AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Tin a cikin gidan suka fara rigima har suka Isa ta shige ya juya ya wuce inda zashi.
Da yamma kuwa babbah ne ya biya mata suka dawo gida tare Yana Bata labarin inda yaje da abinda ya Gani tanata Jin dadi.
Da daddare yau kusan kowa Yana gida lokaci Daya sukaci abinci su a tsakar gidan tanata zuba shagwabarta yanda takeso a cikin iyayenta da yannanta.
*****
Zaune yake a gaban Dad dinsa jikinsa gabaki Daya a mace,
Daga shi har Dad da Dad Lameenu dasuke palon su a zaune Babu me walwala ko farin ciki ko kadan a zuciya da fuskokinsu,
Tarin bacin Rai da baqin ciki ne yake sake tirnike zuciyar kowannensu Yana Kona jininsu.
Dad Lameenu dayake Jin kwata kwata baiga amfanin Haroon a rayuwarsu ba sbd Babu inda suka Kara gaba kullum sai Baya sukeyi suna Neman durkushewa ba shiri,
Rashin JAMAAL a rayuwarsu wani babbar balai da masifa ne Dan kuwa sun sheda Hakan Kuma suna kan shedawa tin daga ranar Daya barsu komai sai rushe musu yakeyi,
Shi baimaga dalilin wani Yanke yanken alaqa ba da Mam yayi da Jamaal din dan kuwa da Haroon din ya miqawa Dr Aleena can taje dashi tayita kayan rashin amfanin dashi.
Mam kasa cewa komai yayi sbd yanason ya kasawa ransa iya danne tsananin rashin ‘dansa JAMAAL a taredashi,
Yanason ya Hana abinda yake cin zuciyarsa gameda rashin Dansa,
A tsawon shekarun Nan da suka diba basa tare Babu ranar da Baya kwana ya tashi da tsananin son kasancewa da JAMAAL,
Babu ranar da Baya kewansa,
Babu ranar da Baya baqin cikin faduwa da rushewan da sukeyi sbd rashinsa.
Kallan Haroon ya sake yi Yana ajiye takardun hannunsa Daya gama karantawa y
Zuciyarsa na quna yace
“Se yaushe ne zaka zama me amfanin dazanyi alfahari dakai amatsayin Dana?
Kasan irin millions din da muke rasawa akowace safiya tindaga ranar da Jamaal ya tafi kuwa??
Zaka iya lissafa asara da faduwan da muketa yi kullum?
Menene yake faruwa acikin kanka ne da kwata kwata Babu Abu Daya a cikin lamuranmu dayake tafiya daidai?
Aikin site dincan a yanzu shi kadai ne abinda ya rage a tayar shine abinda zai hanamu karasa rugujewa sbd ka lalata komai,
Ka rusa abinda mukai aiki tukuru da jini da majina muka hada,
Ka rusa abinda Dan uwanka yayi aiki dare da Rana ya hada duk kana Neman lalata komai a cikin shekaru kalilan.”
Dad Lameenu kuwa kasa magana yayi sbd Jan da idanuwansa sukai zuciyarsa na quna cikin baqin ciki da tashin hankali.
Har abada bazasu hada Haroon da Jamaal ba sbd Jamaal zakin namiji ne da kosu suke shakkarsa,
Ga Haroon yau ya Sakasu a tsaka me wuya sbd Bai iya komaiba sai rusasu yakeyi da rashin amfaninsa.
Cikin zafin zuciyar Dad yace
“Ka tafi ka fara Shirin tafiya wancan babban project din,
Abu Daya nakeso ka sani,
Wannan aikin shine aikin dana Saka dukkanin burina akansa yanzu
Samun matsala akan wannan aikin shine rugujewanmu gaba Daya Dan haka ko rayuwa nawa zaa ci a aikin Nan banason ka tinkaroni da matsala duk tsanani duk rintsi,
Ka nutsu dakyau ka fahimci mahimmanci wannan aikin a gurinmu,
Ka tafi kasan abinda kakeyi idanma haryanxu rabuwarka da Dan uwankane ta kasa sakinka to ka sani wannan Karan a shirye nake da kawar da matsalata kowace iri ce.”
Wani abu me dacin gaske Haroon ya hadiye kansa da kirjinsa na wani irin nauyi da radadin dayake cikinsa na tsawon shekarun Nan,
Tinda Jamaal ya rabu da Dad Bai sake sanin farin ciki ko samun kauna daga mahaifinsa ba Kona Rana Daya ne,
Shi kansa ya sani baida jarumta ko ilimin aiki irin wanna da Kuma izzar gudanar da manyan huldodin kasuwanciba irin Jamaal,
Baida sa’a kaman Jamaal,
Baida cika ido da kwarjinin kasuwanci acikin manyan mutane na gida Dana waje kamar Jamaal
Rayuwarsa gaba dayanta akan abinda ya karanta ya kwallafa ta sedai Kuma babbar jarabansa itace kauna da son kyautatawa mahaifinsa Daya rufe masa zuciya da ido Amma duk yanda yake kokari Dan zama hasken idaniyar Dad din Hakan Bai taba samuwa ba saima lalacewa da komai yakeyi.
Baya tareda mahaifiyarsa,Baya tareda Dan uwansa Baya da kowa sai mahaifinsa da sauran dangin seelahs da duk Babu Wanda yake appreciating nasa ta koina da komai sai Hakan yafara tabasa ahankali ahankali har depression na shigarsa batareda kowa ya sani ba bare fahimta.
A yanzu da shine komai na Seelahs yadawo hannunsa shine yake juyata Babu abinda Bai saniba na sirrinsu Dad sedai bazai taba iya fadawa Dan uwansa Hakan ba,
Bai iya illegal huldodinsu ba,
Bai iya juya business na Seelahs ba na bayyane Dan haka gaba Daya rayuwarsa ta tashi daga Haroon seelahs Takoma wani mutumin daban dabai San kowanne farin ciki ba bare walwala sbd haryanxu Babu abinda yakeso kaman burge mahaifinsa ya samu yabo da alfahari daga garesa.
Wannan aikin na site a yanzu shine abinda zai basa Daman samun yabo da kauna daga Dad dinsa yanda yake buri Dan haka yayi alkawari tareda sakawa ransa zaiyi aiki tuquri akan wannan project din.
Shiri ya fara na tafiya Nasarawa tareda sakawa Akai masa booking na hotel da komai.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
31
Bayan ficewan Haroon daga palon kallan Mam Dad Lameenu yayi cikin nauyin zuciya da rashin Jin dadin komai na duniya yace
“Dole muna buqatan tsananta binciken abinda àka haifawa Omar duk inda yake sbd sanin inda suke zai Saka Omar din dawowa daga inda yake ya dawo cikinmu sbd sanin munsan yanada ‘da a duniya,
Idan ba Hakan mukaiba cikin gaggawa wlh muna gap da rasa komai munaji muna Gani Dan haka yanzu Kam dole mu tashi tsaye dakyau mu samo ‘dan Omar”
Mam da zuciyarsa tafi ta lameenu tsananta a cikin baqin ciki da tafasa tareda bacin Rai baice komaiba sbd Daman ya hangowa kansu Hakan daga ranar da suka Dora Haroon akan komai nasu,
Sam baida jarumta ko amfanin da zai musu yanda ya kamata.
Ta bangare Daya yasan duk Wanda zasu Saka a magajin nasu me gudanar da komai bazasu taba samun Jamaal ba Dan kuwa shi din zakinsu ne.
Numfashi ya sauke ahankali Yana kallan takardun gabansa da idanuwansa da sukai jajir Yana kokarin daidaita tafasar da zuciyarsa keyi,
A yanzu shima Babu abinda ruhi da zuciyarsa suke tsananin buqata kaman dukiyar Omar Dan ita kadaice zasu mallaka suyi tsayuwarda Babu ranar rushewansu a kusa sbd koba komai a tsaftace take Babu jinin kowa aciki Dan haka zeyi wuya ta shiga hannunsu ta lalace kaman yanda tasu ta dauko hanyar lalacewa duk Dan sbd Allah ya basa sakaran ‘da mara amfani sosai duk da Yana son dansa sosai Amma Sam Baya kaunar rashin amfaninsa har ransa yake Jin baqin ciki da tsanar Hakan.
Wayarsa ya miqa hannunsa Daya ya dauka cikin nutsuwa ya Nemo numbern BB ya Saka kira Yana dauka yace
“Ina buqatan ganinka yanzu”
“Yes Sir” ya fada Yana zare sigarin Dake bakinsa Yana zuqa cikin palon gidansa.
Cikin mintinan da Basu wuce hamsin da Yan Kai ba saigashi ya iso gidan Kai tsaye motarsa yayi parking ya nufi hanyar office dinsu Yana zare baqin glass dinsa Dake rufawa jajayen idanuwansa masu Bada tsoro asiri.