AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
“Haroon nayi Maka alkawarin bazamu bar garin Nan ba ayau sai munje munyi gaisuwar iyaye da iyayenta sbd Neman Maka aurenta idan har zaka nutsuwa ka fuskanci nauyin dayake kanka sbd Kaine kaidai zaka iya gyara wannan Barnar data riskemu sbd kafi kowa sanin halinda muke Neman fadawa idan bamu farfado ba.
Tinda suke magana idanuwansa a rufe suka Hawaye masu zafi na gangarowa a acikinsu Saida Dad Lameenu yayi masa alkawarin nema masa auren ya Bude idanuwan ahankali ya kallesa Yana sauke Kai kasa.
Dad dinsa ma Jin yayi yayi Naam da Hakan Dan shine maslaharsu ayanzu kada su maimaita kuskuren Baya gwara su nema masa auren su juyasa akan abinda sukeso tinda zai iya komai akanta din.
Duk yanda wani zai samu Daman sanin matsalar ciwon Haroon Saida Dad ya tabbatarda Bata fita ba hatta siddeeq Bai bari likitocin sun bari yasan duk wani abinda aka bincika aka Gano ba har suka sake kwana biyu a garin Akai sallamarsa a ranar suka kwasa zuwa Nasarawa Dan Kai gaisuwan Neman auren.
#MAMUH#*_Arewabooks@Mamuhgee_*
39
****Su babbah da suka samu labarin zuwan da Dad din zasuyi gaisuwa tini aka gyara koina hatta kofar gidansa Saida aka share har kofar gidan makota aka shirya tsaf Dan tarbonsu da Aminansa guda biyu da zasu tayasa karban gaisuwan.
Dayake ranar su Dad din zasu koma da wuri suka iso guraren karfe daya na Rana Dan haka su Babbah suka tarbesu da girmamawa da mutuntawa sosai har cikin fara isowan gidan babban suka zauna a babbar dadduman da aka shimfida musu me kyau.
Dad Lameenu Dayake amsa gaisuwansu cikin girmamawa da kulawa sosai Shima tareda farin ciki me tsananin da tin anan aka fara farin cikin Samun Sirikai irinsu da duk kudi da matsayinsu sunsan mutuncin mutane da iya mu’amalantarsu.
Babbah Dad Lameenu yayi kallan tsaf Mintina Yana tantance kamannin nasa da son tabbatarda idan shine Wanda yake tinanin shi dinne.
Ganin irin kallan da Alh Lameenu kewa Babbah ya sakashi sai farin ciki yake sake shiga Yana sake musu barka da zuwa kafin ya tambaya jikin Haroon cikin kulawa sosai Yana dorawa da cewa sai anjima su Abdul su shiga dubasa Inshallah.
Abinda ya tarasu suka shiga gabatarwa Babu wani Bata lokaci suka gabatar da kansu da Neman auren Ameenatou da suka zo nemawa dansu Haroon Wanda su Babbah sun sanshi kuma sunsan aikinsa da halayensa daidai gwargwado.
Naam su Babbah sukai kafin suka suka sake gabatar da kansu da shi babban amatsayin mahaifin Ameenatou wadda shine ya haifa abarsa da cikinsa Kuma yayi na’am da Hakan ya Kuma bawa Haroon aurenta.
Farin ciki da hamdala suka ringa miqawa ana sake taya juna murna Dad Lameenu ya cire kudin Neman auren Naira dubu dari biyar ya bayar kafin suka sake miqa godiyarsu har lokacin zuciyar lameenu wani tsalle takeyi cikin rudewa da rikicewa Dan kuwa ya sake tabbatarda Babbah ne suka tana Gani asibiti gurin Omar a lokacinda aka taba Kai masa attack idan Bai mantaba Kuma ya sake dubawa ya tabbata Babbah ne ya Gani Wlh.
Abdul da shine babban yayan Ameenatou Kuma dashi Akai zaman Neman auren Alh Lameenu ya kalla cikin kulawa Yana tambayarsa Aikinsa da karatunsa.
Cikin nutsuwa da ladabi Abdul din ya amsa masa matsayin karatunsa da aikin dayake yi.
Take Alh Lameenun ya nuna raayinsa na Taimkawa yace Abdul din ya hada takardunsa zai Aiko a karba a aika masa Lagos.
Godiya Abdul din yayi su Babbah dasu Alh sabi’u makocin Babbah godiya sukai suna sake nuna Jin dadinsu kafin su Dad suka saki jiki sosai sukai fira da maganganu dasu babban anan ma sukai sallah azahar kafin suka Shirin tafiya su Babbah suka rakosu har waje inda motocinsu da securities dinsu suke suka shiga take aka bar gurin dasu.
Suna barin gurin Dad Lameenu zufan dayake hadawa tin acan yana shanye abinsa a jikinsa ya zari tissue ya goge kafin ya Ciro wayarsa.
Hotunan da BB ya turo musu nasu babban ya Nemo hannuwansa na Dan rawa ya Nemo na Babbah ya zuba masa idanuwansa.
Mam da zuciyarsa kwata kwata Bata cikin dadi Baida energy din tambayar abinda yake faruwa sbd bayajin zai taba barin ya hada zuria dasu Babbah
Ya nema auren ne sbd yana buqatan Haroon din sbd ya Jamaal ya dawo garesa Amma Badan Hakan ba bayajin zai tana yadda ya Kai kansa Neman auren.
Lameenu Daya sake goge zufansa miqewa Mam wayar yayi Yana cewa
“Wannan shine fitilar da zata kaimu ga sanin duk inda dangin matar Omar suke sbd samun Magajinsa”
Kallan wayar Mam yayi kansa na tsananin sarawa da nauyi Amma Jin Abinda Lameenu ya fada ya sakashi cire hannunsa daga goshinsa Daya dafe idanuwansa a lumshe.
Kallan Lameenu din yayi bayan ya Kalli Babbah a wayar Yana jiran bayaninsa.
Cikin nutsuwa lameenu ya tinatar dashi ganin da sukaiwa Babbah a asibiti tareda Omar shekarun Baya.
A saninsu wancan lokacin daga kauyensu Omar yace musu babban yake Amma basusan Menene alaqarsa dashi ba Dan haka dole babba yasan waye yayan matar Omar Kuma bazasu rasa sanin komai ta hanyar Saba Daman a bagiren Neman ko mutum Daya daga kauyen suke amma tsawon shekaru ankasa samu.
Wani sanyayyan sanyi ne ya ciked zuciyar Mam take yaji nauyin zuciyarsa na rayuwa sedai bayajin zasu samu yanda suke so idan suna nesa dasu Babbah din.
Lameenu Dayasan dalilinsa Daman kenan na buqatan daukan Abdul aiki take ya Saka kira yace a tanadarwa Abdul din aiki me kyau da gidan zama a Lagos inda zai dauko iyayensa ya dawo dasu.
*********Su Babbah kuwa A nasa bangaren sunan jeden da Omar yake amfani dashi shine ya hanasa sanin shima Omar din seelahs ne Dan haka farin cikinsu kawai sukeyi.
Da daddare da kansa shi da su Abdul sukaje suka dubo Haroon din Wanda ya danne ya nuna musu karfin hali duk da Yana cikin tsananin tashin hankali da Tsaka me wuya sbd sanin Neman auren bashine aurenba indai Bai cika alkawarin Daya daukanwa Dad dinsaba,
Bayan tafiyarsu da daddare tsananta damuwansa tayi sbd gwara ace baa nema aure ba zai iya runawa ya hakura da Ameenatou Koda zai rasa ransa Dan kawai yabarsu su ta tsira Amma a yanzu da aka nema masa aurenta yasan ba janyewa sedai Kuma irin kaddarar fadila da Dan uwansa yake guje musu.
A cikin Daren siddeeq ya koma Abuja Bai kwana ba Saida ya samu report na komai da akaiwa Haroon ya turawa JEEY Wanda sakonsu ya isar masa a daren daidai lokacinda ya fito wanka daure da towel dinsa gabaki Daya jikinsa wata irin sheqi takeyi kaman Bai taba Shiga rana ba.
Hannunsa yakai ahankali ya dauki wayar Yana ganin report din ya Bude sakon Kai tsaye Yana karantawa.
Tsayar da fararen idanuwansa masu gigita Wanda suka kalla yayi akan report din idanuwan na sauya ahankali zuwa ja zuciyarsa na daukan wani nauyi take.
Shigowan kira ne ya sakashi rintse idanuwan ya budesu ahankali akan sunan Haroon daya bayyana kan screen din wayar.
Iska me dumi ya sake fitarwa daga bakinsa kafin ya daga Kiran batareda yace komaiba ya Dora wayar a kunnensa Wanda yayi daidai da Haroon din na kasa riqe kansa daga zubar da hawayen radadi da kuncin dayake cin zuciyarsa da rubabbiyar rayuwarsa gaba Daya.
Shiru Jamaal din yayi har lokacin Bai furta komaiba sbd wannan shine Karan farko da Dan uwansa ya bayyanar da tsananin kunci da baqin cikin rayuwar dayake ciki garesa,
Bai taba fada musu rayuwar wulaqanta da qasqantar dayakeyi a hannun su Dad ba,
Bai taba barin sun sani ba,
Bai taba nuna musu ba
Ya shanye komai ya hadiyewa kansa baqin ciki da radadin shi kadai Amma ayau dayake cikin tsananin hali ya kasa danne zuciyarsa daga Neman taimakon Dan uwansa Dan idan ya rasa Ameenatou zai iya rasa rayuwarsa gaba Daya batareda yasan rayuwar tasa tana cikin mummunan hadarin tsaka me wuyar da kowane lokaci komai zai iya faruwa ba.