AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Babbah,Hafiz da Dadah kuwa idanuwansu kaman zasu fado kasa sbd fitowa da gwalo mata su da sukai suna kalla hankali tashe da Kuma tsananin kewa da kaunarta me karfin gaske Dake azabtar dasu na rashinta.

Akan fuskan Babbah idanuwanta suka fara sauka ta tsaya cak daga Jan numfashin kuka datake Shirin yiwa Ashley.

Ko kyaftawa idanuwanta kasawa sukai ahakan ta maidasu akan Hafiz tana kalla,

Rawa jikinta yafara yi ahankali Yana qaruwa hakama ta kasa ko kyafta idanuwanta daga kansu.

Babbah ne ya taso da sauri ya tsaya gabanta cikin rawar murya da Mummunan karyewa da zuciyarsa keyi ya Bude Baki yace

“Budurwan Babbah??,
Babbanki ne,tareda Hafiz dinki
Ga Kuma dadanki……

Katsesa tayi cikin rawar da hannuwanta ke qarawa da Bude Baki cikin Wani sauti mara fita sosai ta furta

“Babbah,Babbah,
Ameenatou tanada Babbah,
Ameenatou tanason Babbah,
Ameenatou na son babbah….”

Wata shegiyar ajiyar zuciya su Dr ibrahim suka sauke gabaki dayansu a fili sbd tashin hankalinsu Daya fada lokaci Daya da jin kalamanta Dan kuwa shikenan ba matsalan tafiya da ita Dan Daman tashin hankalin da zaa zuba sukaiwa tsit cikin zufan tashin hankali.

Sake jero ajiyan zuciya md keyi Yana share zufa hakama Dr Charles,
Dr ibrahim kuwa a fili ya bayyanarda farin cikinsa Yana tayasu murna gabaki dayansu harsu Babban.

Su kuwa su Babbah jikinsu ne yayi mummunan sanyi da karyewan zuciya akan ganin Ameenatou dinsu da gaske dai ta koma Hakan.

Dadah kasa riqe hawayenta tayi ta fasa kuka ahankali mara sauti sosai tana tasowa ta nufo Ameenatou din Amma ko tabata bataiba tayi Baya tana girgiza Kai cikin sanyi na rashin kuzarinta tace

“Ameenatou batason kowa Ashley da JAMAAL Haroon da Babbah takeso”

Qarasawa tayi tana kallan Babbah da har lokacin shine a cikin ido da zuciyarta,
Jamaal take Gani da Ashley sai shi da hotonsa ya jima tin farko a cikin zuci da idonta harma da tinaninta Bata taba ganinsa ba a zahiran sai yau Amma Tsaf sunansa a bakinta yake.

Hafiz ne ya taso Shima ya tsaya gabanta tareda Kai hannu zai tabata ta turesa tana komawa bayan Babbah tana girgiza Kai a kasalance.

Kasa magana Babbah yayi sbd nauyi da radadin da zuciyarsa keyi,
Kirjinsa ma yaji yayi nauyi numfashinsa na Neman rokarewa Amma sbd kada a samu matsalan tafiyan tasu da ita saiya daure kawai Yana juyowa gurin su Dr Zakeer aka qarasa rubuce rubucen da zaayi aka Saka hannu da sunansa da komai ya Basu photography na id card nasa Dana Hafiz tukuna sukai sallama suka basa Ameenatou wadda take gefen Babbah kaman ba itaba.

Da farko kin tafiya tayi duk da Babbah ne yake riqe da hannunta da kansa Amma ta tsaya tareda maqalewa bazata ba gurin Ashley takeso.

Cikin mamaki suka kalleta dukkaninsu hadda su Dr kowa Saida ya shiga firgici harsu Babbah din.

Da sauri Dr Zakeer ya matso Yana kallanta cikin kulawa da tausasawa yace

“Ameenatou zata gurin sister Ashley ko??

Gyada Kai tayi tana kallansa,

“Yawwa, to idan Ameenatou tabi su Babbah zasu Kaita gurin Ashley ne harma da Jamaal Haroon Yana can gurin Ashley suna jiran Ameenatou da Babbah”

Wani sanyayyar murmushi ta sake Jin hadda Jamaal zata gani tareda juyowa ta Kalli fuskan Babbah Wanda ya rasa ya zaiyi bayan gyada mata Kai alaman Hakan ne.

Wani murmushin me Fadi ta sake sakewa tana kama hannun babban Daya sake miqa mata suka nufi kofa Dr Ibrahim da sauri ya bude musu yana musu a sauka lafiya.

Har gate Dr ibrahim da Zakeer suka rakosu suka fice Ameenatou na riqe da hannun Babbah gam kaman shine Jamaal din datake ta nanatawa da Ashley,

Duk lokacinda ta ambaci kalman Jamaal da baimasan ta inda ta gansa ba harta riqe sunansa Wani radadi yakeji sedai Kuma idan ta ambaci Haroon a karshen Saiya Tina waye Haroon din a gurinta ciwon yakesata cakuda sunansa Dana Dan uwansa batareda tasaniba Kokuma Bata iya Tina waye nata a cikinsu.

Har suka fito dadah hawaye takeyi tana sharewa hakama Hafiz duk karfin zuciyarsa ta namiji saida yayiwa Yar uwarsa Hawaye Dan itace kadai yar uwansa yanzu tinda Yaya Abdul ya tafi ya barsu.

Suna fitowa cikin sa’a suka samu taxi take suka fada masa inda zasu suka shiga Hafiz a gaba babbah da Dadah a Baya Ameenatou na tsakiyansu tana kallan koina idanuwa a Dan Bude sbd Bata taba fitowa waje Taga mutane haka sosai ba da hayaniya.

Park suka Isa
Hafiz ne ya biya driver kafin suka fito Kai tsaye motar lokoja suka shiga.

Tsananin Hayaniya da tarin mutanen da Bata taba Gani ba ya Saka kanta Wani irin daukan nauyi Yana sarawa sosai
Da karfi ta riqe hannun Babbah da hannuwanta biyu tana rintse idanuwa,

Suna ganin Hakan suka lallabata suka shiga mota Allah yasa ba Jira take motarsu ta daga daga tashar zuwa inda zasu.
#MAMUH#
#THE SEELAHS
#AMEENATOU

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
91

*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

**************
Sister Ashley Dake asibiti Rai hannun Allah sister dinta na ganin Hakan ta cire Rai daga tashinta Dan haka ta fara shirye shiryen tafiya gida da ita can Asalin garinsu gurin yan uwa dan idan ma mutuwan zatai ta mutu a hannunsu dan hakan sukeyi so sunfi son ciwo na tsananta a kaika gida kawai.

Kasancewanta Ma’aikaciyar jinya itama yasaka Bata Sha Wani wuya ba gurin samun Daman tafiya da ita Dan haka cikin kwana hudu tana samun sauki kadan ta tattarata ta dauko mota har asibitin aka dauketa suka tafi Dan hakama Koda abokan aikinta na asibitinta suka taho dubata antafi da ita Basu Sami damar ganintaba.

*********A Poland kuwa komai ya rikice sbd Hankalin JAMAAL da kwata kwata Baya tareda shi sbd rashin ji daga Ashley kusan kwana nawa Dan haka dole abokan Aikinsa da Baya communicating dasu ya nema Dan gap kansa yake da kuncewa akan Hakan.

Dr Charles tinda suka sallami Ameenatou yayi blocking Dr JEEY din a wayarsa batareda sanin kowa ba dan kada ma tsautsayi yasa ya nemesa idan ya tashi,

Dr ibrahim ma Hakan yayi ya rufesa bazai iya samunsa ba Dan haka dr Zakeer kawai ya samu sbd shima shi kadai yake da number dinsa Shima.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected