AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Bude sakon yayi tareda fara karantasu Daya bayan Daya Yana kasa fahimtarsu da kyau.
Sake dawowa Baya yai yafara karantawa dakyau Yana fahimtar duka results ne da awo awon Haroon da abubuwan da aka samu a jininsa kafin rasuwarsa,
Daga karshe Kuma results din Dr Dee ne guda Daya da results dinsa yazo daidai Dana Haroon Shima akan abinda ya kashesa da abinda yakusa kashe Haroon din koma yace ‘dansa ya Dade da mutuwa yawon kawai yakeyi hadarin mota ya qarasa mishi shi,……..wait wait wait wait.. accident din auren Haroon mota ce ta takasu,Kuma drivern motan a gurin mutane suka rufesa da duka suka kashesa,Motar Omar Haroon yabi………
Ajiye wayarsa yayi hannuwansa na daukan rawa sosai zufa na tsinke masa,
Ruwan Dake gabansa ya dauka yakai bakinsa yasha.
Daya bayan Daya yake sake jera abubuwan kansa cikin tinaninsa,
JAMAAL kenan yana tinanin illata Haroon Akai duk tsawon wannan lokacin?
Yana sane kenan yake bincikensa a boye Dan Ganowa,
Kwayoyin da suka kashe Dr Dee sune suka kashe Haroon?
Menene hadin kwayoyinsu?
Kwayar data kashe Dr Dee yanada tabbacin kwayarsu ce Amma Bai taba kawo tinanin ko a mafarki ba ‘dansa na cikinsa kwayar ce tayi masa illa,
Meya hada haroon da wannan kwayoyin?
Kota Yaya kwayoyin Nan suka Isa ga dansa BB Ya sani Kuma zai bayyanarda saninsa Dan kuwa Koda Haroon ne da kansa ya Siya yasha Saiya tabbatarda Wanda ya siyar masa din yabisa inda yake,
Idan Kuma Wani ne ma ya illata masa shi to bayanin dai duka dayane.
Wayarsa ya daga cikin nutsuwa ya Saka Kiran Lameenu Yana daidaita kansa tareda bayyanarda nutsuwansa a sauti.
Lokacinda Kiran ya shiga wayar Lameenu Yana zaune tareda matarsa mum Sarah suna magana tana zuba masa fresh Madara me sanyi a cikin bowl din fruit Dake gabansa.
Kallan wayar yayi Yaga sunan Mam,
Da mamaki ya sake kallan wayar sbd saninsa Mam Baya kasar,
Sake dubawa yayi da kyau sai yaga Whatsapp call ne Dan haka ya dauki wayar Yana ambatar sunansa da cewa
“Ya sauka ne??
Dan murmushi Mam yayi Yana jeho masa gaisuwa suka gaisa suna shiga zancen abubuwa daban daban tsawon lokaci kafin Mam yace
“Ina Poland tareda Jamaal yayi rashin lfy nazo dubasa Amma bamu Hadu ba sbd zafin kansa yaqi sauka har yanzu,
Amma Kuma na samu Wani zance me daure Kai akan rasuwar Haroon a bakin Siddeeq batareda sun San naji Hakan ba,
Jamaal Yana zargin mune muka kashe Haroon Dan haka bincike ake masa sosai,
Binciken ba abin damuwarmu bane sbd nasan Babu Wanda ya Isa ya kashe ‘dan Mamman Seelah idan ba Allah ba,
Amma abin mamaki anan shine Dr zayyan naji ya kira siddeeq Yana sanar dashi sun samu hada results din Haroon Dana Wani Dr da akace ya rasu kwanaki………….
Ruwan Madarar da aka zuba cikin fruit salad dayake Sha ne ta biyo ta hancinsa da karfi cikin sarkewan tashin Yana dire bowl din har Yana zubewa a shaqe yana dedeta muryansa yace
“Me yake kokarin yi da results din Wani daban Kuma??
Meye amfani ko dalilin Hakan?
Haroon ya Riga ya rasu yabar Dan uwansa ya kwanta lafiya,
Kuma yasan dai Babu yanda zaayi mu illata Haroon da kanmu sbd shi ‘dan mu ne”
Murmushi me sauti tareda ajiyan zuciya Mam ya sauke Yana sakewa a natse yace
“Nabari su hadasa da results din Dan Nima inason Jin Menene sakamakon”
Zufa lam ya share Yana miqawa Mum Sarah hannu ta Sako masa tissue ya sake goge hancinsa da ruwan Madara ke fitowa ciki har lokacin.
“Hakan ma shine daidai muna buqatan samun results din kafin JAMAAL din Amma sbd kada Akai masa abinda zai ruguza mu batareda mun saniba”
Murmushi Mam ya sake sakewa Yana cewa
“Dayake shi din jinina ne Magajina zai iya samun Hakan Amma bayan shi kansa ganin akwai Wanda zai taba Mam Seelah tabawa irin wannan ya miqe kuwa?”
Dariyan karfin hali lam ya sake Yana janyo Wani zancen.
Sallama sukai Mam Yana ajiye wayarsa gefensa idanuwansa na sauyawa sosai sbd ya karanci abinda yakeson karantar.
Lameenu seelah yayi wautan datafi shiga ruwa da hular dutse.
Wayarsa y dauka Kai tsaye ya kira bullet yace a Saka ido a gidan Dr zayyan a Gani idan zaa Kai masa hari a gidansa.
Hakama a tanadar masa kwayoyinsu zaiyi gwajin overdose da normal dose ga mutum biyu Daya overdose Daya normal dose Kuma a cikin ahalin seelahs zaiyi kwajin idan har ayau ankai farmaki gidan Dr zayyan zancen ya sake Bude masa da kyau.
Yana kashe wayarsa miqewa yayi ya shige ciki Yana Jin Asalin jininsa na Seelahs na Wani irin tafasa da kunar da Bai taba samun kansa a cikiba,
‘dan cikinsa ake maganar anyiwa mummunan illan da tai kusan sanadinsa koma tayi din Dan ko baiyi accident ba mutuwar zaiyi sbd kwayoyin bazasu taba barinsa ya rayun ba,
Tabbas zaiyi gwajin abinda yagani a ranar da Haroon dinsa ya ringa aman jini da kusan mutuwa,
Zaiyi gwaji ga mutane biyu da Hakan zai girgiza kowa Dan tantanve yawan adadin Wanda suka durawa ‘dansa kafin ya waiwayi Wanda yayi aikin gaba daya.
Lameenu kuwa tinda ya ajiye wayar yake Neman wayar BB Amma kwata kwata Baya samu Dan haka dole bullet ya kira Kai tsaye sbd idan gari ya waye komai zai iya faruwa idan Dr zayyan ya aikawa JAMAAL sakamakon komai zai iya faruwa Wanda yasan sanin JAMAAL kadai zai iya zautashi bare Mam ya sani.
Mum Sarah Kuma itama tashin hankalin take Neman shiga na Neman Aliyah da aketa yi tin dazu Babu zancenta Babu labari,
Siyam kuwa ma Bata qasar sai satin zata dawo Dan haka hankalinta ya tashi tanason sanar masa Amma ganin Halinda yake ciki na Kaida kawo Yana hada zufa ya Sakata kasa sanar masa taci gaba da Kiran Aliyahn.
*********Sai dare sosai suka Isa lokoja lokacin Ameenatou tayi Nisa sosai a bacci,
Taxi suka dauka har kofar sabon Dan qaramin gidan dasuke haya Hafiz ne ya Bude gidan bayan ya sallami me motar suka shiga Ameenatou na qanqame hannun Babbah sbd duhun datake Gani tafara Kiran sunan jamaal Dana sister Ashley.
Da sauri Hafiz ya qarasa ya kunna wutar tsakar gidan Yana cewa gashinan ya kunna mata haske.
Rintse ido tayi tana Jin kaman zata tsorota Amma yanda suka zagayeta kowa na kokarin rarrashinta ya Sakata fasa rikicewa ta Bude Baki a hankali cikin sanyi da kasala tace
“Ameenatou zatayi fitsari,
Kuma Ameenatou zatasha tea”
Dadah ce ta zare mata qaramar hijab din kanta tareda kama hannunta zuwa toilet din tsakar gidan dayake fes takaita Tayo suka fito.
Babu maganar gyara a tsakar dare Dan haka salloli sukai Dadah tayiwa Ameenatoun wanka Hafiz ya kawo tea da bread tareda kwai aka Bata Tasha tea sosai Amma bataci kwan ba tana gamawa tafara neman Jamaal kafin ta rikice bacci yayi gaba da ita.
washe gari da safe gyaran gidan dadah tayi tareda gyare dakin Ameenatou din tsaf tai mata wanka ta Saka mata kayanta ta zaunar da ita tana binsu da kallo kowa na faman yimata hidima kaman zasu cire mata ciwonta a rana Daya lokaci lokaci tana Ambatar a kira mata Jamaal da sister Ashley.
Abinci dadah ta Dora Babbah kuwa gefen Ameenatou Shima Akai masa shimfidar ya zauna Yana tayata duka shiririta ko rikicin da zatai
Hafiz kuwa wankin kayansu da suka dawo dasu yayi harma Dana Ameenatou din Yana gamawa ya fita aiki Super market din dayake Aikin yamma.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_