AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

“Zakiyi magana da JAMAAL Haroon??

Gyada Kai Ameenatou din tayi tana kallan wayar.

Matsar da wayar tayi zuwa gareta tace

“Kiyi magana”

Shiru tayi batace komaiba sai sanyi da jikinta yayi sosai da Jinsa sbd kewansa datai a bayyane take.

Cikin nutsuwa da kulawan datake bayyane sosai akanta taji yace

“AMEENATOU,
Ameenatou tana son ganin JAMAAL ko?
Zan dawo idan Mum taji sauki na taho dake,
Zaki taho right??

Gyada Kai tayi Wanda yaji Hakan Dan haka ya sauke ajiyan zuciya cikin kulawa yace

“Me Ameenatou takeso??

Kaman Yana kusa da ita ta dago ta sake kallan wayar kafin ta kalli Ashley ta dawo da kallanta kan wayar tana narkewa kaman zatai hawaye tace

“Ameenatou tanason JAMAAL Haroon”

Rintse idanuwansa yayi ahankali cikin Wani irin yanayi me nutsuwa kalman ta shigesa kafin ya Bude tareda sauke numfashi mara sauti da wata irin murya me sanyi yace

“JAMAAL zaizo gurin Ameenatou ba dadewa,
Zai tafi da Ameenatou”

Murmushin Jin dadi ta sake me sautin Daya sauka har cikin kunnensa ya sake lumshe ido Yana sauraronta.

Tambayarta yayi taci abinci tace eh,
Ya tambayeta taci chocolate Shima tace Eh,.

Sama sama ya ringa tambayarta tana amsawa cikin Jin dadi shikuwa jikinsa ne yake sake mutuwa harya gama wayar dasu tukuna sukai sallama bayan ya sake magana da sister Ashley din sosai akan yanayin jikin nata yaji Kuma Babu matsalan komai data taso Dan ya rubuta a file dinta ya dakatar da alluranta Dan haka aka Dena mata kwata kwata sai maganin Daya Dorata Akai,alluran Kuma an Barwa su nurse Fahat Wanda gaba Daya kusan yafi kowa hauka a asibitin Dan gabaki Daya JEEY din ya jujutasa haukansa ta gasken ce tuburan yake yinta shiyasa shi kullum a daure yake a gadonsa.

Suna gama wayar Ameenatou taketa murna tana Jin dadi JAMAAL din yace zai taho gurin Ameenatou.

Sister Ashley ma da Bata cikin farin ciki ko walwala kwata kwata ganin Ameenatou din nata farin ciki da murnan ya sakasata Jin itama sanyi harda murmushinta tana tayata farin ciki da murnan da ita kanta tayi kewan kulawansa akansu Dan tinda mijinta ya rasu ya dauke nauyin komai na rayuwarta Dan gidanta kansa Saida ya sauya mata sbd taimaka mata gurin rage radadin kewan mijin da kadaicin gidan datai rayuwa da mijin.

A can nasa bangaren tinda yayi wayar ma komai ya sake yi masa nauyi sbd zancenta na son Jamaal data fada wanda ya shiga zuciyarsa sosai gashi anan din abubuwan a daure suke Babu ranar tafiyansa a kusa sai anyi aikin mum dinsa zai iya barowa ya taho shiyasa ya matsu Siddeeq ya gama ya koma Nigeria duk da idan ya Tina Mam Baya Nigeria saiyiji sauki saukin barinta da yayi din acan.

****Tin daga ranar Babu ranar da Baya waya dasu Kuma yayi magana da ita duk tsananin zamansa busy kuwa Saiya kirasu din Ameenatou ke samun walwalan kyale sister Ashley da Rigiman a kirasa hakama Shima saiyayi magana da ita din yake samun nutsuwar ranar duk tushewan abubuwan kuwa.

Sabo da hakan ya Saka idan Bai Kiraba ta ringa rigima kenan tana Hana sister Ashley zaman lafiya har takai video call yake Kiransu Duk da baiso Hakan ba Dan duk yanda yakeson ganinsa ya Hana kansa yin video call dasu ne sbd zuciyarsa Dake son Raba tinaninsa,hakama itama yasan rigimarta ta son ganinsa zata qaru ne ta Hana sister Ashley zaman kalau.

Aikuwa Hakan ne ya faru Dan idan ya kira tana karban wayar daga sister Ashley Taga Babu fuskansa Akai ta ringa rigima kenan dole suka koma video call din kullum Wanda Hakan ke yaga zuciyarsa Amma Yana basarwa da dannewa Amma baya Wani dadewa duk rigimarta haka yake lallabawa ya kashe.

Hakan yasaka kullum sai anyi rigima da ita yanzu dan Babu Daman ayi wayar a kashe ta ringa rigima da fitina kenan harda su kuka sosai wasu lokutan wasu lokutan kuwa rigima ce sosai har sai ciwonta ya tashi ta rikice musu da kyar ake samu a shawo kanta ta saurara duk da baa san menene yake kawo hakan ba sister Ashley ce kadai tasan menene abinda yake kawo hakan amma babu ma abinda zai sakata fada ko barin ma a sani.
#MAMUH#
#AMEENATOU
#JAMAAL JEEY SEELAH
#HOT
#ROMANCE
#BESTLOVE
#SEELAHS
#JDENS

 

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
86
*_AISHA’s COLLECTIONs_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products

Location: LAGOS
We deliver nationwide

09013833502

https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL

************
Kwanaki nata Dan tafiya,yawan Rigiman datakeyi yanzu ya Saka take jawa kanta zazzabi suyita fama saita kwana biyu sister Ashley ta samu ta warke,

Sister Ashley tana sanar masa ko ciwon Kai Ameenatou din tayi Dan haka ya rage yawan Kiran da mugun shagawabatan dayake yi a wayar sbd bayason yawan ciwon Shima,

A nata bangaren kuwa rage yawan Kiran ya Saka ta qarasa rikicewa kullum sai anyi gama da ita ta koma kawai wata rigimammiya kullum sister Ashley cikin dawainiya da fama da ita take sai itama ta koma Abar tausayi sauran nurses kuwa duk sai suka ji basa kaunar Ameenatou din ko kulata basa iyawa kowa ya Barwa Ashley wahalarta duk da Daman Tim can itace me wahalar Amma dai idan rigimarta ta tashi kusan nurses na taruwa akanta.

Wannan rigimar tata tasaka lafiya take Neman gagararta yau lafiya gobe ciwo take tafara rama haka kawai tana Wani irin haske kaman zata koma jinjira,

Ciwo me wahala takeyi sbd sosai take laushi idan ya tashi ko motsin kirki Bata iyawa ko tayar da ita sai sister Ashley tayi,
Itama sister Ashley din yanayi na zuciya na rashin mijinta da rigimar Ameenatou din datai yawa tareda wahalar ya Sakata itama layin Ameenatou din zazzabi takeyi sosai da rashin lafiyan Dan haka suka koma dukkaninsu sai ahankali.

JAMAAL ma dole ya sake rage Kiransu sosai tinda Kiran ke Saka Ameenatou din rigima da tashin ciwon…

Wannan yasa abubuwan suka fara cabe musu Amma duk da Hakan karfin hali sister Ashley keyi sosai tana kulawa da Ameenatou Dan tafita jin jikinta sosai hakama batason asan dukkaninsu Basu da lafiya sosai irin Hakan Dan zaa iya Bata Hutu ita ace saita warke to Kuma a yanzu da Ameenatou batada lafiyan batajin tafiyanta shine maslaharsu Dan kuwa qarasa rikicewa Ameenatou din zatai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected