AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Ajiye cup din hannunta tayi tareda daukan wayar cikin girmamawa suka gaisa ya sanar da ita Dr JEEY SEELAH din na buqatan ganinta.
Shiru tayi tareda sauke ajiyan zuciya ta Kalli time Taga magrib ma ake kokarin Kira yanzu gashi Bata Isa gurin nata aikinba tasan Tama Riga ta samu matsala kenan idan ba Allah ya rufa mata asiri ba.
Numfashi ta sake saukewa ahankali kafin tace
“Ok Ina bawa Ameenatou Abinci ne gaba Daya yau din bataci komaiba ganinan zuwa…
“No ki bata kawai just send me block da kuke da ward sai room number dinta.”
“Ok sir Inshallah yanzu Nan”
Kashe wayan siddeeq yayi tareda kallan JEEY Dake waya a natse suna jiran a shiga sallah su shiga.
Tin suna sallah siddeeq yaji shigowan Sako Dan haka suna fitowa ya sanar da JEEY din Wanda Yana Jinsa ya kashe wayarsa Yana kallan time Dan a Daren zai fara shiga bangaren patients din ya dubasu.
Suna komawa office siddeeq yabar asibitin shi kuwa wayarsa kadai ya Saka aljihunsa ya fito.
Nurses uku ne da likita biyu a tareda dashi lokacinda ya Isa kofar dakunan patients din suna masa bayanin kowace patients da abubuwan datake Kai tin daga kan allurai da magani da sauransu.
Suna zuwa kan patients din karshe sister Ashley ta shigo dakin da sauri sbd da ita yakamata ayi round din Amma tana can gurin Ameenatou Dan haka tana shigo Fahat ne ya ambaci sunanta qasa qasa Wanda sunan ya sauka a kunnen Jamaal ya dago idanuwansa masu hasken gaske ya Dan kalleta a taqaice tareda cigaba da sauraron bayanin da ake masa.
Ita kanta sister Ashley din Satan kallan JAMAAL din tayi tana mamakin yanda zasuyi Aiki da bature gashi hausansa dai kaman ya iya kaman be iya ba ta Wani bangaren tana mamakin Menene alaqansa da Ameenatou.
Suna gamawa ya fito Kai tsaye masallaci ya nufa sallan ishai suna fitowa Kai tsaye office dinsa ya wuce sbd Shirin wucewa gida.
Karfe Tara da Mintina sister Ashley tayi Shirin tafiya gida tinda yanzu tabar gurin Ameenatou ta dena kwana asibitin daga jiyan,
Dakin Ameenatou din ta nufa Kai tsaye da Jakarta a rataye tana Bude dakin Ameenatou na kwance shiru idanuwanta a rufe kaman me bacci Babu kuzari a jikinta Bude kofan sister Ashley Bai Sakata Bude idanuwanta ba Saida taji shiru ahankali ta Bude idanuwan suka sauka a bayan sister Ashley din ta lafe kofan dasu batareda ta motsaba.
Tsaye yake a bakin kofan dakin daga bayan sister Ashley da batasan da zuwan nasa ba Dan kusan tana Bude kofar dakin Yana kawowa dakin Shima Amma Bata lura dashi a bayanta.
Idanuwansa ya zuba mata Yana kallanta a natse duk da baisan asalin kalanta ba Yana iya ganin qarin haske a fatarta tareda sanyi,
Zuba masa nata fararen kyawawan idanuwan tayi tana samun kanta da tinanin ranar farko data fara ganinsa a rayuwarta da zuciyarta da tinaninta da Babu abinda ya Tina sai shi din ayau.
“HAROON” ta furta batareda ta motsaba cikin Wani tattausan sauti me tsananin sanyi da mutuwan jiki.
Shine abu daya da zuciyarta ta kasa mantawa,shine Abu Daya da ruhinta ya riqe,shine kadai suka da so da tinanin daya kasa ficewa kwata kwata daga kanta duk juyewan kanta,
Dashi da Babbah ne zuciyarta take azabtuwa da buqata da sonsu Amma kanta ya kasa Bata Daman Tina Hakan,
Sune tsananin dayake azabtar da kanta akan son tinasu Amma kan yaqi aminta da Hakan Dan haka ganinsa shi a yanzu gabanta ya yaye duk wani duhun sonsa da juyewan kanta ya rufe,
Duk da Bata iya Tina komaiba ko sanin ita wacece Amma ganinsa ya Bude zucuyarta dayake ciki.
Sister Ashley data shiga shock na sunan da Ameenatou din ta ambata da sauri ta juya bayanta gabanta na faduwa idanuwanta suka sauka akan Dr JEEY din Dake tsaye kofar ya kasa karasowa sbd Jin sunan Data ambata a Karo da farko datai magana ta nutsuwa tin fara haukanta.
Mutuwan tsaye sister Ashley take Neman yi da mamakin sunan datake Ji a bakin Ameenatou kullum dare yau ta kalli Dr JEEY SEELAH ta ambacesa da sunan bayan idan tanaji daidai shi Dr JAMAAL seelah ne sunansa Kuma sunan Haroon kaman sunane na daban Shima.
Hannuwansa Dake zube acikin aljihun wandonsa ya zare ahankali tareda sauke numfashi me nutsuwa mara sauti ya Tako ahankali cikin nutsuwansa ya shigo dakin
har tsakiyan dakin ya iso sedai kafin yayi Wani motsi daga inda yake ga mamakin sister Ashley Ameenatou din miqewa tayi ahankali cikin Tsananin sanyi da nutsuwa tareda rashin kuzari ta sauko gadon a Karan farko Bata damu da sanyin qasa ba ta miqe Babu takarmi ta nufosa tana masa Wani irin kallo iduwanta na cikowa da Hawaye,
Sister Ashley kallon tsoro take binta dashi
Shi kuwa numfashi me dumi mara sauti ya kuka saukewa Yana kokarin juyawa ya fice daga dakin sbd yasan anriga an samu matsala tinda yasan me take nufi da ambatarsa da Haroon,
Sedai ko taku biyu baiyiba ta ra zira hannuwanta biyu ta rungumesa ta bayansa tareda fashewa da kukan daya Saka sister Ashley sake fiddo idanuwana tana rasa mema zatai.
Shikuwa cak ya tsaya sbd abune da Bai taba tinanin zai faru ba hakama Bai taba tinanin zata iya Tina Koda Haroon din ba a wannan yanayin datake ciki…..
Qanqamesan datai ya sakashi Dago idanuwansa ya kalli sister Ashley da itama shi ta kallan da sauri.
##MAMUH#
#BESTLOVE
#HOTLOVE
#EMJAY
#B ARFAT SEELAH
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
67
Sister Ashley ya sake kalla da alaman Yana buqatan taimakonta a gurin batareda ya furta ba itama Kai tsaye ta fahimci Hakan sbd qaramar kyakkyawar runguma Ameenatou din tai masa ba Wanda tasan banbareta daga jikinsa kai tsaye zaiyi wuya amma bata tsaya tinanin hakan ba tayo kansu da sauri tinani kala kala fal cikin kai da ranta ta miqa hannunta a natse kan Ameenatou din tareda ambatar sunanta cikin tsananin kulawa da tausasa harshe zata janyota
Sake qanwamesa tayi da sauri har lokacin Hawaye ne ke gudu daga idanuwanta ta rintsesu da karfi tana girgiza Kai da karfi tana sake mannuwa da bayansa kaman zata tsaga bayan nasa ta shige.
Rintse idanuwansa yayi sbd ba qaramar runguma tai masa haka zalika kukanta sauti yake qarawa har lokacin girgiza Kai takeyi da karfi a bayan nasa tana Ambatar sunansa can qasan maqoshinta da Baya fita sbd kukan datakeyi.
Sister Ashley kallansa ta dago tayi tana sake Kai hannuwanta duka biyu kan Ameenatou din zata banbarota ba tsammani ta sakar mata Wani irin ihun kuka wannan Karan tana kokarin dawowa gabansa ta qanqamesa yayi saurin juyowa da Sauri ya zareta daga jikin nasa tareda yin Baya kadan kafin yayi yunqurin magana ta sake shigewa jikinsa kai tsaye wannan karan ta gabansa ne ta shige kai tsaye ta zura hannuwanta duka biyun bayansa ta qanqamesa tana sake fashewa da sabon kuka.
A rayuwarsa kaf bayan mahaifiyarsa data haifesa Babu macen da a taba runguma a jikinsa Kokuma jikinsa ya Hadu sosai da nata sai yau,