AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

A nasa bangaren kuwa Shima abubuwan sun tsananta Dan haka Shima suka jisa shiru ba labari kwana biyu,

Ana cikin Hakan jikin Ameenatou yaqi sauki Tako ina Sam Dan haka dole likitoci suka Maida hankali sosai akanta sbd patient din Dr JEEY ce kowa yasan tanada mahimmanci a gurinsa a asibitin dan duk yanda yakeda basarwa da kamewa duka an fahimci mahimmancinta a gurinsa Dan Yanda yake dubata daban da sauran patients hakama suna lure da kyautatawan dayake wa sister Ashley akan yanda take kulawa da ita batareda sunsan asalin alaqarsa da ita ba har yanzu din.

********Tashin farko abinda Dr Zakeer ya samu a results nata shine ya sakasa Zare farin glasses dinsa ya Ciro handkerchief dinsa ya goge glass din da kyau a natse ya sake mayarwa fuskansa ya Saka tareda sake daukan takardun ya Bude da kyau Yana sake karantawa.

Abinda ya Gani farko ya sake Gani Wani zufa na tsatsafowa daga goshinsa har tafin hannuwansa.

Baya tayi da kujeran dayake Kai ta office dinsa ya miqe tareda daukan sauran takardun ya nufi kofa ya fice zuwa office din Dr Ibrahim Yana sake dubawa da kyau Dan kada yaje aga ba Hakan bane ya zamana ya hadawa kansa masifa.

Harya Isa office din Abu Daya yake Gani ba gizo bane.

Yana zuwa office din cikin sa’a dr Charles ma Yana office din suna tattauna maganar Nurse Fahat da familynsa ke rokon a tsananta musu Neman lafiyansa,

Zufansa ya share ya iso gurinsa tareda ajiye takardun hannunsa kan table din gabansu batareda ya sake gaisawa dasu din ba bayan wadda sukai da safe da suka Hadu.

Kallan takardun sukai a tare kafin Dr Ibrahim ya dawo da kallansa kan Dr Zakeer din
Shikuwa Dr Charles takardun yake kalla har lokacin Yana Kai hannu ya dauka Yana cewa

“Menene?
Results din waye?”

Bude takardun yakeyi Yana fara karantawa.

Yana gamawa ya dago ya Kalli Dr Ibrahim Dake jiran Jin Menene kafin ya dawo da kallansa kan Dr Zakeer cikeda mamaki me girma yace

“pregna….””

Katsesa Dr Zakeer yayi da qarasa masa da cewa

“Yes,patient 6, Ameenatou Omar”

Dr Ibrahim Dake Neman shiga duhu akan rashin ganewa ne ya karbi takardun ya fara karantawa a bayyane.

Ajiye takardun yayi tareda dagowa ya Kalli Dr Zakeer cikin son Bude zancen sa kyau kan kowa ya sake yace

“Ciki ne a jikin patient dinmu?
A wannan asibitin?
A cikin asibitinmu?
Cikin haihuwa fa,
Cikin haihuwan ‘dan mutum fa??ko dai na aljanu ne??
Tayaya zaa samu wannan mummunan masifar Rana tsaka a asibitin Nan??
Kun San me Hakan ke nufi??
Kunsan license dinmu ne gabaki dayanmu ya hau Wani mummunan siradi kuwa na rayuwa da mutuwa?
Kaiii innalillahi.”

Dr Zakeer ma dayake cikin mummunan tashin hankalin share zufansa yayi sbd sanin Suma makomarsu irin ta dr Dee ce kenan,
Tayaya zaa samu patient dinsu da ciki?
Tayaya zata samu ciki a qarqashin kulawansu?
Me zasu fadawa Wainda suka kawota?
Me zasu fuskanta daga lokacinda zancen cikin ya fita Dan hukun Hakan me girma ne tinda mahaukata ne basa iya gane Wanda yayi musu Cikin sbd tabbas tabbas dole daga cikin ma’aikatan asibitin ne dole aka samu Wanda yake lalata patient tinda angansu Basu da hankali shiyasa ake hukunci me tsananin da zai lalata career din aikin mutum gaba Daya to su yanzu da baa San ta inda zaa San ina wannan masifar ta bullo ba.

Dr Charles daya fisu shiga shock kallan result din yayi Yana cewa

“Menene abin tsayawa fargaba da tashin hankali har Wani yasan da cikin bayan a cire mata shi asiri rufe Babu sanin kowa,
Kokuma tsayawa zamuyi tinanin abin yi har nurse dinta tasan da cikin zancen ya fita,
Kuna sane da Dr JEEY SEELAH ne ya Saka aka dauke Dr Dee daga Nan daukewan wulaqanci data Saka sa kashe kansa bayan sunansa ya gama Baci akan qwayoyin da aka samu a tareda gawarsa,
Dr JEEY na sanin maganar anyiwa wannan patient din ciki a asibitin Nan zai tabbatarda careers na mutane da dama a cikinmu sun lalace,
Ku kalla nurse Fahat Wanda bibiyan yarinyar kawai ya gwada yi Amma Ina yake yanzu???
Akwai Wanda ya Isa yayi magana akan Hakan??
Dukkaninmu munsan lafiya kalau Fahat yake Amma dare daya haukan ta samesa dole muka bi yarima muna Shan kida bare yanzu ace ciki,
Ciki na haihuwa fa??
Raping dinta fa kenan akeyi da alama ba so Daya ba akwai Wanda yake Kwanciya da ita a cikin ma’aikatanmu ko likitoci ma ko nurses ko clearners koma ward attendence duk zai iya faruwa ace Wani daga cikinmu ne.”

Shiru dukkaninsu sukai kowa na shiga nazari Dan sune manyan asibitin sai md Wanda Shima dole a sanar dashi asan mafita Dan kuwa daga kan likitocinsu har asibitin gabaki dayanta zaa iya sokesu.

Dr Charles ne ya buqaci abari ya sake aunata da kansa ya Gani Dan su sake tabbatarwa kafin su Sako md acikin zancen tukuna,

Naam sukai da Hakan Dan haka aka bari aga me sakamakon ze bayar.

Babu Bata lokaci Dr Charles ya koma office dinsa yayi abinda zaiyi kafin daga baya ya nufi dakin Ameenatou din.

Koda ya Isa sister Ashley na hanyar zuwa dakin itama Dan haka cikin girmamawa ta gaidasa suna qarasawa tare Yana tambayarta jikin Ameenatou din ta amsa masa da ba laifi tana samun lafiya zazzabi ne kadai yanzu yake Sakata gaba ko ya tafi Saiya dawo.

Dan juyowa yayi ya Kalli sister Ashley din wadda itama tayi wani irin zuru zuru da ita
Yayi mata kallan mintina kafin ya dauke Kai suna shiga dakin tareda wata sister fareeda data biyo Dr din.

Ameenatou na kwance lafe a gadonta tana Jin yunwa Kuma Bata son komai bayan fruits Dan yanzu su kadai takeso take Kuma ci sosai wanda itama sister Ashley sbd yawan siyansu da yanda Ameenatou Kesha yasa dole suka zama tata cimar itama Dan haka tare suke Sha ba sauki.

Har Dr ya iso gabanta ya tsaya Yana mata kallan tsaf Bata dago ta kallesa ba Danma ciwo ya Sakata laushi sosai da yanzu tafara rigimar kada ya matso inda take.

Tambayoyi yakewa sister Ashley akan yanayin jikin nata da yanda take Ji harma da tambayoyin da suka Saka sister Ashley kallansa cikin mamaki da gabanta daya Dan Fadi.

Bata amsa tambayar ba Sbd sister fareeda Dake tsaye tana kallansu,
Shima bayason fareedan ta fahimci wani abin Dan Haka ya kalleta tareda turata Wani aikin Dan bazasu kowa ya San komaiba bayan sister Ashley wadda itama Dan ta zama dole ne.

Sister fareeda n wucewa ya juyo y Kalli Ashley din ya sake maimaita Maya tambayarsa.

“When last did she see her period???

Sanyi jikin sister Ashley ke Neman yi sbd faduwan da gabanta ke tsananta yi,
A Sanyaye tace

“If na Tina daidai last month bataiba Amma na bayan na manta na last month din dai bataiba shi na Tina daidai,
Dr akwai Wani abin ne daya Saka wannan tambayar??

Shiru yayi Yana sake kallan Ameenatou din Baya buqatan qarin bayanin komai a matsayinsa na likita Kai tsaye yaga ciki a tareda ita sedai Kuma a tsakanin rayuwa Da rashinta dasuke ciki yanzu suna buqatan binciken kwakwaf akan cikin Dan tabbatarwa.

Sister Ashley ce ta kama masa ita suka fito zuwa office dinsa Wanda kafin ya fito tin dazun ya Saka aka kawo masa komai scanning zai mata Kai tsaye yaga abinda yake cikin baro baro ba Wani tsayawa jiran result din awo.

Ita kanta sister Ashley gabanta faduwa yakeyi sosai hankalinta na tashi sai zufa take tsiyayowa idan har ciki ne jikin Ameenatou kaman yanda ta fahimci su Dr din na zargi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected