AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Ganin Jamaal ya sakata fashewa da kukan data kwana biyu bataiba tana tausayin yanda idan zai iya karbanta kaman yanda mum dinsa ta karbeta sbd tasan baya shiri kwata kwata da Mum dinta ko fuska Babu a tsakaninsu.
Mum dinsa shigewa jikinsa tayi ya rungumeta Yana kasa cewa komai sbd nauyin da zuciyarsa tayi sosai Kuma itama ta fahimci hakan takuma San radadin dayake cinsa gameda Dad dinsa wanda Kai tsaye tsakaninsu uku ita dashi da Omar da sukasan waye Mam sun San aikinsa ne.
Saida ta sanyaya masa abinda yakeji da kalamanta kafin ta Dora da yiwa lameenu dasu Aliyah fatan samun rahamar Allah.
Bai nuna damuwansa ga Ayesha ba saima gaisuwan rashin Mum dinta da yayi mata kafin ya amsa gaisawan maman fadeela akan rashinsu daddy lameenu din datai masa tukuna ya wuce sama.
Siddeeq ma gaisuwa sukaiwa juna kafin ya wuce bangarensa bayan yakai kayan Jamaal sama har bedroom dinsa ya sauko.
Tsit gidan yayi kaman rasuwar na dawo musu sabuwa sbd Babu wanda ya dauka Jamaal zaiyi zafin rasuwar sosai haka.
Siddeeq kuwa a ranar ya fara hada aikin da Jamaal din ya basa Dan kuwa Babu ruwansa ko waye Jamaal ya buqata Aiki akansa Yi zaiyi Dan haka take takardun hannunsu na duka wansa signing din Jamaal suke hannunsu ya hadasu guri daya
Sauran dukiyar Mam da basusan da ita ba take ya Saka qwaqwaran bincike akanta Wanda ta Nan ne ya samu labarin mutuwar BB da aka samu gawarsa a gurin bullet wanda Shima ya mutu.
Wanna qazamin labarin rufesa yayi Bai sanarwa Jamaal ba sbd Babu amfani bayan sake quntata zuciyarsa da lamarin zaiyi.
Sai dare Jamaal ya sauko bayan ya wuni cur a samansa bai saukowa ba sbd ciwon Kai na damuwar daya samu kansa a Ciki.
Mum dinsa da kanta ta Taya masu Aiki sukai girkin dinner wanda ba komai ta iyayi ba sai simple snacks irin cupcakes da pancakes sai hada tea, smoothie, milkshakes dasu fruities haka Dan haka ba Wani aikin tayiba Amma dai tayi nasa Cake dinta datasan shi kadai yakeci sbd Sam bayacin cake Amma idan tayi nata Yana ci.
Sun zauna dinner a natse ba hayaniya Cikin kwanciyar hankali sukai suka gama ya miqe siddeeq ya bisa suka nufi office dinsa na Cikin gida ya zauna Yana masa bayanin abubuwan daya fara hadawa wanda Jamaal ya gyada Kai Yana cewa yayi kyau.
Wayarsa ya fidda ya Saka Kiran Ameeenatou wadda a daidai wannan lokacin tana tareda babbah a palonsa Suna fitarsu tana ganin Kiran tasan numbernsa ce Dan haka taqi dauka ko kallan wayar Bata sake yiba harta tsinke.
Babbah wayar ya kalla yace
“Ba kiranki ne akeyiba budurwan Babbah?
Girgixa Kai tayi tana kasa kallan babban tace
“Lokacin daukan wayana ya wuce sai gobe idan an sake Kiran zan daga”
Murmushi yayi Cikin Jin dadin yar budurwansa ta zama mace ta musamman yanda yake fata tin tana yarinya Dan haka ya share Kiran Shima Suna cigaba da firarsu dadah ma ta shigo tareda Ashley da suke dakin dadah tin dazu Suna tasu zancen suka zauna Suna cigaba da firar gaba dayansu.
Sai 10 suka baro bangaren su babbah suka Dawo dakinsu sukai Shirin bacci lokacin tini Arfat yayi bacci Sarrah na dakinsa zaune tana gadinsa.
Tana Shirin bacci ta nufi dakin nasa ta kwanta tareda shi a gadonsa bayan ta sallami Sarrah ta tafi dakinta.
Washe gari da safe Didi da Mum Nur suka tafi Abuja Wani Taron da suka wakilci jdens.
Gidan tsit yake hakama Ashley tayi Shirin Aiki ta fita.
Ita kadai ta rage sai ARFAT wanda Shima dadah zaibi zasu fita tareda babbah zuwa auren Abokinsa Tin na wancan zaman da sukai a Lagos kafin rasuwar su Abdul.
Shirya Arfat din tayi ta takasa har mota driver na jiransu Cikin lafiyayyar motar babbah sabuwa da drivernsa.
A dawo lafiya tayi musu suka wuce ita Kuma ta koma Ciki Dan Shirin office.
Tana juyawa ana budewa motarsa qatuwar gate din mansion din ya shigo.
Taga shigewanta Cikin kayan baccinta Riga da wando masu Dan kauri da santsi.
Parking yayi tareda fitowa Cikin nutsuwa da Wani irin kwarjini da kamewa ya nufi Cikin gidan bayan ya amsa gaisuwan securities da suka taho sukai masa.
Bata Riga ta hau sama ba kitchen ta nufa ta Saka a hado mata Madara me zafi da sponge cake dayaji whip cream a qaramin plate an jero mata su a tray ta fito sbd batai breakfast ba.
Tana fitowa kitchen Yana shigowa qamshinsa ne yafara sauka Cikin hancinta ta dago a natse ta Kalli kofar tagansa Cikin class da Wani irin kwarjini yana tinkarota fuskansa me tsananin kyau da Haske tareda lafiya tana daukan Idanuwanta.
Baiyi tinanin samunta a palon ba Dan haka ganinta ya sakasa Jin zuciyarsa na warwarewa daga nauyi da damuwan datake Ciki gabaki daya
Ya zuba mata Ido Yana jifanta da kallan daya sakata ita dauke nata Idanuwan daga kansa tana qarasa fitowa tsakiyar palon daidai Nan Shima ya qaraso Ya Kalli abinda yake hannunta ya dago hannunsa daya ya miqa mata Yana cewa
“Hi,good morning Mrs Jamaal Seelah”
Wani kallo tai masa kafin ta Kalli hannunsa tukuna ta daga hannunta daya ta miqa masa tana Bude Baki a sanyin sauti tace
“Morning Dr”
Kame hannunta yayi tareda janyota gabansa suka hade sosai ya ja qamshin dayaketa jiran ya shigesa ko karfin jikinsa ya dawo.
Kayan hannunta tayi saurin nuna masa da Idanuwanta tana cewa
“Easy Dr,mu anan bama barna”
Wani Mayen murmushi ya sake Yana dago fararen Idanuwansa masu kyau ya zuba mata kafin ya kama hannunta daya ya Dora mata akan tray din da hannunta dayane kadai yake riqe dashi ya Kalli Cikin Idanuwanta da itama shi ta kalla ya daga mata girarsa daya da sautin daya kusan sakata sakin tray din yace
“Ok Nima bana barna lady am so zamu ga waye zaiyi barnar idan ta kama”
Riqe tray din tayi da hannu biyun tana kokarin matsawa daga kusan da sukai ya juyar da ita tareda rungumeta ta baya ya ziro kansa wuyanta kafin tayi motsin komai sai Jin bakinsa tayi a kunnenta ya saukar mata Wani sanyayyan ajiyan zuciya Mai dumi kafin yace
“Yaya kike??
Meyasa jiya Baki daga wayana ba?
Kinsan nayi kewanku kuwa?
Rawa tray din hannunta yafara Dan haka ta sake qanqamesa da kyau tareda hadiye Wani ajiyan zuciya me sanyi kafin ta Dan juyo gefenta ta kallesa daidai daman yana jiran hakan Dan haka kissing kawai ya sakarwa lips dinta Yana sakar mata Wani murmushi Yana qarasa zagayeta da hannuwansa Cikin Wani arnen salon daya Saka tray din hannunta kufcewa sedai dayake yasan zaayi hakan a shirye yake ya riqesa da sauri tareda hannunta Yana juyowa ya Kalli fuskanta murmushinsa na qaruwa yace
“Ohhh lady am na dauka gidan Nan bakwa barna kikace¿”
Rasa abin cewa tayi sai kawai ta sakar masa tray din tana cewa
“Ko yanzu ai barnar Bata faru ba kayi saurin riqewa ne Dan Koda baka riqe dinba ba faduwa zaiyiba sbd Ina riqe dashi ai”
Yanda tayi maganar ne ya kashesa da Sabon sonta Dan haka ya janyota jikinsa gabaki dayanta Yana zagayeta da hannunsa daya yai kissing hancinta kafin yace
“Koma me kikace ni Abu daya na sani shine I love you Ameeenatou Omar Jaden,
Ko Ameeenatou babbah zance ne ma wai?” Ya qarasa zancen Yana Jan qamshin jikinta duk da batai wankan safe ba kamshine kawai me sanyi ke fita jikinta.
Zamewa tayi tana cewa
“Breakfast zanyi zan fita office so bye”
Hanyar wucewa sama take kokarin bi dauke da tray din ba zato taji ya dauketa gabaki dayanta da tray dinta a hannu yayi saman da ita sbd wata irin tafiyanta data juya zatai data kashesa kaman zai rasa notin kansa biyu a gurin Cikin uku.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
134
Da sauri ta kalleta tana riqe kayan hannunta da qarfi kada zu zube tace