AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Har aka gama aka daure kan tsakiyar kanta tareda goge fuskanta ta gyara ta fito fes kyakkyawar budurwanta me daukan ido da hankali ta zauna jiran Hafiz din Wanda sai kusan 6 ya iso ya biya ta fito suka wuce tana narke masa fuskan Baizo da wuri ba saita fadawa Babbah baida aiki sai yawon fira gurin Yan matan da babu me kyau bare maana.
So yayi ya buge bakinta Amma sbd suna hanya ya danne zuciyarsa Yana harararta ta saki dariya me sanyi tana cewa
“Akwai wadda takeda kyau ne? bare kace karya nayi Maka ko sharri nai musu”
Shiru yayi mata yana jiran su Isa gida yaga ubanda zai hanasa yimata duka ayau dinnan.
Dariya taci gaba dayi masa kasa kasa tana jiran su Isa gida ta shige da gudu Dan tasan a cike yake suna Isa Saiya daki bakinta idan ba Babbah ko dadah suka ceceta ba.
Gap da magrib suka iso gidan tana Ganin sun kusa Isa kofar gidan tace
“Yaya Hafiz naga Kanata kumbura nidai kayi hakuri to Karka tabani tinda kaga oganka fa yake sona Kuma kana tabani zai iya baka aikin wahala a gurin aiki ka……
Kafin ya qarasa ya daga hannu zai buge bakinta sbd sun kawo gap da kofar gidan Dan haka tayi gaba da gudu ya shige gidan daidai fitowansa daga cikin gidan Da gaba Daya ya sauya iskan gidan da qamshinsa Daya sakata saurin dakatawa sbd kirjinsu Daya Hadu sbd baisan da shigowan kowaba kaman yanda itama data zo da gudun batasan da tahowansaba.
Cak ta tsaya gabansa tareda dago fararen idanuwanta ta zuba masa sauran murmushin dayake kan fuskanta data shigo dashi Bai qarasa bacewaba ta tsayar da idanuwanta akan fuskar Data Saka kirjinta mummunan bugawa hakama bugun zuciyarta qaruwa yayi tana kasa motsawa hakama tinaninta tsayawa yayi cak.
Kafin tayi Baya shine yafara Baya alokacinda kirjinsu ya Hadu batareda ya dago ya Kalli fuskartaba a cikin wani fitinanniyar nutsatsiyar murya me sanyi da kamalan Dake hade da kamewa yace
“Sorry” Yana rabata ya wuce batareda yako kalletaba bare sanin itace Ameenatou din.
Kasa motsawa tayi daga inda take tsaye harya fice daga cikin gidan yabarta da qamshin turarensa Daya cika hancinta Yana toshe kanta daga tinanin komai bayan na mamaki.
Hafiz ma dayayi kusan mutuwar tsaye daga abinda ya Gani din ya faru kasa motsawa yayi Saida siddeeq ya fito daga cikin gida Yana yiwa dadah saida safe daukeda basket din abincin da aka Saba kaiwa Haroon yagansu tsaye baisan meya faru ba Dan Bai dauka sun Hadu ba sbd saurin dayake son suyi Subar gidan kenan kada Ameenatou ta dawo su hade sbd Yasan waye JEEY idan zai iya komai har abada bazai iya kallan wata macenba Koda ba Sonta yakeyiba da sunan sake mata.
Ganin Ameenatou da Hafiz Basu ce komaiba ya Sakasa silalewa ya fice.
Ameenatou kasa motsawa tayi sbd duk da Babu haske sosai magrib tayi tana ita tantance sauyin Haroon dinta Koda ta iskan Daya bar mata tana shaqa ne da qamshinsa yake daban da dukkanin abinda hancinta ya taba shakar mata.
Hafiz dayaji ana kokarin tada sallah wucewa yayi ciki Yana cewa
“Ki wuce ciki naje nayi sallah na dawo mu Dora inda muka tsaya”
Daga kafarta Daya tayi datai mata sanyi tayi tana wucewa ciki bugun zuciyarta har lokacin Bai dawo daidaiba,batama tantance Menene ya faru ba mintinan da suka wuce,
Haroon dinta ne a gabanta ko kuwa sabon Haroon aka sauya mata a duniyarsa Babu abinda yake masa kyau da kasa Dena kalla idan ba itaba.
Tana shigowa cikin walwala dadah ta kalleta tana cewa
“Yanzu Haroon ya fita sedai baima zaunaba gaisawa kawai mukai siddeeq yace Abuja zasu koma da Daren Nan acan ya zasu kwana”
Hafiz Dake alwala Bai juyoba yace
“Mun Hadu zai fita Amma dai inaga kaman Bai gama warwarewaba Dan baima ganemu ba a duhun duk da Babu wani duhun”
Ameenatou data kasa magana har lokacin sai Daya gama maganarsa ta Bude Baki tana kallan Dadah da idanuwanta da suka sauya tace
“Kaina ciwo yakeyi Dadah aban magani”
Kallanta Hafiz yayi Yana ficewa tafiya sallah,
Dadah kuwa wayar hannunta ta karban mata tana cewa
“Kiyi alwala tukuna idan kin Sallah kunci abinci be Dena ba sai asha maganin”
Gyada Kai kawai tayi ta wuce tana Dora tana kirjinta dayake buga mata ba daidaiba Bata taba Jin Hakan ba sai tsoro ma yake Neman kamata inde na zuciyarta ta samu matsala bane aikuwa bara Babbah ya dawo.
*******Daga kofar gidan Kai tsaye Abuja suka nufa siddeeq ne Mai tuka motar shikuma Yana waya da mum dinsa wadda yake magana da ita a natse cikin Kwanciyar hankali Babu hayaniya bare daga murya ko sauri,
Kaman yanda yake komai a natse haka yake wayoyinsa a tsanake da aji.
Suna Isa Kai tsaye lafiyayyar gidan da aka kama masa aka sauya mata komai zuwa yanda zai iya rayuwa a cikinta kaman Yana Poland haka Akai mata siddeeq ya nufa dashi ga securities sosai a anguwan Amma dai shi Babu Wanda ya dauka Dan qasar ne sbd yanayinsa Dan kamanninsa tareda irin tsarin rayuwar dayake gudanarwa.
Sama da qasa ne Dan haka Kai tsaye sama ya wuce siddeeq Kuma bedroom dinsa aqasa yake.
Yana shiga bedroom dinsa wayarsa ya ajiye tareda id card na Haroon dayake jikinsa ya kwabe kayan jikinsa dagashi sai wani tsadaddiyar underwear Dake jikinsa ya nufi toilet Yana shafa gashin kansa me tsayin gaske Daya Yanke sbd Haroon.
Wanka yayo kusan mintina masu Dan tsayi kafin ya fito dauresa towel dinsa datake Neman zamewa ta Fadi fatan jikinsa fresh sai kyalli takeyi ya nufi mirror Yana kokarin miqa hannunsa kan body oil dinsa wayar Haroon Dake kunne gefen tasa kira ya shigo cikinta Wanda ya sakashi dakatawa daga abinda zai dauka Yana kallan sunan sake rubuce kan screen din da manyan letters ‘DAD’
idanuwansa ya dauke daga sunan Yana qin daga Kiran Kai tsaye har Saida ta tsinke Kiran ya sake shigowa daidai lokacinda ya ajiye towel Dake hannunsa qarami yayi receiving call din Wanda Dad Bai tsaya komaiba yace
“Haroon Ina buqatan ganinka a Lagos gobe kome kakeyi ka ajesa ka biyo flight”
Bai tsaya Jin amsar Haroon din ba bare tambayar jikinsa ya kashe wayarsa.
Wayar JAMAAL ya zubawa idanuwansa da suka sauya take kafin ya saki wani mayen numfashi a natse.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
42
Kayan baccin Avves masu santsi da tsadan gaske ya Saka sedai baima rufe gaban riganba ya fito lafaffiyar cikinsa dake fidda murdewan jikinsa sbd motsa jiki ya sauko kasa sbd Yana buqatan ruwa da drinks sbd aikin da zai kwana yanayi sallah Kuma Daman kafin su baro Nasarawa sunyi ishai ma kafin su shigo gidan sunyi.
Siddeeq ma tini yayi wanka ya shirya cikin gajerun kayan baccin da sukaiwa jikinsa kyau Shima Dan Shima Yana motsa jikinsa sosai Dan hakane ma yafi Haroon budaddiyar jiki kaman ubangidansa.
Shima fitowansa kenan yaji saukowan JEEY da kamshinsa Dan haka ya dakata harsaida ya sauko kallo Daya yayi masa ya dauke idanuwansa sbd JEEY SEELAH ko namiji Dan uwansa yake kallansa zai iya kamuwa da sonsa bare mata Danma Baya mu’amalantar inda mata suka yawaita da baasan irin matan dazai samu masu jiransa ba, har mamakin yanda JEEY din ya kamu da son fadila yakeyi da yanda zuciyarsa take riqe da iya ita kadai yakeyi.