AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Mahaifinta yakai a yanzu ayyukan wahala yakeyi ya samo musu abinci Dana ciko cylinder oxygen dinta,
Takai ta kawo ma yanzu ba cinsu da shansu yake nemowa ba oxygen dinta yake yiwa nema a wahala da kunci tareda tsananin rashi suke rayuwa.
Kusan lokaci me tsayi likitoci suka sauka akanta kafin suka samo numfashinta ya dawo daidai duk da ba sosai oxygen din take kawai lungs dinta ba sbd mugun Nisan datai
Allah ne kadai yayi tanada kwana a gaba ma da tini wani zancen akeyi Amma dai ta samu oxygen din Kuma Daman nata Dan kadan ne ya rage dole Dr Jamaal ya Bada umarnin aka Saka mata sabo na asibitin tasu.
Rubuce rubuce yayi sosai a file nata tareda zuba mata fararen idanuwansa masu kyau Yana kallanta kafin ya dauke idanuwan nasa ya maidasu kan rubutun dayakeyi ya gama ya miqawa nurse din Dake gefensa suka fito Yana zare gloves din hannunsa Yana tattaunawa da sauran likitocin suka nufi wata patient dinsa Dayake ji da ita dattijuwa ce sosai tana fama da diabetes duk ya rikitata kaman me matsalan kwakwalwa ga tsufa Dan haka aketa fama da ita shikuma Yana lallabata sosai shiyasa idan ba shi ya Bata magani ba Bata sha sai anyi daqyar.
Round yayi a asibitin ya duba patients sosai har kusan 11 kafin ya juyo ya dawo dakin dasu fadila suke ya sake dubata yayiwa iyayenta tambayoyi sosai akan ciwonta Yana sake rubutu acikin file din kafin ya Basu tabbacin Inshallah zata tashi Amma ba yanzu ba zata iya kawai gobe da Rana ko Yamma ba Dan haka su kwantar da hankalinsu.
Sai 12 ya koma office dinsa yana shiga Kai tsaye toilet dinsa ya wuce ya wanke hannuwansa sosai tareda fuskansa ya sake shafo sensitizers ya fito ya rage hasken office din yazauna tareda janyo laptop dinsa ya Bude bayan ya dauko ruwa me sanyi kadan daga fridge dinsa ya Bude yasha kadan ya ajiye gefe yafara aikin dayake gabansa.
Washe gari bayan sallan asuba kaman yanda ya Saba Saida ya sake duba patients dinsa da yawa harda fadila kafin ya wuce gida.
Haroon Bai zo ba driver ne yazo ya daukesa sbd safe ne sosai.
Suna Isa gida Kai tsaye part dinsa ya nufa Yana shiga ya tube kayan jikinsa ya jefasu laundry room dinsa ya fito da underwear kawai ya jikinsa ya nufi bedroom dinsa.
Wayarsa kawai ya kashe ya jefar kan sofa ya nufi toilet ya shige
Wanke bakinsa kawai yayi da mouthwash na spray mint flavor batareda yin wani brush din ba Dan yayi a office
Yana gamawa wanka yayo ba jimawa sosai ya fito daure da towel cikin nutsuwa ya shirya a gaban mirror tsaye kafin ya saka underwears da kayan bacci marasa nauyi ko kadan ya haye gadonsa ya rufe jikinsa tareda kashe hasken dakin take bacci ya daukesa me dadi da nutsuwa.
Baccin awa biyu da rabi yayi kafin ya tashi ya sake brush ya shirya ya fito cikin ash Armani’s ya nufi cikin gida Kai tsaye palon Dad dinsa ya nufa acan suka gaisa ya fito daidai fitowan Haroon suka nufi dining room tare suna magana.
Breakfast sukai suna gamawa suka fito Kai tsaye motarsa Bentley continental gt ya nufa ya Bude ya shige tareda tayarwa Kai tsaye ya nufi gate securities suka Bude masa gate ya fice
Shima Haroon ko gate din baa rufeba ya Saka kan tasa tsadaddiyar motar ya fice zuwa nasa office din.
SEELAHs ya nufa office dinsa Wanda yanada ma meeting da baqi da safen su Dad ma duk zasu halarta sbd mahimmancin Taron meeting din.
Se karfi uku da Rabi ,hudu saura mintina kadan ma ya baro office Dan haka Yana dawowa sallah ya fara yi a masallaci kafin ya shige.
A dining na palonsa ake Kai masa lunch dinsa ana jere masa Dan haka abincin ya zauna yaci Yana gamawa sake kwantawa yayi bacci sai yamma ya tashi yayi wanka ko abincin Dare baici ba ya fice sbd hankalinsa Yana asibiti.
Yana Isa acan yayi sallan magrib Yana fitowa masallaci office dinsa ya dawo dan yanada patient da zai duba.
Sai bayan ishai yasha ice tea a office dinsa da cake kafin ya fito round nasa.
Fadila ce patient ta karshe Daya duba Kuma yayi mamakin ganinta zaune Amma gaba Daya Babu farin ciki ko kadan a tattareda ita,
Mahaifiyarta tayi kuka har idanuwanta basa dubuwa ga damuwa qarara a fuskanta,
Shi kansa mahaifinta Yana cikin tashin hankalin sallaman da zaa musu basuda kudin oxygen nata
Sunsan Babu oxygen Babu rayuwar yarsu ne Dan haka suke cikin mafi girman tashin hankali.
Da farko Dr Jamaal din ya dauka damuwan tashin hankalin jiyan ne Bai sake su Dan haka ya sake Basu qwarin gwiwan ta warware Inshallah.
Godia sukai masa suna sake maimaita farin cikinsu akan taimakon gaggawan Daya bawa fadilan jiya.
Fadila Dake zaune idanuwanta a rufe da oxygen dinta a hancinta Bata iya Bude idanuwanta ta kallesa ba sai qamshinsa Mai sanyi da dadi Daya cike iskan gurin gaba Daya Yana Sakata Jin jikinta na sake mutuwa gabaki Daya.
Shima a hankali ya juya ya Dan kalleta kafin ya dauke idanuwansa akanta Yana barin gurin.
Ranar ma a asibitin ya kwana sbd sunada emergencies sosai Dan haka Koda gari ya waye sosai yake a gajiye yabar asibitin.
Kwanansu fadila biyu a asibitin aka sallamesu batareda an cajesu komaiba sbd Dr Jamaal din Daya sanar da Hakan.
Daqyar baban fadilan ya samo kudin da sukai refilling Rabin cylinder na oxygen suka tafi.
Sati biyu sukai suka dawo asibitin da ita Rai hannun Allah Kuma sukai babbar sa’ar Dr Jamaal na asibitin Dan haka Shine ma ya amshi matsalarta tareda shiga damuwa sosai sbd ganin Halinda take ciki yafi na Baya muni.
Daqyar suka samu numfashinta ya dawo bayan sunsha wuya sosai Dan haka Kai tsaye ya tattauna da iyayenta sosai ya fahimci tsananin rayiwan da suke ciki da azaban da fadilan Kesha tin tana yarinya har zuwa yanzu datake ganin kaman ta zama musiba ga iyayenta.
Da kansu iyayen suka ringa masa Hawaye suna rokonsa ya fahimtar da ita suna tsananin Sonta ahakan Basu taba gajiyawa da ita ba bare kallanta a matsayin musiba.
Lamarin fadila da iyayenta tsaya masa yayi arai Dan haka Ya karbi file dinta gaba Daya ya mayar da ita patient dinsa da shi kadai ne yake dubata hakama ya dauke musu siyan oxygen nata shine me siya.
Ta Dade sosai wannan Karan kafin aka sallamesu Kuma duk wanna taimakon da dadewan da sukai asibiti Bata taba dagowa ta kallesa ba sedai ta riqe qamshinsa da kaf asibitin Babu me irinsa bayan shi kadai,
Shi kansa Bai taba tsayawa ya kare mata kallo Dan ba dabiansa bane qarewa mace kallo dan haka tsakaninsu gaisuwa da Godia ne kadai Amma umman da baban sun Saba ahankali ahankali Dan sosai Allah ya Saka musu kaunarsa da tsananin ganin girmansa Dan tinda suke wannan dawainiyar ta ‘yarsu Babu Wanda ya taba taimaka musu sai shi Dan haka suke tsananin kauna da ganin girmansa.
#MAMUH#
#DR JAMAAL
#AMEENATOU
#HAROON SEELAH
#FADILA
#JEDEENDS
#THE SEELAHS
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
21
Acikin kankanin lokacinda bamai tsayi ba iyayen fadila suka zama tamkar wasu ahalin Daya hada jini dasu Dan kuwa sosai yake taimka musu bayan matsalan ciwon Fadila wadda a yanzu tafara Dan sakewa tana amsar rayuwarta da kaddararta sbd shi din Daya bayyanar mata da wata sabuwar rayuwar hakama tana ganin iyayenta cikin walwala sbd taimako da kulawansa sai kawai ahankali take kallansa da wani irin matsayi me girma.