya kafin suka iso Kuma Yana isowa Kai tsaye asibiti yafara Isa daqyar aka barsa ya shiga da taimakon Ahmed ya dubo Omar din Wanda ake kokarin dawowa dashi gida.

Alh Mam seelah da Alh Lameenu seelah duk suna tareda Omar din a lokacinda ya shigo dubasa sedai kallo Daya dukkaninsu sukai masa suka dauke Kai Dan Babu Wanda yasan waye she bare inda ya fito hakama Shima Omar din Bai sanar dasu waye babba din ba.

Gida suka dungumo suka dawo harda babban Wanda Yana saukar da idanuwansa kan cikin dayake gaban Amina Jin yayi idanuwansa suna cikowa da hawayen farin cikin dabaisan zai taba ji ba idan yaga zuriari Aminarsa,
Yau Aminarsa ce daukeda juna biyu zata haifar masa wasu yayan bayan nasa.

Ita kanta Aminar ganinsa ya Saka Hawaye cikowa daga idanuwanta suna gangarowa masu dumi hakanan taji jikinta yayi sanyi da tsananin farin ciki da kewan Dan uwanta Kuma ubanta,
Inama zai zauna da ita harta haihu Kokuma a mayarda ita gida ta haihu a gaban dadanta da Babba Dan tasan Suma zasu so Hakan.

Farin cikinsa karuwa yayi ya qaraso lafiyayyar palon baqin da akai masa iso sanyin ac da qamshin arziki Tako ina Yana tashi ga wani sanyi da laushin carpet din tsakiyar palon dayake takawa suna ratsa jikinsa suna rage masa gajiya.

Qarasawa tayi itama ta zauna gefensa tana masa sannu da zuwa tareda tambayar meyasa Bai fada mata ya taso ba bare isowarsa ba.

Murmushin Jin dadi kawai ya sake Yana Jin kaman ta haihu kafin ya koma yayiwa abinda zata Haifa huduba da kansa kafin ubansa ya masa Dan ganin yakeyi ko uban cikin bazai Kaisa son abinda zaa Haifa din ba tinda ‘ya ko ‘dan Aminatunsa ne dole suga soyayya da gata uwa Uba idan yayi kudi karbe abinda zaa Haifa zaiyi inshallah.

Abinci aka kawo masa kala kala da abin Sha duk da Yana Jin gajiya Saida yaci ya koshi kafin aka Kaisa har boys quarter yayi wanka yayi sallah ya kishingida dan hutawa da rage gajiya.

Washe gari ma ya samu lokacin Omar sosai sun zanta hakama Amina da daddare kusan raba Daren sukai suna magana tinda asuba ya juya ya koma sbd ya matsu yaje yafara shirin haihuwar aminan yakuma fadawa Dadah Dan ya kasa fada mata a waya.

*****Abubuwa sunyita faruwa Daya bayan Daya na son daukan ran Omar Amma Allah na basa kariya sedai abubuwan sun fara tsananin gaske Dan kuwa ayanzu duk makusancin Omar yasan rayuwar Omar din na cikin hadarin da baa San daga Ina ne masifar ke fitowa ba hakama baa San su waye masu Neman rayuwar tasa ba a HANYOYI mafi Muni Dan aduk lokacinda Akai niyar illatasa sai anyi sanadin rayuwar wani har abin yakai yafara girgiza nutsuwa da rayuwar Omar.

Suk kansa su Alh Lameenu hankalinsu ma qaramin bayyanarda tashinsa sukayi ba shiyasa suka dauki mataki sosai aka sallami kaf securities na gidajensu da gurin ayyukansu suka zuba sababbi harma da jamian tsaro.

Wannan ne ya Dan kwantar da hankalinsu Ahmed da Omar din Amma kwata kwata nutsuwar Omar da tinaninsu sun shiga wani yanayin daban na tinanin dole akwai mummunan al’amarin Dake bibiyar rayuwarsa ba tin yanzu ba Dan kuwa mace macen da akeyi a rayuwarsa ya fara yawa daga wannan ya mutu sai wannan Dan haka yaji hankalinsa ya fita kwata kwata daga zaman Nigeria Kodan bawa iyalinsa kariya musamman Amina da abinda yake cikinta,
Ya tabbatarda duk me son rayuwarsa sbd dukiya ne to Dan haka bazaa taba son ya samu magajin dukiyarba idan har ita akeso.

To tin farko ma wayene me son dukiyar tasa?
Bayada abokan gaba,hakama shi mutum ne Mai Sirri da son rayuwar kaffa kaffa Bai bayyanarwa da duniya irin Fadi da yawan dukiyarsa ba Dan a idon duniya anfi sanin dukiyar su mam akan tasa Dan shi kusan duk Rabin dukiyar na Poland,bayan Yan uwansa Babu Wanda yasan adadin dukiyar da yake da ita.

To meyake faruwa a rayuwarsa ne?
Da gaske Ahmed yake na kusa dashi ne masu Neman rayuwarsa kokuwa dai bashi Omar jeden din ake Neman rayuwarsa ba?.
#MAMUH#
#JAMAAL JEEY SEELAH
#DEEP
#HAROON SEELAH
#LOVE
#CRAZINESS
#ZAFIN KAI
#AMEENATOU

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected