AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_
Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200
*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*
*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*
*_MTN/VTU 09134848107_*
_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
18
Shekarun Dr Jamaal Seelah Kusan 15 zuwa 16 da dawowa hannun Dad dinsa kwata kwata,
Kuma a wainnan shekarun abubuwa da yawa sun faru wainda suke akan wani matsayi na daban.
Tinda Jamaal ya dawo gurin mahaifinsa ya zama dukkanin wani abin alfahin Dad din sbd iliminsa da zafin kansa a komai daban yake Dana kowa dayake cikin ahalin seelahs,
Likita ne shi Kuma marikin dukiyar mahaifinsa ne shi Mai kulawa da kusan duka kamfaninsu batareda Saka hannun Haroon aciki ba sbd gaba Daya Haroon ya koma tamkar wani matsoraci kaman yanda Dad din ke fada shiyasa kwata kwata Dad din Baya wani yinsa.
Haroon shine yasan ciki da wajen huldodin su Dad sosai sbd shine lawyer dinsa a yanzu Daya zama cikakken lawyer me zaman kansa Kuma kwararren Daya San aikinsa,
Yasan duka boyayyun illegal huldodinsu da Babu Wanda JEEY ya sbd tsananin taka tsantsan da boyewan da suke masa Dad Baya kaunar yasan ko aikinsa Daya mara kyau Dan kuwa JAMAAL din na sani zai iya barinsa har abada ya komawa Dr Aleena Kuma zai iya Jin haushi ko tsanarsa ko janyewa daga garesa Dan haka duk wata mummunan boyayyar harkarsu Babu wadda JAMAAL SEELAH ya sani suna tsananin kiyaye Hakan,
Haroon Daya San komai baida ikon fadawa JAMAAL din bare Bude hanya komai kankantarta da JAMAAL din ze sani hakama shi Daya sani Yana taka tsantsan sosai akan bayyanar sirrinsu sbd sanin hukunce Sharia da shariar kanta,
Sharia da aikin shariar ya ratsasa sosai da yake kiyaye kaidojin aikinsa Baya shiga shiga huldodin Amma dai shine me riqe da mukullin rufe sirrin batareda barin hanyar fitarsa ko kadan ba hakama Baya taba barin kowace matsalar da zata bayyanarda huldar iyayensa ta aikin danyar zinariyar Dake tafiya da rayukan mutanen da Basu da adadi ba hakama da drugs masu tsananin hadarin gaske wainda BB ne akan wannan bangaren duk da shine riqe da sirrinsu na boye da babu Wanda ya sani Haroon din Shima baisan iyayen nasu sun taba dauka rayukan mutane da hannuwansu ba Kuma Yan uwansu tamkar jininsu Dan haka Bai taba kallan Dad dinsa ko daddy lameenu a matsayin komai ba face jajirtaccin Dake Gina ahalin seelahs a boye batareda sanin irin gwagwarmayar dasuke fama da ita ba.
JAMAAL SEELAH a yanzu da dukiyarsu da komai yake hannunsa Yana gudanar dasu ne akan ilimi da kwarewa sosai dukiyarsu Daketa business din gaskia da duniya ta sani take sake habbaka da samun cigaba da nasarori Dan haka Dad ke sake Jin tsananin alfahari da farin cikin kasancewar Dr Jamaal Seelah dansa ne jininsa ne.
A can Poland a asibitin mahaifiyarsa yake aiki Amma anan din duk girma da tsari tareda dukiya me yawan da Dad dinsa ya kashe aka Gina masa asibitinsa ta kansa maidata yayi asibitin marasa karfi da tallafi Dan kuwa raayinsa ne gidan asibitin duba mara lafiya cikin tsananin sauki da Bada taimako sosai.
Hakan da yayi Dad Bai hanasa ba Bai Kuma nuna komaiba duk da Hakan yayi tsananin Bata ransa Se kawai sukai Hakan batareda saninsa ba ana kawo magani mara quality a asibitin Amma cikin ikon Allah Hakan Bai taba bawa Dr JAMAAL din matsalaba saima sake daukaka da suna da mutunci harma da girma dayake samu gurin mutane sbd tausayinsa duk da kwata kwata baida sakewa ko kadan sai a gurin patients dinsa wannan zakaga ya sake musu kyakkyawar fuskarsa me daukan ido sosai Amma badai ma’aikatansa ba harna asibiti harna sauran business dinsa.
Daga Baya Suma su Dad da sukaga asibitin sake qarawa SEELAHs girma da mutunci sosai takeyi tareda mutunci sai suka koma suna Jin dadin Hakan Amma dai a fili kawai cikin ransu Dad din Babu abinda yake so da burin kaman Jamaal ya aje komai kwata kwata ya shiga cikin huldansu ya riqe komai sbd dagashi har daddy lameenu kallan Jamaal sukeyi amatsayin sa’arsu Dan duk abinda ya Saka musu hannu Akai sai yayi musu yanda sukeso harma fiye Dan haka suka rasa yanda zasuyi su sakashi cikin huldansu na boye sunada tabbacin zasu samu harma abinda basutaba tinanin samu ba karshe ma dukiyar Omar Dake kashesu da ransu a duk numfashin dasuke shaqa tasu zaso tafi tasa su Dena wahalarda kansu duk da ciwon dukiyar Omar da rayuwarsa ma gaba Daya wani mummunan kurjin ciwo ne Da Babu ranarda zai fashe yabarsu saisun rufe kasa da idanuwansa.
Dr Jamaal Bai cika zama available sosai ba a Seelahs specialist da safe sai yamma Kokuma da daddare shine Asalin lokacinda kake samunsa a asibitin Dan yafi samun nutsuwa sosai acan da dare zai zagaya patients nasu sosai ya duba su tareda Basu kulawa sosai.
Su kuwa a bangaren su Dad Hakan shine daidai yayi musu
Da safe Yana tareda su a gurin aiki da yamma zuwa dare Yana asibitinsa sukuma ana gudanar musu da tasu huldar lokutan.
********Rayuwa tayiwa kowa yanda yake so sosai harma da qari dan kuwa lokaci yaja ayau sunkai JAMAAL SEELAH yana musu huldodinsu da duk sukeso batareda yasan da yawa ayyukan dayake musu na harkar banza bane sun taru sun rufesa duk da kulawansa sosai sun fisa kiyayewa sbd Bai taba tinanin wani abu Yana gudana a cikin familynsa ba da Bai saniba,
Sam Babu tsoro ko shakka ko rashin saa a lamarinsa saima izza da Kai tsayen da Babu acikin familyn kamansa,
Idan akwai abinda yafi farin ciki da Kwanciyar hankali tareda alfahari da Jin Babu kamansa to Dad Mam Yana ciki,ko sunan wani idan ba Jamaal ba bayason ana ambata a ‘dansa,
A duniya ko asirinsa Baya tsoron ya bayyana ga duniya kaman yanda shakkarsa Daya da tsoronsa Daya JAMAAL yasan su din su waye ne,
Me sukeyi a boye,
Ina suke zuwa,
Me suke hadawa da kuncewa uwa Uba abubuwan da sukai da rayukan da suka kawar ciki hadda na Dad Omar dinsa Daya kasa cire masa shi daga zuciyarsa kwata kwata duk kwata kwata haryanxu Babu Hulda tsakaninsu da Omar din.
Wannan kadai ne yake jijjiga zuciyarsu da tsoro da fargaba Amma bayan wannan ko Hukuma da duk wata sharia da masu yinta baima daukesu abin sakawa a lissafi ba Dan ya Dade da karbe wannan power din a hannunsa dukkanin wata hukuma da sharia sune suke juyata yanda sukeso su Saka a kawar musu da Wanda duk sukeso da sunan sharia.
Yanzu cigaba da karfin da suka sake samu akan barnarsu shine da sharia suke amfani a kawar Dana kawarwa a rufe na rufewa har karshen rayuwa,
Sun Dena Bata hannuwansu da jini Amma na Abinda Omar ya Haifa da Omar din shikam halastacce ne a gurinsu.
A bangaren Daddy lameenu ma kaman yanda Mam ke bugun gaba da alfahari da Jamaal haka yake wannan alfaharin dashi Dan kuwa manyanci ya Saka da yawa fiyeda Rabin nauyin dayake kansu Jamaal din ya dauke musu hakama Bai taba banbanta matsayi ko kaunar Dad dinsa akanshi ba sbd sanin shi din qanin mahaifinsa dayake kallo uwa Daya Uba dayane Dan haryanxu kaf familyn Babu Wanda haryanxu yasan ba uwa Daya Uba Daya SEELAHs suke ba.