AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Cikin nutsuwa suke tattaunawa har suka Isa cikin main palon mansion din inda yake tsare da luxuries na Jin dadin rayuwa da asalin Hutu.
Hanyar dining room suka nufa dukkaninsu daidai fitowan mum Atey da itama Hutu da Jin dadin rayuwa yake bayyane a tattareda ita.
Tana ganin Jamaal ta washe Baki cikin kulawa tana cewa
“Dr jeey tin dazu nake cewa kana hutawa baka fitoba bare muyi Maka barka da dawowa”
Dan kallanta tayi a gazarce Yana Dan sake fuska kadan batareda murmushinsa ya bayyana ba ya amsa da
“Eh na gaji ne Koda na iso Ina buqatan ishashiyan Hutu,.thank you”
Fitowan Ayesha ‘yarta ne ya sakashi Dan daga girarsa Daya sama Yana Dan dauke kallansa daga gefen kwata kwata suna cigaba da magana da Dad akan abinda suke tattaunawa.
Gurin Haroon ta nufa tana sake fuskanta gaba Daya da farin cikin ganin Jamaal din tace
“Dr sannu da dawowa.”
Batareda ya waiwayoba yanda ya kamata ya Dan juyo kadan yace
“Yawwa thank you”
Zama tayi a kujeran kusa da Haroon tana gaida Dad Shima kafin ta dawo da kallanta kan Haroon tana magana kasa kasa kada kowa yaji me take fada masa Yana dariya fuskansa a sake sosai sbd akwai shaquwa da kulawa sosai a tsakaninsu.
Mum kuwa gefen Dad ta zauna sai ya zamana gefen Jamaal din shi kadai ne Daman Hakan shine raayinsa Dan haka take masu aiki suka qarasa kawo abubuwan da Babu a dining din su ruwa da drinks da cutlerys Dan Basu gama hada table ba masu gidan suka hau.
Mum Atee sosai takeson samun shiga kamar me gurin Jamaal sbd tini ta gama da kame Haroon ta koma itace uwarsa komai da ita yakeyi a matsayin uwa shi kuwa Dr ko a mafarki ba’a Haifa macen da zata maye gurbi ko samun matsayin mahaifiyarsa ba bayan mum dinsa itace kadai tak dinta Dan haka duk tsananin dagiya da son nuna masa tsananin kauna da kulawa da mum Atee keyi Bata taba samun shiga yanda takeso ba Amma dayake ta iya naci da kisisina Bata Dena nuna masa kulawa da tattalin ba saima sake dagewa datakeyi Dan tagama fahimtar Dr din shine SEELAHs ma gaba dayanta yanzu da zuwa Nan gaba hakama Dr ne kadai zata kama ta kama dahir a zaman seelahs harma ta taka matsayin shugaba a cikin matan zuriar duk da akwai wainda suka rigata dadewa a family harda manyan Yaya Amma dai nata burin daban ne akan nasu Dan ita ba zaman auren kadai tazo yiba hadda nemawa Kai suka da matsayi.
Cikin nutsuwa da wayewa sukecin abincin da sakewa dukkanin kulawan mum Atee akan Jamaal take tana tura masa abubuwan datasan Yana ci tana basa tabbacin sbd shi Akai girkin.
Sun jima sosai gurin cin abincin kafin suka gama suka baro dining din Kai tsaye Palo suka dawo suka zauna harsu mum din suka zauna suna magana tsakaninsu ita Dan Haroon da Ayesha shikuma Yana magana da Dad.
Anayin ishai suka fito Sallah suna gamawa Kai tsaye bangarensa ya nufa ya sauyo kansa daga guntaye zuwa dogon Riga da wando na Dior black ya fito Yana qamshi ahankali wayarsa kawai ce a hannunsa sai laptop.
Haroon already Yana harabar gidan Yana waya Dan haka Yana ganin fitowan Jamaal din ya Bude motar ya shiga Shima Yana isowa ya Bude ya shige suka fice harabar gidan securities da suka San Dr Jamaal din ba dawowa zeyiba a Daren suna masa a dawo da safe lafiya.
A hanyar ta zuwa tinda suka fito Jamaal ya kira mum dinsa ya Saka handsfree ya ajiye a tsakiyansu suna magana da ita su duka biyun cikin tsananin kaunar datake musu da wadda sukewa junansu Suma.
Suna Isa Haroon a harabar asibitin ya ajiyesa ya juya ya fice sbd ana jiransa wani guri.
Shi Kuma Kai tsaye ya wuce office dinsa duk inda ya wuce ana masa barka da zuwa cikin girmamawa da kulawa harya Isa office ya Bude ya shige.
Laptop din ya fara ajiyewa da wayarsa kafin ya rage AC kadan sbd tin kafin ya iso ake sake tsaftace office dinsa a kunna AC dasu humidifier.
Ajiye remote din yayi bayan ya rage AC Yana nufar files din dayake kan desk dinsa Bai taba ba ya nufi toilet ya wanko hannuwansa ya fito bayan ya goge hannun da towel fari qarami.
Sensitizers ya fara shafawa hannuwansa kafin ya nufi files din ya fara dubawa.
FADILA ALIYU MUHD shine sunan dayake kan file din.
Budewa yayi cikin nutsuwa Yana dubawa tareda karanta dukkanin bayanan dake ciki.
Dr zayyan ne ya shigo office din bayan yayi knocking Yana sanyeda kayan theatr da fitowansa kenan ganin Jamaal ya sakashi sakin ajiyan zuciya da numfashi me sanyi sbd suna tsananin buqatansa akan patient din da aka juye masa file nata.
#MAMUH#
#DR JEEY SEELAH
#BARR HAROON SEELAH
#HASSAN AND HUSSAIN
#AMEENTOU
#FADILA
#LOVE
#ROMANCE
#CRAZYINLOVE
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_
Arewabooks@Mamuhgee_*
20
Dagowa yayi bayan ya gama sauraron bayanan Dr zayyan akan patient din Daya gama karanta severe long term asthma take fama dashi Wanda gabaki Daya rayuwarta da oxygen take rayuwa.
Idanuwansa ya dago yakai kan inda ake rubuta shekarun patient yaga shekarunta duka duka ashirin da Daya.
Dagowa yayi ya kalle Dr zayyan kafin yace komai nurse ta kwankwasa office din cikin sauri ya shigo ta sanar dasu ana buqatansu emergency ne yanzu yanzu fadilan taqi yadda a Saka mata oxygen dinta tayi nisa komai zai iya faruwa a daidai lokacin.
Dr jamaal dinne ya wuce gaba riqesa file din suka biyo bayansa cikin sauri.
Tin kafin ya iso nurse Farry na hangosa ta dauko masa hands gloves ta tarbesa da ita ya miqa mata file din hannunsa yana sakawa Yana karo sauri Dan isowa ga patient din da kusan ranta ma zaa iya cewa ya kusa fita Dan kuwa ta fizge oxygen nata gaba Daya gashi matsalanta pneumonia ne yafara mata mummunan kamu kafin asthma ya rikido.
Yana qarasawa da sauri yakai hannuwansa duka biyu ya Dora akan nata tareda dafeta Yana cewa ayi sauri a Saka mata oxygen din da gaggawa.
Dayake tayi nisa sosai Babu Bata lokaci aka mayar mata da oxygen din har lokacin Bai saketaba sbd Nisan datai ba lallai oxygen din ta shigeta da sauri ba Dan haka ya Bada umarnin ayi gaggawan kawo alluran da zai mata.
Gaba Daya sauri sukeyi Dan cetan rayuwarta musamman iyayenta dake kofar dakin suna kuka sosai Dan tini suka cire Rai daga gareta ganin yanda rayuwarta yake sama Yana qasa numfashinta na barin jikinta.
Addua suka hau cikin tashin hankali da fatan samun sauki da lafiyan Fadilan.
Sunyi tsananin laushi da zama abin tausayi akan ciwonta da lalurarta tsawon shekaru,
Duk abinda suka mallaka ya qare tas basuda komai bayan rayuwarsu sbd ciwon fadila,
Da oxygen take rayuwa koyaushe Yana tareda ita,
Mahaifiyarta da mahaifinta ita kadai garesu hakama tayi karatu sun inganta rayuwarta sedai ciwonta a yanzu da itama take ganin ta gaji sbd ta zamarwa iyayenta lalura,
Komai dasuka mallaka tana kallo ya qare duk sbd ciwonta dayake cin kudin da yanzu sun Dade da fin karfinsu dan haka take ganin kaman idan ta mutu zasu rage Shan azabar da sukesha sbd ita,