AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Sakin curtain din yayi cikin tsananin mamaki tareda juyowa Yana ziro slippers a kafafunsa Shima jacket din ya Sako kan kayan baccin jikinsa ya fito Palo Kai tsaye Yana nufar kofar ficewa daidai Nan mum itama ta fito tana cewa

“Lafiya kuwa?
Meyake faruwa?

Batareda ya juyowa ba yace ta koma daki zai dubo meyake faruwa.

Yana fitowa harabar gidan Dad ma Yana fitowa cikin mamaki da shakkar abinda ya fidda Haroon a lokacin.

Securities din gidan ma duka suna tsaye a harabar gidan

Dad da mamaki yace

“Meyake faruwa?
Waye ya fita da motan Haroon din?

Jamaal kuwa Yana isowa Kai tsaye yace

“Wats going on here?”
Waye ya fita?
Ina Haroon?

Daya daga cikin securities dinne ya Kalli Dad yace

“Sir,sir Haroon ne ya fita Amma security Daya yabisa sbd dare ne sosai Kuma baima tsaya mukasan meye matsalan ba ya….

Jamaal da kallo Daya yayiwa gate din da Haroon ya fice Bai tsaya Jin sauran zancen ba ya juya ya koma Kai tsaye key ya dauko da wayarsa Daya kunna Yana kokarin Kiran numbern Haroon.

Dad na ganin fitowansa da key cikin mamaki da tashin hankali yace Maza securities su janyo mota su bisa Dan bazai bari yayansa duka biyu su fice a Daren ba batareda yasan meyake faruwa ba da rashin tsaro.

Mum ma hankalinta tashi yayi mummunan yi da sauri ta dauro jallabiya me girma akan kayanta ta fito Amma Jamaal yace kada Dad yabari ta biyosa.

Daukan wayar Haroon yayi daidai da isar Jamaal motarsa cikin murya Mai sautin Kai tsaye yace

“Meyake faruwa?
Meyasa zaka fita a wannan time din?
Bazaka iya sanar da kowaba kafin ka fita?
Ganinan fadamun inda kake kawai…

Shiru yayi tareda dakatawa daga Bude motan dayake kokarin yi maganar da Haroon din ke fada cewan gobara ne sosai ya kama gidansu fadila.

Wani mummunan jiri ne Mai qarfi sosai ya debesa yayi saurin daga motar
Mum ma da saurin gaske ta qaraso gurinsa itada dad tana tambayarsa Menene Amma Sam Bai ya cewa komaiba sai idanuwansa da suka sauya take ya dago ya zuba mata Saida gabanta yayi mummunan faduwa.
#MAMUH#
AMEENATOU
#ZAFIN KAI

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
25
Dad na ganin Hakan yayi saurin kallan Abdul Yana cewa Maza a fiddo mota a biyo bayansu da ita sbd yasan koma ya cewa Jamaal yayi zamansa ba zaman zeyiba Dan haka ya koma ciki Ya Sako jallabiya doguwa fara kal ya fito.

Koda ya fito tini Jamaal yabar gidan Dan haka Kai tsaye shi da mum da securities suka mara masa Baya zuciyarsa na nauyi da fatan kada komai ya samu ‘yayansa a cikin wannan sililin Daren ace sun fita Babu Wanda yake tareda jamian tsaron lafiyarsa a cikinsu har gwara Haroon ance security Daya ya bisa
To Jamaal fa¿.

Mum kuwa duk a tsorace take ma kwata kwata sbd tsoron idan ba wani abin ne ya faru ba me girma ko zai faru,
Koma dai Menene itadai fatanta Allah ya tsare mata ‘yayanta ya Basu kariya da kaucewa musiba da masifa kowace iri.

Dad daya kasa tantancewa ko canko Menene yake faruwa shiru yayi Yana fatan Isa ga yayansa cikin gaggawa kafin kome zai farun ya faru tukuna…

Bayan motar Jamaal suke hangowa Yana gudu sosai Wanda ya Saka jinin Dad fara Hawa Yana Jin zuciyarsa na wani irin tsalle da rawar tashin hankali Dan kuwa Jin yayi kaman zuciyarsa ne a cikin motar Jamaal din ana wannan gudun da ita.

Mum kuwa idanuwanta a rufe ma suke tana Jin alamun itama BP dinta ya haye sama a take.

Hanyar gidansu fadila da suka nufa ya Saka Dad Jin wani irin Abu me nauyi Yana saukowa daga maqoshinsa zuwa kirjinsa sbd ya tabbatarda idan ba ciwonta yayi ajalinta ba to tabbas lameenu ya aika su BB rufe aikin kwata kwata kafin asanar da Jamaal sakamakon Wanda Shima akwai tanadin da yayiwa Hakan Amma a cikin sanyi da cike aiki take batareda barin kowace alama ba.

Tin daga nesa wutar Dake cin gidan sosai suke ganinta
Take jikin mum ya dauki rawa hawayen tashin hankali na ciko idanuwanta sbd Jamaal kada yace zai shiga gidan.

Dad da Shima dukkanin jikinsa ke cirewa sbd wannan tsoron tini yace ayi parking cikin daga murya.

Ko gama parking baayiba Dad ya Bude motan ya fito yayi gurin Jamaal da sauri Yana Kiran sunansa hankalinsa tashe sedai Jamaal din Baya jin komai fadila kawai dayake buqatan Gani a hannuwansa.

Haroon da siddeeq ne suka hango zuwansa da gudu Haroon yayo gurinsa ya tareda tareda rungumesa sosai daidai isowan Dad idanuwansa kaman zasu fado sbd tashin hankali da sauri ya rungume Jamaal din ta Baya Shima Yana Jin zufa na tsinko masa.

Jamaal zare jikinsa yakeson yi Amma sun masa wata irin kyakkyawar runguma Haroon na cewa

“Fadila is safe siddeeq ya fito da ita”

Wannan kalaman ne suka Saka Jamaal din jikinsa ya saki tsawon minti Daya kafin ya dago idanuwansa jajir Yana buqatan ganin fadilan.

Ambulance ta asibitinsu ce ta iso cikin gaggawa aka dauki Fadila wadda batasan Ina kanta yake ba tareda umma wadda itama take a sume sbd hayaqin Daya bugeta.

Motan kashe gobara ce itama ta iso daidai lokacin sukuma suka bar gurin zuwa asibiti cikin gaggawa.

Siddeeq barinsa Akai tareda mutane da masu kashe gobara harma da Police da suka iso gurin cikin tashin hankali sbd baba Dake cikin gidan baa fiddosa ba,

Mum asibiti suka marawa su Jamaal Baya itada da Dad Wanda yakejin Yana dawowa hayyacinsa daidai sbd barin yayansa gurin Dan motan Haroon ne bayan ambulance din sukuma suna bin tasa motar.

Ana Isa asibiti cikin gaggawa likitoci suka amshi fadila da umma aka shige emergency dasu
Haroon kuwa da Dad Jamaal din suka zauna tareda dashi Dan basa karfin gwiwa.

Mum da ita aka shiga emergency din Dan taimakon gaggawa fadilan take buqata sbd Bata tareda oxygen nata tini ya fizge yana can.

Zaman jiran tsammani me azabar gaske sukeyi dukkaninsu tin daga Jamaal din har Dad da Haroon,

Haroon sai Kai da kawo yakeyi Yana Jin kaman ya yayewa Dan uwansa abinda yake ji.

Sai asuba likitocin suka samu shawo kan fizgo numfashin fadila aka Saka mata wani oxygen din bayan mum ta tantancesa.

Umma kuwa Daman tini ta farfado Dan Daman hayaqi ne ya sumar da ita Amma dayake mijinta da yarta ne a ranta tini ta farko cikin sanyin jiki da fargaban baba da akace Yana can tareda siddeeq ita Kuma fadila tana asibitin tareda ita.

Dad da mum ne suka koma gida bayan sallan asuba suka bar Haroon tareda Dan uwansa.

Suma bayan sallan asuba dubo fadilan yai suka dawo office dinsa anan yayi shiru Yana tinanin yanda zasuyi su sanar da umma gawar baba na asibitin.

Siddeeq ya kalla cikeda kulawa da tausayawa Dan Shima maraya ne gaba da Baya su baba dinne gatansa danginsa yanzu baba ya rasu.

Har karfe tara na safe suna asibitin Kuma Basu sanar da umma komai ba sai guraren goma suka taho dakin datake Jamaal ne Kai tsaye ya sanar da ita rasuwan baban cikin dacin zuciya da tausayi me tsanani.

Numfashi ta sauke ahankali me zafin gaske batareda ta motsa ba sbd jikinta ya Bata Hakan Kuma zuciyarta tini ta amsa Hakan ta karbi jarumta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected