AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Qarasawa sukai gaban Babbah Wanda yasan ba komai bane ya sakasu shiga mamakin face sunan Omar jeden daya ambata Dan ko ciwon haukan ne da ‘yar Jaden sun San tafi karfin asibitin Nigeria bare shi da suke gani talaka yana tsaye da ciwo a jiki.
Dr Ibrahim ne ya sake jeho tambayarsa ga Hafiz sbd tinanin ko Babban baida cikakkiyar lafiyan Kai tsufa yafara cinye kan a natse cikin kokarin fahimtarsu ya Kalli Hafiz yace
“Daga Ina kuke?
“Menene cikakken sunan mara lafiyan taku?
Babu yanda zaayi su fada asalin inda suka koma a yanzu Dan haka Kai tsaye inda aka Sansu a Baya ya fada.
“Daga Nasarawa muke,
Wannan mahaifinmu ne,ga mahaifiyarmu Nan tsaye a gefe,
Ita wadda mukaxo Gani qanwata ce sunanta AMEENATOU OMAR kaman yanda ya fada”
Dr ibrahim zai sake jefa wata tambayar sbd kansa ya kasa dauka, shi ganin yake kaman Basu gane tambayarsa ba, dr Zakeer ne ya katsesa da sauri ta hanyar cewa su shiga ciki ayi maganar kawai.
Daman Hakan Dr Ibrahim Shima yakeda niyar yin Dan haka take aka shige dasu Babbah zuwa cikin asibitin aka bar securities da mamaki me girma da shakka sbd sunan daya fito daga bakin babban.
Kai tsaye office din md suke nufa Wanda yake asibitin tin sassafe sbd hankinsu duka yau din baa kwance ba da abinda zasu aikatawa Ameenatou,
A matsayinsu na likitoci sunsan illan abortion da hadarinsa musamman irin wannan da sune zasuyi sa da kansu,Barna ce akan Barna suke Neman aikatawa Dan rufe Barna da barnar,
Fatansa dai Allah yasa sunada Rabon rufe wannan Barnar batareda komai ya faru ba.
Shigowan su Dr Zakeer office dinsa ne ya Sakasa sauke ajiyan zuciya zaiyi magana su Hafiz suka kunno Kai.
Kallansu Dr Ibrahim yayi Yace su Jira waje tukuna.
Komawa sukai waje suna Jira Dr Zakeer ya rufe kofar ya dawo Yana cewa
“Dr ibrahim kana tinanin baban Nan Yana lafiya kuwa??
Numfashi Dr Ibrahim ya sauke Yana fara jerowa md bayanin komai kafin ya Dora da cewa
“Lafiyansa kalau ga dukkanin alama,
Kuma idan na Tina duka bayanin Ameenatou dayake rubuce a file nata itace Ameenatou Omar Kuma address nata Nasarawa ne kadai a jiki,sedai abin mamakin anan shine wannan din yace shine mahaifinta sannan Kuma ya ambaceta da Ameenatou Omar Jaden a sanina Kuma Omar Jaden Daya muka sani Babu wani”
Qara karfin AC md yayi sbd zufan Daya fara jiqasa hankalinsa na tashi kansa na daukan zafi kaman yanda Dr Zakeer Shima ya rude.
Wata masifar ce da alama take Neman Hawa akan masifar da suke ciki.
Meya hadasu da ‘yar Jaden Kuma??
Yar Jaden anmata ciki a asibitinsu ai qiyamarsu ta tsayu,
Suna baqatan bayani dai cikakke,
Idan dai yar babban ce su bincika kawai asirinsu rufe su Bata sallamarta ya tafi da ita batareda sanin cikin ba Dan tana tafiya record dinta clean zaa rubutasa Babu komai Babu matsala Dan ko zancen cikin ya bulla Babu ruwan asibitinsu lafiya kalau suka badata.
Wannan shawarar Dr Zakeer ya bada Amma suka kasa Naam da Hakan sbd tsaro Dan haka Dr ibrahim ya kirawo su Babbah suka shigo.
File dinta Dake office din md tin jiya
md din ya miqawa Dr ibrahim ya Bude Yana fara karanta informations nata Daya bayan Daya da abinda aka rubuta ya kawota asibitin da duka bayanai akan ciwonta da komai.
#MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
89
*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products
Location: LAGOS
We deliver nationwide
09013833502
https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL
************
Numfashi me zafi Dr Ibrahim ya sauke tareda dagowa ya Kalli Babbah dasuke zaune gefe cikin bada nutsuwarsa ga abinda zai tambaya da amsar zaa basa yace
“Baba kace cikakkiyar sunan ‘yarka Ameenatou Omar??
“Eh hakane sunanta” Babbah ya fada cikin nutsuwa Shima.
“Kaine ka haifeta?
Menene cikakken naka sunan?
“Sunana Nuhu babbah,
Ba nine na haifeta ba Amma a hannuna aka haifeta Dani da mahaifiyarta uwarmu Daya ubanmu Daya nine Uba Kuma uwar mahaifiyarta hakama itama nine ubanta nine gatanta Dan har ayau batasan ba nine na haifetaba.
Shiru sukai dukkaninsu na seconds kafin Dr Zakeer yace ko zamu iya sheda Hakan??
Da sauri Hafiz yace “eh” Yana ciro wallet dinsa daga aljihunsa ya Ciro id cards dinta guda uku duka masu hotonta da sunanta Ameenatou Nuhu babbah ya miqa musu.
Voters card dinta ne,sai national id card,sai Kuma na exams dinta na waec datai duka suna hannunsa Daman shine ko Yaya Abdul suke ajiyewa.
Address dinsu ya tambaya suka karanto masa Ya duba na jikin id cards nata shikuma Dr ibrahim ya duba na jikin file yaga Abu Daya ne Dan komai nata Babu Wanda JEEY ya saka na Seelahs ko na Jaden duka na Nasarawa ya Saka sbd tsaro Kar asan ita wacece din nuhu babban ne kadai bai saka a sunan mahaifinta ba ya saka omar sbd bai san sunan babbah na asalinba babbah kadai yasan suna ambatarsa hakama da sunan asalin mahaifinta aka daura masa aure da ita shiyasa Kai tsaye ya Saka mata Ameenatou Omar kawai batareda ya Saka Jaden din ba.
Md Daya matsu yaji inda sunan jden ya Hadu Da wannan maganar gabaki dayanta ya jeho tasa tambayar d cewa
“Menene cikakken sunan asalin mahaifinta?
Yana raye ko ya rasu ne?
Shiru Babbah ya Dan yi kafin ya Bude Baki Kai tsaye ba shakkar komai yace
“Omar Jaden seelah ne asalin mahaifinta”
Tsit suka sake yi md yana sake goge zufan goshinsa,
Kenan Dr JEEY yar uwarsa ce shine Bai taba nunawa ba koda wasa bazaka taba cewa ma ya Santa ba bare hada family,
Duk kulawan dayake Dan nuna mata da karban case dinta da yayi duk Yana sane,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun.
Zufa kowannensu ya sake sharewa hankali na tashi.
Dr Ibrahim ne yayi karfin halin tambayar Babbah dalilin kamuwa da ciwonta da abinda yasa duk tsawon wannan lokacin Basu taho sunzo gurinta ba.
Ahankali Babbah ya zayyano labarin da kusan kowa ya sansa A ranar daurin auren ‘dan Mam Seelah yayi taccident ya rasu tareda mahaifin matarsa da uncle dinsa Alh Omar jden wanda tin da Akai accident din Babu Wanda ya sake Ji daga Omar din da ahalinsa.
Iya daga Nan labarin yake tsayawa koina batareda an Dora da sanin Ina amaryar take ba bare danginta tinda su talakawa ne baa sake tada nasu zancen ba.