AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Jamaal ma dayake tuqin tasa motar Jin yayi kaman zuciyarsa zatai bindiga sbd tsananin zafi da tafasan datakeyi.

Su babbah ma zagine kala kala yake jifan Mam dasu Yana tsinewa rayuwarsa gabaki dayanta tareda tausayin Dr Aleena Yana Kuma Jin Dan sassaucin abinda yakeji sbd hankadosa da yayi ta benen Yana fatar kansa ya fashe ko dayan idon ya tsiyaye.

Hafiz dai baice komaiba sbd damuwa da tashin hankalin abinda yake faruwa din.

Siddeeq ma Kai tsaye asibitin jdens din ya nufa sedai kafin su isa Siyam tayi Wani irin Nisan da hankalinsa yayi mugun tashi.

Mam ma mummunan hali yake cikinsa kafin a isa asibitin take jikinsa ya Dena Aiki sbd alluran da Akai masa hakama wata azabane da ita yanaji tana quna jininsa kaman ana yanka Naman jikinsa Amma Kuma Bai iya ko motsa yatsansa daya hakama idonsa daya dabai tsiyayeba baya Gani sosai sbd tsananin azabar dayake Ciki.

Duk azabar dayake Ciki radadin da zuciyarsa take Ciki na abinda ‘dansa na cikinsa da matarsa sukai masa tareda Omar shine Ciwo mafi zafi dayake ji Dan haka wasu hawayen azaba ne suke gangarowa gefen Idanuwansa.

Dukkaninsu asibitin jigum jigum sukai bayan an karba Mum zuwa Ciki da Siyam ma dasuka iso daga baya.

Omar da Jamaal har lokacin Babu wanda ya furta kalma ko daya bayan tsit da sukai kowanne da abinda zuciyarsa take Ciki wanda baya faduwa Dan haka kowa gurin ya sake shiga damuwa da yin shiru Suna jiran tsammani da fatan komai yaje daidai Dan basa fatan daga Mum din har Siyam su rasa ko daya.

Ameenatou na gida batasan meyake faruwa ba itada Ashley dasu Mum Nur Dan hakane suke fama da tasa gagarumar matsalar Cikin rashin madafa.

Baa dauki lokaci doctors din dasuke kan Dr Aleena kusan guda biyar sai kace wadda tayi mummunan accident duk da ba Wani rauni bane kawai dai shaqar da yayi mata ne ya galabaitar da ita.

Doctors din na fitowa bayani sukaiwa se Omar akan Babu matsalan komai gameda Dr Aleena bayan galabaita datai na toshewan numfashin Amma inshallah komai ya dawo daidai.

Siyam ce dai itama tana tsananin hali sbd daman ba lafiyayya bace sunyi mamakin samun lafiyanta lokaci daya sai Kuma mummunan shaqar da Akai mata data Riga takusa rabata da ranta Dan haka gaba daya lungs dinta ma sunqi karban numfashi anata kokarin dawo da numfashin dasu oxygen da dubarunsu na qwararri.

Ajiyar zuciya Jamaal da Dad Omar suka sauke a boye batareda sautin kowannensu ya fito ba.

Sai alokacin kowa ya sauke tasa a bayyane Suna Jin tashin hankalinsu ya fada.

Jamaal ne ya miqe ahankali Cikin nutsuwa ya nufi dakin siddeeq ya Bude masa ya shige fuskansa Babu walwala ko kadan sai Idanuwansa da sukai Wani mummunan ja.

Yana shiga mum din na Bude Idanuwanta Cikin nutsuwa da sanyi ta zuba masa tausayinsa Mai tsananin gaske Yana rufeta koina sbd tasan tsananin radadin dayake Ciki gameda Mam wanda yake mahaifinsa Kuma bazai iya masa komaiba daya dangaci zagewa ya masa mummunan wulaqanci Dan hakan ne zuciyarsa take cikin Wani irin suya da qunci me qarfin gaske.

Takowa yayi ahankali ya iso gareta
Kafin ya iso ta tashi zaune ahankali tana share hawayenta da suka gangaro ahankali
Zaunawa yayi ahankali gefenta ya Bude hannuwansa Cikin sanyi ta shige jikinsa ya rungumeta Yana Dan qanqameta Cikin sanyi da tsananin kaunarta.

Itama lafewa tayi jikinsa Cikin sanyi da tsananin kaunarsa ta motsa bakinta zatai magana ya tareta ta hanyar sake rungumeta bayan yayi kissing tsakiyar kanta ahankali Yana Bude Baki da wata shaqaqqiyar murya Mai tsananin sanyi yace

“I love you Mum,
I love you,.I love you”

“I love you too son” tafada itama tana sake lafewa jikinsa.

Sun jima a hakan kafin aka Bude kofar dakin ya dago jajayen Idanuwansa yaga su siddeeq ne da babbah sai Hafiz da uncle Ahmed daya iso Shima sai Maman fadeela da Ayesha dukkaninsu Cikin kulawa da kauna suke mata sannu tana amsawa batareda ta dago jikin Jamaal dinba.

Sama sama suka jajanta kafin suka fito Dan tafiya gida sbd doctora sunce ba zata kwana ba tana sake hutawa gida zaa koma da ita sai zuwa dare ko gobe su sake zuwa gidan a dubata.

Suna fitowa Hafiz da babbah da maman fadeela da Ayesha suka fice daga asibitin a motar Hafiz.

Fara biyawa gida yayi ya ajiyesu har lokacin Ayesha bata Cikin cikakkiyar hayyacinta sbd tsoro da tashin hankali da mummunan firgicin zuciya datake Ciki na abinda duka yafaru da abinda taji akan mutuwar Mum dinta Dan haka Suna isa gidan dakinta ta shige ta rufe tareda zubewa qasa ta fasa Wani irin Kuka Mai tsima zuciya da tausayi tana tinanin ta tabbata kenan ita batada kowa yanzu sbd Mam ne take tinanin Dad dinta da zaici gaba da zama mahaifi kuma ubanta Amma yanzu tsoron Jin sunansa ma da akeyi.

 

Bayan barin kowa asibitin sai alokacin Dad Omar ya sauke ajiyan zuciya Mai Dan taqaitaccen sauti Yana miqewa ya nufi dakin Kai tsaye Shima ya shiga Cikin nutsuwa da kamewa kaman ba Cikin tashin hankali ya fito ba.

JAMAAL da har lokacin Idanuwansa Basu dawo daidaiba sbd zuciyarsa datake tsananin tafasa da Kuna har lokacin ya dago ya Kalli Dad Omar din wanda Shima Idanuwansa suke sauye Cikin yayi kokarin daidaitasu da kansa.

Janye Mum din yayi daga jikinsa Yana miqewa tsaye bayan ya sake kissing gefen fuskanta ya juya ya fice
Siddeeq ma bayansa ya bi uncle Ahmed ma sannu yayi mata tareda juyawa ya five daga dakin bayan yaja kofar aka bar su iya su biyun Cikin dakin.

Shiru dakin yaji Babu wanda ya motsa bare magana.

Itace ta fara dagowa ahankali ta kallesa Taga Idanuwansa kafe suke akanta Yana mata Wani irin kallo zuciyarsa na tinanin da Mam yayi nasarar illatata Yaya zasuyi shi da Jamaal??

Takowa yayi ahankali tareda isowa har inda take tukuna ya zauna inda Jamaal ya tashi tareda miqa mata hannunsa Yana kallan Cikin tsakiyar Idanuwanta data kasa kallansa sedai ta dago hannunta da yayi mata Dan nauyi ta miqa masa tana Dan rintse Idanuwanta.

Kama hannun nata yayi da nasa tafin hannuwansu na haduwa a tare suka sauke Wani ajiyan zuciyan shekarun da suka debo tin kuruciya na jira da fatan wannan ranar.

Dagowa tayi ahankali ta kallesa Shima ita ya zubawa Idanuwansa da jan da sukai har Lokacin Bai washe ba sbd radadin dayake cin zuciyarsa.

Tasan zuciyarsa tafasa takeyi kaman ta ‘danta akan duka abinda Akai mata Dan haka ahankali ta daga hannunta daya wanda baya Cikin nasa ta Dora a gefen fuskansa ahankali ta shafa Cikin sanyi da nutsuwa da tsananin kulawa da so da rarrashi tana sauke hawayen da zuciyarta ta kasa riqewa sbd feelings da yawa.

Rintse Idanuwansa yayi Shima ahankali tareda sake damqe hannunta dayake Cikin nasa Yana Jin zuciyarsa na sanyaya ya Bude Ido ya sake zuba mata su zaiyi magana ta Dora hannunta ahankali kan lips dinsa tana kallan farar lafiyayyar fuskansa data manyanta sedai kyansa da ajinsa da lafiyan fatarsa tin ta kuruciya haryanzu Suna Nan musamman yanzu da asalin Hutu da kwanciyar hankali ne da Arzikin gaske suka ratsasa komai nasa kaman ma yafi kyau a yanzu.

Cikin sanyi da nutsuwa tareda son tausarsa ta Bude Baki da rashin kuzari sosai tace

“It’s okay,am okay inshallah Babu komai,banajin komai yanzu.”

Ajiyar zuciya ya sauke me sanyi Yana Dora hannunsa kan hannunta dayake kokarin sauka daga fuskansa ya maidasa datareda Dora nasa akan nata din Yana sake sauke ajiyan zuciya Cikin nutsuwa da kulawa tareda zafin zuciyarsa daya ragu ya furta

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected