AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Sun Dan jima suna wayar kafin suka kashe ya Dan juyo ya Kalli siddeeq da sai a lokacin yake gaidashi ya amsa yana rufe laptop dinsa ya ajiye gefe yace
“Kayi magana da KAANTES?
Yaushe ne suka zaba lokacin meeting din?sbd nayi magana da NEYO shi Yana Angola daga can zai wuce Greece din”
iPad dinsa ya fitar ya Bude Wani sakon Yana cewa
“Eh,Sir Bilal kaante ya bada nasa ranar da yayi da sauran Holders din,
Sir DD KAANTE kuwa naga Kaine kuke magana shiyasa ban nemesa ba,
Sir AB TURAKI ma yace Se a ranar zai Isa,
Sir AA MAJEED Kuma Yana Greece din already sbd matarsa Dr Inayah dataje attending Wani program na likitoci na sati biyu ita da matar Sir MD ZABEERA wato Dr Amatu.”
Shiru JEEY yayi Yana mamakin AA MAJEED din da duniya ta sani babban mutum me class da dukiya tareda izza ace Yana Greece ya raka matarsa program har sati biyu shi da MD ZABEERA Wanda Shi Babu me ma daukan zai iya raka ko ubansa taro wata kasar sbd tarin ayyukan gabansa amma duka harya samu space din wannan yawon rakiyar mace.
Kai tsaye cikin basarwa yace ba damuwa zuwa gobe sai a hada komai a Siya ticket din na tafi.
Shiru siddeeq yayi Yana Dan Saka iPad din key ya dago ya Kalli JEEY din kafin yace
“Dad Seelah ma Yana cikin sabbin holders da aka samu,Kuma shima already yana Greece din hadda shi zaku hadu”
Shiru yayi batareda ya dago ya Kalli siddeeq din ba kaman yanda Bai ce komaiba,
Mintina suka dauka a Hakan kafin ya dago ya Kalli siddeeq din Yana basar da wancan zancen yace
“Ka sanar Dani time na tafiyana tin yau idan ka Siya ticket din”
Miqewa yayi ya nufi kitchen Yana son hada tea da kansa sbd tabbatarda iyawansa Dan gaba idan siddeeq Baya Nan Kokuma Idan shi dinne Baya Nan.
Siddeeq Bai bisa ba wayarsa ya fitar Yana waya cikin nutsuwa da gogewa akan tafiyar da sauran abubuwan da zasu gudana.
Yana cikin wayar Kiran sister Ashley ya shigo wayar JAMAAL Daya bari a palon,
Har Kiran ya katse Bai lura ba sbd wayar na silent.
Kuma shigowa kiran yayi sai a lokacin ya lura da Kiran ya dauki wayar ya kaiwa JEEY din kitchen Wanda kusan duk ya Bata hannuwansa da Coffee Da Madara Daya hada.
Tsayawa kallan abinda yayi siddeeq yayi kafin ya miqa masa wayar Yana cewa sister Ashley.
Handsfree ya Saka wayar tareda ajiyewa Yana saurarenta bayan ya dauka da cewa
“Yes,Ashley”
Abinda ta fada ne muryanta a shaqe cikin tsananin kuka ya Saka Siddeeq sallama ya kashe wayarsa Shima JAMAAL din abinda yakeyi ya dakata da yi Yana kallan wayar tasa.
Kashe wayar tayi sbd kukan dayaci karfinta batareda ta Jira amsarsuba Daman sanar musu zatai sbd Ameenatoun data baro asibitin.
Kashe tea maker din JAMAAL yayi tareda juyawa ya wanke hannunsa da kyau ya dauko towel qarami na kitchen din sabo Yana goge hannunsa ya kalli siddeeq daya shiga tashin hankali da damuwa take yace
“Kasan asibitin data fada right??
Gyada Kai siddeeq yai Yana juyawa suka fice sbd sister din tana buqatan taimakonsu a daidai yanzu tinda kusan batada kowa mijin Nan shi kadai ne gareta gashi yayi accident mummuna a hanyar dawowa daga tafiyarsa da yayi wadda siddeeq ya Kaisa Tasha.
Ko tea din babu Wanda yasha a cikinsu fruits kadai Jamaal din ya iya dauka apple Daya da tangerine biyu Kai tsaye asibitin suka nufa a mota yaci.
Koda suka Isa asibitin ba wata babbar asibiti bace Wanda ko likitoci kwararri Babu hakama likita daya ne a kansa Babu sauran likitoci wai basa Nan gashi ba qaramin muni lamarin hadarin yayi ba dole Dr JAMAAL dinne ya shiga Dan cetan rayuwarsa bayan sun tabbatarda shine Dr JEEY SEELAH da suke ji.
Sister Ashley kuka takeyi sosai tayi harta rasa karfin yin wani tana zaune tareda siddeeq Wanda yake yi Yana Bata hakuri duk bayan mintina suna jiran tsammani da abinda Allah zaiyi.
A ciki kuwa duk yanda Dr JEEY da Dayan likitan Daya koma kaman Nurse a gaban Dr JEEY din tareda sauran nurses sunyi iya kokarinsu Amma Allah yayi hukuncinsa ya karbi ransa Babu yanda suka iya bayan fara rubuta bayanai shikuwa Dr JEEY fitowa yayi zuciyarsa a matiqar jagule da cikakken tausayin Ashley.
Sister Ashley na ganin fuskan Dr JAMAAL ta rintse idanuwanta batareda ta iya budewa ta kallesaba sai data hadiye Wani yawu me kauri kafin ta sake kallansa.
Shikuma siddeeq ya fara kalla da idanuwansa da suka Dan sauya kafin ya dawo da kallansa kanta,
Siddeeq na ganin Hakan yasan Menene ya faru Dan haka Shima sister Ashley din ya kalla lokacinda Dr din ciki ya fito shine ya Bude baki Kai tsaye ya sanar mata tareda Bata hakuri ya wuce.
Kuka me karfi take Neman sakewa Amma yaqi fitowa sai kawai ta Yanke jiki ta zube a gurin tana fasa wahalallen kuka Mai tsima zuciya da tausayi me tsananin gaske.
Siddeeq ne ya biya qasan Yana Bata hakuri duk ba Jinsa takeyi ba.
JEEY ne ya Bada duka abinda zaa buqata na daukan gawan zuwa gida sbd a ranar ayi jana’izansa.
Karfe biyu da Mintina gawar ta Isa gida hakama shine da kansa ya ja sister Ashley din ya Kaita gida sbd lokacin Yan uwan mijin da suke kusa tini suka cika gidan da abokan arziki anata kuka da tashin hankalin rashinsa.
Yana ajiyeta gida ya wuce tareda siddeeq Daya iso gidan a motan da aka dauko gawan.
Asibiti yaso zuwa sbd Ameenatou Dake ita Daya Amma hakanan ya daure ya bari lokacin janazah din yayi suka halarta shida siddeeq kafin suka sake yiwa sister Ashley gaisuwa daga can asibitin suka wuce Siddeeq ya ajiyesa ya wuce gida.
Office dinsa y fara shiga ya ajiye wayarsa da laptop dinsa kafin ya fito ya nufi dakinta Kai tsaye.
Itada wata nurse ne a dakin suna rigimar abincin data qi ci kwata kwata a yau din sbd rashin Ashley Dan rigima ta wuni tanai musu Kuma su Basu iya lallabata ba kaman Ashley
Masifa da fada suke mata sosai Wanda ya sake rikitar da ita.
Bai shigo dakin ba daga kofan dakin ya tsaya Yana kallan yanda aketa fama da ita Amma taqi yadda taci abincin.
Numfashi Mai dumi ya sauke mara sauti tareda takowa ahankali ya shigo dakin Yana kallanta da idanuwansa da suka jima Basu ganta ba.
Itama idanuwanta da suka fada ta dago ahankali tareda kallansa batareda ta firgita ko matsawa ba harya iso gabanta ya tsaya ta Dauke idanunta akansa ahankali tareda Bude bakinta cikin tsananin sanyi tace
“Ameenatou sister Ashley takeso,
Ameenatou batason kowa”
Lumshe idanuwansa yayi ahankali cikin Wani irin sanyi da nutsuwa batareda yace komaiba sbd sautin nata Daya shigesa.
Nurse na Jin Hakan ta juyo ta kallesa cikin rawan Kai tace
“Dr tin safe muke fama da ita kwata kwata batacin komai sister Ashley kawai takeso Kuma sister Ashley Mai gidanta ne ya rasu yau din…”
Hannunsa daya ya miqawa Ameenatou din batareda ya tsaya sauraron nurse din ba Yana kallanta.
Kwata kwata taqi juyowa ta Kallesa bare nurse din saima Kwanciya datai tareda dunqulewa guri Daya tana rufe idanuwanta.
Shiru yayi itama nurse din ajiye cup din hannunta tayi tareda juyawa ta ficewanta.
Ya jima a gurin tsaye kafin ya juya ya fice,
Bai jima ba ya dawo dasu biscuits da chocolates da apples ya ajiye mata akan drawer ya juya ya fice.
Kaman ta sani Babu jimawa ta Bude idanuwanta Taga kayan da kanta ta tashi taci iya cinta tana Kiran sunan Ashley harta gama ta koma tayi kwanciyarta take bacci ya dauketa.
Karfe goma Sha Daya ya dawo dakin ya sake dubata a Karo na kusan uku yaga baccinta yayi nauyi ya gyara mata rufa ya fice.