AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Wasu Kuma da yawa manya masu taka nera da dollar yanda sukeso sun fara nuna shaawan Sonta Amma Kuma sanin waye Omar Jden da yanda turai ta ratsashi bazai iya aurawa yarsa dattijo ba,
Wasu Kuma masu shigowan matasa ne masu dollar da nera lafiyayya Amma Kuma duba da yanayin rayiwanta da itama Sam Babu alaman namiji na gabanta Sam ya Saka suke fakewa da zama abokan business kawai.
Babbah da Dadah ne tareda Arfat da mum Nur suka tafi Umrah ita Kuma da Hafiz suka wuce Miami sbd Dad dinta dayake Jiransu acan akan sabbin shares Daya Siya da sunanta suna baqatanta Dan signing nasu shares din Dan haka ita da Hafiz suka tafin sbd komai Daya danganceta shine yake hannunsa.
***************
Black Lamborghini ce tayi parking a haraban asibitin ALEENA BOZEMAN,
Bude kofan motar Akai tareda fitowa gabaki Dayansa cikin nutsuwansa da kamewansa data rabasa da kusan Rabin abokan Aikinsa a yanzu sbd komai nasa ya sauya daga Dr JEEY din da suka sani Dan yanzu kamewansa da rashin sakewansa da mutane ya wuce tinaninsu,
Kwata kwata Baya maamalantar mutane sosai sbd bayason hayaniya ko yawan surutu,
Ya Dena aikin asibiti kwata kwata sai dace kawai ake samun damansa idan case ya zama babba yaxo ya duba musu sbd Bayama zama guri daya,
Yawon qasashe kawai yakeyi yanzu sai business dinsa Daya bunqasa fiyeda na iyayensa a yanzu Amma Sam ba shine akan business dinba ma siddeeq ne akan komai,
JAMAAL SEELAH ayanzu Wani JAMAAL dinne daban ba Wanda suka saniba,
Mum dinsa ta warke kaman Bata taba ciwo ba ganin tana kwance zata rasa ‘danta Daya Dan haka ta dage da dauriya da fighting da rokon Allah
Allah ya tayar da ita ta warke fes Abinta ta fara taro danta daga damuwan da zata iya kashe mata shi sbd tasan idan zai rasa ransa ahakan bazai taba fadan abinda yake ransaba,
Siddeeq ne ya sanar da ita komai Dan haka itama saita Hana kanta damuwa akan yawon tafiye tafiyansa kasashe bayason zaman gurin Daya Koda Hakan zai sake masa zuciya.
Ya samu sauyin rayuwa Dana kamanni sbd irin hasken Daya qara na asalin baturensa da wani lafiyayyan gashin fuska Daya Tara me tsananin laushi da kyau Daya qara masa sosai kaman bazaka iya dauke idanuwanka daga kansa ba,
Komai nasa ya sauya tin daga kan,
Halaye,yanayin gudanar da rayuwa,
Sake budewa sosai a jikinsa Sbd geamin da nutsatsiyar Hutu da daulan rayuwan Asalin luxury life dayake cikinta na komai Daya sake zaunuwa a rayuwansa.
Dukkanin wannan sauyin Abu Daya ne Bai sauya ba daga zuciya da rayuwarsa Wanda yake zaune boye cikin ransa shine Neman Ameenatou da Neman Ashly da Bai denaba Kuma bayajin Hakan zai tsayu har sai ranarda yayi ido biyu da dayansu.
A Baya Yana communicating da Ahmed akan lafiyan Dad Omar da tana hannunsa Amma daga lokacinda ta bata daga asibitin Kuma lokacin ne ya samu tabbacin samun lafiyan Dad Omar din Bai taba barin sun sake magana ba sbd radadin dayake Ji a zuciyarsa na bacewanta a hannunsa batareda ya sadata da mahaifinta ba.
Qarin abinda ya Saka Dad Omar a nasa bangaren Baya samunsa shine yanayin rayuwan Hutu da yawon dayakeyi ya Saka idan ba siddeeq da mum dinsa ba to duk Wanda ya nemesa Baya samunsa Saiya bi ta hanyarsu,
Ko Dad dinsa Saiya nema siddeeq ko mum din yake samun Daman magana dashi sai idan shine yaso ya nemesa da kansa.
Ash Ralph Lauren Riga da wando da loewe jacket,
Wayarsa ce kadai a hannunsa ya nufo cikin asibitin duk inda ya wuce sai qamshinsa ya sauya iskan gurin da qamshin Paco Rabanne dinsa Da shine abinda kadai Bai sauyaba daga sauyin dayawa komai na rayuwarsa.
Doctors din Dake jiran isowansa ne bayan request da suka ringa turawa na buqatan zuwansa tin last month sai yanzu ya samu Daman sauka Poland din Dan haka fitowa sukai gabaki dayansu Dan tarbansa da masa barka da zuwa suka dunguma zuwa ciki Asalin office din mahaifiyarsa dayake ba Wani zama zaiyiba a qasar yanada tafiya Miami a satin dan haka Kai tsaye baya buqatan Bata time zai duba musu cases din a kwanaki kadan yabar qasar.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
102
*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products
Location: LAGOS
We deliver nationwide
09013833502
https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL
*******
Ranar da suka isa Miami Kai tsaye Lodge dinsu ta isa shi Kuma hafiz gurin aikin daya kawosu ya nufa Dan yau akwai abinda zai fara.
Wanka tayi tareda saka Riga da wando marasa nauyi tayi sallah takuna ta kwanta Dan hutawa ko waya batai da kowaba saita gama hutawa sbd kanta dayake Dan ciwo.
Sai tsakar dare Dad da hafiz suka dawo tareda Uncle Ahmed lokacin tini ankawo mata komai na abinci an jere taci iya abinda zataci tayi brush da wanka ta shirya cikin kayan bacci ta Haye gadonta tagama wayoyinta tayi bacci abinta.
Da safe dukkaninsu Babu Wanda ya fito baccin safe da hutawa sukai sai after 10 kusan 11 ma tukuna.
Itace tafara fitowa sanyeda wide leg jeans da sweatshirt din Burberry da qaraman hula tana waya dasu arfat dayake musu rigima sosoi akan rashin Dad da uncle hafiz dinsa da ita mommahn nasa Amma dai ta samu ta lallabasa ya manta da zancen rigiman sunyi fira sosai dasu dadah kafin ta kashe.
Kamshin Dad dinta ne na musamman da Bata taba tantance Wani namijin dayake da qamshin nutsuwa irin na Dad dinta ba Dan haka a duk lokacinda ta shaqi qamshin mahaifinta me nutsuwa kamansa sai ta godewa Allah akan yanda yayiwa mahaifinta albarka SBD a duniyarta mutanen datafi so fiyeda rayuwanta dukansu Maza ne su uku,
Babbanta,Dad dinta da ‘danta Arfat.
Omar jaden ma Yana waya a natse ya qarasa fitowa palon ya zauna cikin farar jallabiya data nutsu a jikinsa yana ganin yarsa yayi sallama da wayar a Natse kafin ya ajiye wayar gefensa Yana sake kyakkywan fuskansa ta cika da murmushi da farin cikin ganinta Dan ita kadaice a duniyarsa da idanuwansa suke kalla fuskansa ta yalwatu da sanyin farin ciki da murmushi a take.
Itama farin cikin NE ya mamayeta ta qaraso har gefensa tana cewa
“Dad Ameenatou da Arfat munyi kewanka sosai”