AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Ashley kuwa ana Isa dasu asibiti ita aka fara karba da gaggawa sbd cikinta da itama batasan dashiba yake kokarin zubewa.

Wata nurse data fito daga emergency ce taga shigewan da zaayi da Ashley ta zubawa fuskanta ido tana kallanta Dan ko zata mutu ta dawo bazata manta kamannin Yar uwarta ba duk da sunyi shekaru baa tare ba tinda sun Rabu ne tin kafin iyayensu su tasu Dan haka take ta juya da sauri tana Ambatar sunanta.

Acikin abinda baifi awa nawaba Allah ya taimakesu cikin Bai zubeba aka samu ceto ranta itama amma dai kam sai yanda allah yayi dan tayi nisa.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
90

*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

**************
Har yamma shiru Ameenatou bataga Ashley ba hakama taqi yadda kowa ya matsota bare taci abinci daga Wani
Duk da ciwon Dake cinta na zazzabi da rashin kuzari ko kadan Amma wuni yunwa tayi Dan taqi cin komai daga kowa.

Duk yanda nurses sukai yaqi yadda da kowa hakama taqi ko magani Tasha,

Dan haka ta sake laushi sosai zuwa yamma
Koda dare yayi kwance take Bata iya komai bayan ambatar sunan Ashley
Idan taji shiru ta ambaci JAMAAL idanuwanta na gangarowa da Hawaye daga karshe dai sai dare dole aka takurata ta yadda taci abincin sbd galabaitan datai da tausayinta tareda tashin hankalin labarin accident din sister Ashley Daya samesu zuwa Daren Dan sunsan shikenan Ameenatou din ta shiga samon hauka kenan tinda kafin ta fara yadda da wani ba Ashley ba to rigima zaayi sosai da tashin hankali tareda tashe tashen ciwonta.

Su Dr Zakeer ma sabon tashin hankali suka shiga na samun labarin accident din sister Ashley dan kuwa ta tabbata bada Ameenatou dole garesu Dan idan babu Ashley babu sauran iya cigaba da boye zancen cikin dan kuwa dik nurse da zaa sake bawa Ameenatou ba lallai ta rufa ba hakama da wuri tana ganewa ma zanven zai fita hakama idan babu Ashley ameenatou bazata taba yadda da kowa ya fita asibitin da itaba har zuwa wata asibitin a cire cikin.

Dr Charles dayaga aikin na Neman cabewa da wannan sabon tashin hankalin Daya bullo na rashin Ashley da zai Saka haukan Ameenatou tashi
Kuma tashin haukanta daidai yake da bayyanar cikinta tinda zai iya zubewa a gaban duk Wanda Allah yace ya Gani ko gaban mutane da yawa,hakama kawai duka sunfi Aminta da barinta asibitin gabaki Daya kwata kwata Dan haka Babu Sanya ya tsananta binciken da zasuyi dan tabbatarwa da Kuma shedan su Babbah iyayenta da duka sai an Saka a file nata Dan gaba ko kuma idan Jeey ya dawo Dan fuskewa zasuyi tsaf su Qi barin dalili ko daya dazai kamasu da laifinsa.

Su Babbah kuwa daqyar suka ga kwana ukun Nan ta cike suka nufo asibitin tinda safe Dan a ranar Babbah yakeson barin Lagos idan aka Basu ita Dan haka da Shirin tafiya ma suka iso asibitin daganan mota zasu su dauka shata su tafiyarsu inda ko sunansu Babu me sake Ji.

Md ya Riga su babban zuwa asibitin ma sbd ya fisu matsuwa da su tafi da itan yanzu Dan tini ta haukace musu da rashin Ashely Amma sbd cikin su Kuma su Dr Zakeer sunqi barin kowanne likita ya dubata hakama sun kasa sun tsare sun Hana ayi mata alluran kwantawan haukan sbd anayi cikin zai fita,
Yana fita komai zai bayyana tinda dole Nurses ne mata zasuji da matsalar idan Kuma sukaji da matsalar zancen cikin ya fita kenan Dan Koda ya zube ne zancen ya fita duka dai masifar da balain Daya ne dan haka suke jiran iyayenta yau din su bada ita Dan gwara su lallaba su bawa wannan baban nata ita akan JEEY ya dawo take zai gane ciki a jikinta basuda mafita kenan Kokuma asalin mahaifinta ya waiwayota anan yazo ya tadda ciki.

Address dinsu na Nasarawa suka aika takanas aka je akayo bincike aka tabbatar musu da tabbas shine babanta hakama makarantar ta sunje,
Sunje asibitin can ma duka an duba musu sun gama tabbatarwa tareda hada shedan Hakan suka Saka komai a file nata tareda rubutawa Dr ibrahim ne ya Saka hannu a ciki suka kammala komai bayan jiran Babbah Babu abinda sukeyi Dan Doctors din su duka a ranar asibitin suka kwana sbd tabbatarda Babu abinda zai Bata musu aiki kafin safen Dan Saida Dr Zakeer ya tashi tsaye akan nurses da suketa kokarin yi mata allura shiyasa shi a yawon dakin Ameenatou ya kare cikin kwana biyun kafin ranar Bada ita tazo.

Babbah ma kaman yasan Jiransu akeyi Dan haka ya zabi zuwan safen,

Baa Basu matsala ba a gate din aka barsu suka shiga tafiya tafiya har office din md suna Isa Dr Charles na shigowa hakama dr ibrahim
Shi kuwa Dr Zakeer Yana ward dinsu Ameenatou din ya Saka an wata nurse ta sauyawa Ameenatou din kaya zuwa doguwar Riga black da hijab din sister Ashley fari qarami me kyau dayake cikin kayanta sbd basuda time na tsayawa ware wasu kayan Ashely Dake hade da nata tinda yasan su can bawai buqatan kayan sukeba andai hada mata abinda ya sauwaka sbd kowa yasan iyayenta sunzo zasu tafi da ita akan sun gaji bazasu iya cigaba da biyan asibiti ba basuda hali.

Kowa yayi mamakin Hakan sbd tinanin Ameenatou yar manyan mutane ce duba da yanda Ashley ke dawainiya da ita da yanda ko abinda take amfani dashi daban ne Dana kowa asibitin,
Ko slippers na banza Bata sakawa bare sauran abubuwan amfaninta Amma ace Hakan?to Amma tinda ba huruminsu bane likitoci sun sallameta basuda abin fada bayan kallo da fatan samun lafiya duk inda aka tafi.

Babu wani Bata lokaci sharuddan ciwonta da yanayin yanda zatasha magani da Kuma yanda Bata yadda da kowa duk sukai musu bayani Daya bayan Daya tareda cewa suyi kokari su ringa zuwa ana dubata zuwa gaba sosai haka.

Kaman yanda suke a matse hakama Babbah yake amsawa da ya gane cikin matsuwar Shima Dan fatarsa idanuwansa su sauka akan yar budurwansa ta shigo hannunsa.

Ko rufe Baki baiyiba ga amsar karshe sister fareeda ta shigo office din da Ameenatou wadda daqyar ta yadda tazo sbd ance mata gurin Ashley zaa Kaita.

Idanuwan md Dana Dr Ibrahim da Charles akan Ameenatou da yanda zatai reacting idan Taga su babban duka suke zuciyarsu a Dan rikice da fargaba Dan Hakan ne ma Dr Zakeer yayi saurin sallaman sister fareeda din yace ta tafi sbd Yana bayansu tana ficewa ya rufe office din Yana dawowa gaban Ameenatou din daga bayanta dayake Yana kallanta lokacin ne ta dago kanta fuskanta a rame idanuwa duk sun fada ta narke idanuwanta Dan yiwa Ashley kukan barinta datai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected