AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Ahankali ta Bude bakinta Cikin sanyi tace

“Mum Nur Allah ya Saka Miki da mafificin alkhairinsa duniya da lahira,
Allah ya qara Miki hakuri da juriya tareda lafiya,
Thank you for being calm Mum Nur,
I love you”

Ahankali Mum Nur taji Wani sanyi da nauyin datake ji a kirjinta tin ranar da Akai auren ya fada mata sbd Babu wanda ya zauna da ita ya rarrasheta bayan mijin nata wanda yayi iya kokarinsa gurin rarrashinta da nuna mata kauna da tsananin girman datake dashi a Idanuwansa sai Ameenatou din yanzu data rarrasheta batareda dogayen magana ba Cikin sanyi da kaunar gaskia Dan haka rungumeta tayi ahankali tana sauke numfashi me sanyi tana sake Jin har ranta tasamu sanyin komai game da auren.

Cikin kulawa da nutsuwa ta Bude Baki tace

“Thank you my baby,and I love you too”

Shiru sukai har Lokacin am na jikin Mum Nur din Suna debowa junansu kewa da Dan susar da zuciyoyinsu sukai ita am na mahaifiyarta da Bata duniyar ita Kuma Nur na kanta sedai Kuma yanda Dad Omar Bai hada farin Cikinsu da komaiba ya sakasu Jin nasa farin Cikin na karbansa hannu bibbiyu da zuciya daya Suna tayasa murna har zuci musamman am din da yanzu ne take Jin asalin tarihin soyayyar Dad din da Dr Aleena tin Yana asalin baqar fatarsa baida Wani gogewa sosai kaman yanzu.

A dakin Mum din suka wuni su biyun tana kokarin cire mata duk Wani abin damuwa ko makamancinta tinda da daddaren ranar zasu gidan SEELAHs din.

Jikinta ma jinta Yi ya warware sosai ba laifi sbd harga Allah taji auren a farko kafin Kuma suka samu nutsuwa dashi hakama tasan mahaifiyar Jeey dinta bazata taba cutatar da Mum Nur ba sbd itama she’s calm.

Ashley ma ta taho da ita suka qarasa wunin tareda Mum Suna debe mata kewa tareda nuna mata irin kaunar da suke mata harta qarasa sakewa zuciyarta fes sukai lunch dinsu a sama su duka harma da Didi data taho Fatmah Kuma batanan ta fita zuwa spa sbd yau zata ga Jamaal.

Dadah ma sosai ta sake ganin girman Mum Nur suka Taru aka wuni Cikin walwala da farin Ciki har yamma tayi tukuna kowa ya watse suka tafi dakunansu Dan sallan magrib da fara Shirin fitar.

Arfat Ameenatou tafara shiryawa da kanta Cikin wasu Ted Baker set na Yara Riga da wando navy blue sbd sune best kalan da akafi Siya a kayansa sbd sunfi komai fidda kalar fatarsa me kyau da tsananin haske.

Jacket ta Dora masa Akai da Valentino fcap itama navy blue sai jacket dinsa da talkarmansa na berluti dasuke ash me duhu qamshinsa me sanyi wanda sak turaren Dad dinsa ne ya zu ake masa amfani dashi sbd Jamaal din da kansa yake siyowa Yana bawa Ashley tana masa amfani dashi Wanda a duk lokacinda am taji qamshin jikin Arfat sai ta kusan hadiye numfashinta sbd tinanin Jamaal din na kusa sai take dena Saka masa indai ba Ashley datace itace take siyo masa ba ya shafa masa.

Itama wankan tayi ta shirya Cikin doguwar fitted abayar da dakanta aka aunata aka Dinka mata daidai jikinta shape daidai a Dubai dataje tareda Mum Nur a Lokacin.

Babu kwalliyar komai ajikin rigar bayan black crystal dasuke Saka rigar motsawa tana Dan daukan idon fidda asalin kudin da aka zuba gurin siyarta.

Qaramar veil Ash me duhu kalar takarman Arfat da jacket dinsa ta nade kanta dashi.

Babu kwalliya a fuskanta bayan eye Kajol me kyau dayake Cikin idonta ya qarawa Idanuwanta haske Yakuma sakata yin kyau ko man Baki Bata shafawa lips dinta ba hakanan ta fito tana fidda qamshi me sanyi sai wayarta Dake hannunta.

Ashley ma dagowar rigar ce a jikinta me shegiyar tsada datake rawa da veil data nade kanta dashi itama qamshinta yafi na Ameenatou tashi sbd ita Ameenatou saika kusantota kake jinsa har Cikin ranka sabanin ita nata Yana Dan tashi tinda ba igiyoyin auren kowa kanta gashi itama natan tsadar ne dashi.

Kaman hadin Baki itama Fatmah doguwar rigar ce a jikinta me shegen kyau da kwantawa a jiki maroon da black hakama Babu me makeup a cikinsu.

Didi ma doguwar Rigar Lafiyayyan lace ne ajikinta daya kwanta sai Mum Nur da ita Kuma Wani shegen material ne da kallansa kawai zai sakaka sanin ba kudi kadan suka siyesa ba Amma baida kwalliya sosai very simple and unique doguwar Riga da mayafin da itama Rollin nasa tayi sai ta koma kaman yarinya a cikinsu Ameenatou din.

Dadah da babbah bazasu samu daman zuwa ba Dan haka su kadai zaa bari.

Hafiz kuwa Yana fitowa Cikin lafiyayyun Cesare attolini black da suka fiddo kyansa da wayewansa fuskansa fresh da Hutu kawai.

Kallo daya Fatmah tayi masa ta dauke Kai tana barin gurin Shima Bai Kalleta ba ya qaraso Yana kama hannun yaronsa Wanda yake murnan ganinsa sukai gaba.

Sai a Lokacin Dad Omar ya fito Yana saukowa Cikin black Kaftans na Armanis da suke bayyanarda shine Asalin jden din a cikinsu sbd ilimin da wayewan bama daya ba sbd shine tushe.

Hannu ya miqawa Ameenatou Dake kallansa Cikin tsananin kaunarsa ta kama tareda shigewa gefen jikinsa kafin Mum Nur ta kama hannunsa daya suka fito Kai tsaye motocinsu Dake jere ana jiransu suka nufo.

Motar Dad Omar shine a Ciki da mum Nur sai Ameenatou.

Dayar motar kuwa Hafiz ne da Ashley sai Arfat da Fatmah sai dayar uncle Ahmed da Didi da Arry.

Barin Mansion din sukai Kai tsaye tareda nufar asibiti suka fara duba Siyam wadda dangin Mum dinta suka taho Dan samun saukinta su tafi da ita gurinsu Wanda Dad Omar Bai Musa Hakan ba zai aikasu India idan taji sauki zasu dawo da ita hannunsa sbd shine zai riqeta dan shine mahaifinta kaf duniya a yanzu.

Sunji dadin hakan sunyi masa godia tareda jinjinawa zuciyarsa kafin suka fara Shirin tafiya idan ya kammala musu komai.

Zuwansa asibitin da iyalansa kaf ya sake basa girma sosai a Idanuwan dangin Mum Sarrah din akan Siyam.

Suna barin asibitin Kai tsaye gidan Jamaal din suka nufa wanda Suma acan angama shirya dining room da komai gidan tsaf kaman Babu tashin hankalin daya faru a jiyan Kuma dayake tsarin ginin turawa ne Babu mahaukacin girman Nan sedai kusan kana shiga zaka San gidan turawa kazo ga Babu hayaniya
Chiefs dinsu da Maids dinsu duka sun tafi bangarensu Babu Wani bako bayan su Yan gidan.

Siddeeq ne da kansa ya tarbesu sai Ayesha wadda itama take shirye Cikin doguwar riga kwance a jikinta da silk scarf daure akanta.

Da farin Ciki suka tarbesu Suna musu barka da zuwa lokacin Jamaal ya sauko ya fito palon Yana sauke Idanuwansa akan Dad din ya rungumosa yana juyar da Idanuwansa da sukai Ciki take akan Ameenatou Dake gefen Dad din itama shi din ta kalla Idanuwanta na narkewa kaman zata narke masa agurin take ta kashe jikinsa sbd ganinta kadai kashe duk wata wutar jikinsa yake musamman ya azabtu daga jiyan zuwa yau dabai ganta ba Kuma Bai jita ba.

Sakin Dad din yayi Yana yiwa su Mum sannu da zuwa Cikin nutsuwa da Wani irin ajinsa da kwarjinin dayake cike musu Idanuwa da kyansa.

Dr Aleena ce ta sauko qasan itama ta nufo palon tana musu sannu da zuwa Cikin nutsuwa sanye Cikin daguwan rigar data qarawa haskenta kyau sosai itama Idanuwanta akan Mum Nur tana sake fuska sosai suka Dan rungume juna kafin sukai Ciki.

Siddeeq ne a baya da Ashley Suna kallan juna magana na cin bakin kowannensu.

Gaba zatai tabi bayan Dad dinta ya riqo hannunta tareda dawo da ita baya ya hada bayanta da kirjinsa ya rungumeta Yana lumshe Idanuwansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected