AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Sake shigowa Kiran yayi a Karo na biyu,
Qin dauka daddy lameenu din yasake yi shikuma Dr Dee din Bai Dena kiranba.
Satan kallan Mam yayi a fakaice sbd karantar yanayinsa Amma Kuma kwata kwata hankalin Mam din Baya kansa,
Yafi kowa sanin Mam Dan haka Hakan ba shine ke nufin Bai Ankara da rashin daukan wayansa ba duk da rashin daukan waya garesu normal Abu ne da kusan haka rayuwarsu take Dan ba kowane yake kira su dauka din ba tinda kusan dabia ce ta wainda Naira ta jiqa suka jiqu,
Suma Hakan ne garesu basa daukan waya Sam ta kowa Amma Kuma Mam kallo Daya yake Maka ya karanceka tsaf batareda ya nuna Hakan ba Dan shi Baya Saka ido yake gane abu,
Hakan ne ya Saka daddy lameenu din kasa samun nutsuwa Dan kobai daga ba Mam zai iya karanto Wani abin Wanda Komin qanqantar abinda zai fahimtar to tabbas Saiya gane sauran bayanin Dan haka daddy lameenu dole ya kame fuska ya daga wayar cikin nutsuwa da Kwanciyar hankalin dayake yafawa kansa na karfin hali ya Dan sake fuska Yana cewa
“Hello barka da Rana Honourable”
Cikin tashin hankali Dr Dee da baima San shi aka kira da honourable din ba yace
“Ranka ya Dade Dr JEEY SEELAH ya lalatamin career kwata kwa…..
Wani mummunan Tari me qarfin gaske ne ya tirnike daddy lameenu din sakamakon yawun bakinsa da suka wuce ba daidaiba da abinda Dr Dee din ya fada dayafi sakwon mutuwa tashin hankali a gurinsa gashi ba Daman tambayar wane JEEY SEELAH din Mam Yana zaune ya jisa,
Shi Kam wane babban bala’in ne wannan ke Naman rikito masa?
Tayaya Yana cikin masifar rashin Kwanciyar hankalin Mam karya Gano komai gameda abinda yake boyewa,
yanzu Kuma Rana tsaka wannan Yana ce masa Dr JEEY?..
Innalillahi wainna ilaihirrajiun” ya Karanta a zuciyarsa kusan so goma Yana Jin jininsa na neman tafasa ya kone a gaban Mam batareda ya iya motsawa ba Dan motsinsa kadai Mam ke jira ya fahimci abinda yake ciki.
“Ya Allah ka dauki ran Dr Dee dinnan yanzu yanzu idan ya fita daga inda yake sbd wannan mugun balain da masifar dayake Neman Sakasa.”
Dr Dee dayake kan wayar yanata zuba bayani cikin tashin hankalin dayake ninkar masa baisan daddy Lameenu tini ya ajiye wayar gefensa ba batareda ya kashe wayar ba sbd rikicewa.
Tarinsa Bai tsayaba har lokacin hakama Mam Bai juyo ya kallesaba Sedai a natse hankali kwance ya dauki cup din ruwan sanyin Dake gabansu tareda roban bottle water da aka tsiyaya a glass cup din ya miqawa Lameenu din Bai dagoba har lokacin karatun emails din yakeyi a natse yace
“Lafiya dai??”
Ruwan daddy Lameenun ya karba ya Dan sha kadan Yana gyaran muryansa sbd ruwan da suka tsaya masa su qarasa wucewa Shima a nacen Yana calming kansa yace
“Eh, inaga Yana tareda mutane baimasan ya kira din ba,
Idanma Wani abin ne zai sake kira inaga.”
Cigaba sukai da abinda yake gabansu Amma kusan hankalin daddy lameenu ya kasu kashi kusan goma Amma bazaka taba gane Hakan ba.
Sun jima suna tattaunawa Kuma tsawon wannan lokacin Dr Dee Bai Dena kira ba Amma dayake daddy lameenu din ya Saka wayar silent take shi yasa shi kadai ne me ganin shigowan Kiran da tsinkewansa.
Suna gamawa daddy lameenu ya fito Yana kokarin Saka Kiran BB ya nufi office dinsa sedai kafin ya Isa lift ta Bude da Dr Dee Dan haka kusan tare suka Kalli juna cikin mamaki da tashin hankali sedai na daddy lameenu din a boye yake Babu wani abu na damuwa ko tashin hankalin a tattare dashi.
Gaidashi Dr Dee yake kokarin yi ya amsa masa a taqaice tareda sanar dashi yaje zasuyi magana anjima zai nemesa yanzu yanada baqin da zai Gani.
Cikin tashin hankali Dr Dee ya biyosa zuwa office dinsa suna shiga ya Kalli Daddy lameenu din muryansa na sarqewa yace
“Dr JEEY SEELAH ya……
Dakatar dashi daddy lameenu yayi da zaunawa kan kujera ya ajiye wayarsa gefensa yace
“Wane Dr JEEY SEELAH din kake magana?
Kasan shi ne?
A Ina ya sanka dazai Maka koma Menene kake kokarin fadan ya makan?
Dr JEEY SEELAH Daya ne Kuma Baya qasar ba Kuma zai taba dawowa kasan ba..
Cikin Wani irin dacin zuciya da damuwa Dr Dee yace
“Dr JAMAAL JEEY MAM SEELAH guda Dayan daka sani nake magana Dan kuwa Yana qasar Nan…..
Wani sarawa Rabin kan daddy lameenu yayi ya dago idanuwansa sai alokacin ya zubawa Dr Dee su yanason Tantance kodai alluran mahaukan asibitinsu ta cakesa ne ta samman masa juyewan kan,
To Amma a yanda ya fada cikakkiyar sunan JEEY din alamace ta kaman daidai yake.
“Dr Dee ka tabbata JEEY SEELAH ne dai namu kake magana Akai??
JAMAAL SEELAH ‘dan Mam??
Kasa magana Dr Dee yayi saima zaro takardansa ya ajiye gaban Daddy lameenu din Yana dafe goshinsa tareda rintse idanuwansa da sukai jajir kaman zasu fashe.
Daukan takardar daddy lameenu yayi ya karanta Bai qarasa ya tabbatarda wlh tallahi aikin JEEY din Kuma Hakan na nufin Yana zargin Dr Dee din Kokuma yafara fahimtar akwai Wani abu a qasa game dashi Dan haka yaji zufa na jiqasa.
Dole Yana Neman batar da sheda ko duk wani abu da zai danganta sunansa ko da Saka hannunsa akan abinda yake faruwa acikin asibitin bare kofar asirinsa su bude gaba daya qiyamarsa ta tsaya.
Kallan Dr Dee yayi da idanuwansa da suka sauya take yayi Yana hango masifun da zasu biyo bayan sanin Abu Daya da JAMAAL zaiyi daga Dr Dee hakama a yanda Dr Dee dinnan yake a rude a rikice cikin tashin hankali da son riqe position dinsa na asibitin JEEY zai iya samun Wani sirrin daga garesa Wanda shine karshen tashin hankalin da zasu shiga shida su BB Dan haka dole ya sassauta ya sake numfashi cikin nutsuwa da kwantarwa Dr Dee din da hankali yace
“Dr Karka damu da wannan takardar Babu abinda zai faru Nima ayau dinnan basai gobe ba zanyi magana Koda zaka tashi goben zaka samu kyakkyawar rayuwa tana jiranka inshallah.”
Kasa Kwanciya hankalin Dr Dee yayi Amma hakanan daddy lameenu ya tabbatarda ya kwantar masa da hankali tareda masa alkawarin sabuwar rayuwa kafin goben inshallah Dan haka ya sake tareda Jin nutsuwansa ta dawo jikinsa.
Hadda kudi masu kauri daddy lameenu din ya basa kafin sukai sallama bayan sun Dan jima suna tattaunawa ya wuce.
Yana ficewa waya daddy lameenu ya dauka ya Saka Kiran BB Wanda Shima daga kwancen dayake tashi yayi da karfi Jin Jamaal na qasar ya dawo Amma Kuma ya Akai duk baza idanuwa da kunnuwan da sukai Basu taba sanin ya sauka kasarba.
##MAMUH#
#AMEENATOU
#BESTLOVE
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
70
A gida ranar JEEY ya wuni wayansa a kashe batareda ya koma asibiti ba ya huta sosai sai yamma sosai bayan la’asar ya shirya da kansa yaja motansa yau cikin ash Armani’s ya nufi asibitin.
Koda ya shigo asibitin office dinsa ya nufa Kai tsaye Saida yayi wasu ayyukan kafin ya fito sallan magrib Yana fitowa magrib Kai tsaye dakinta ya nufa.
Duk inda ya wuce ya Hadu da ma’aikata ko nurses cikin girmamawa ake gaidasa tareda masa barka da shigowa cikin turanci sbd da yawa Basu sani ba ko Yanajin Hausa ko Wani yaran.