AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Rayuwa tayiwa Hafiz nauyi sosai Dan Babu abinda yake kalla kaman haihuwan Ameenatou da Baya kaunar ko kadan tazo da matsala,
Hakama Babbah koyaushe maganarsa daya shine Hafiz yayi kokari ya tanadi komai kada Ameenatou ta haihu da matsala ko buqatan komai.
Duk yanda hafiz yake kokarin ganin samun aiki lamarin ya gagara Dan haka kullum yawon aikin karfi yakeyi shiyasa ba Wani abu yake samu ba duka wahalance yake koyaushe,
Cikin Ameenatou Koda ya shiga wata 8 Hafiz ya sauya kamanni gabaki Daya sbd azabar rayuwa da wahala tareda nauyin dayake kansa da yayi masa yawa,
Duk zafin Nemansa da yanda yake tinanin samun mafita kafin haihuwan Ameenatou lamarin ya tsaya cak Dan haka kawai ya yankewa kansa shawarar abinda zai inganta rayuwar Ameenatou dinsu da abinda zata Haifa tareda tsaronsu da samun yancinsu tareda tsayawa su fuskanci komai da kowa kansu a tsaye dan haka batareda sanin kowaba yafara neman hanyar da zai sanar da OMAR JADEN inda suke dan yasan duk inda yake zuwa yanzu yana can yana nemansu.
A yanzu dai Kam Tako ina dukkaninsu suna buqatansa musamman Ameenatou hakama shi nasa karfin Neman Yana Neman qarewa kaman Wanda Bai taba shiga aji ba,ga babba ma duk da ya samu lafiya yanzu Amma Babu karfin nema yanzu,ga Dadah ma duk wahala na Neman tsofar da ita,
Babu me farin ciki ko walwala a cikinsu shiyasa haryanxu sun kasa sakewa sosai a cikin mutanen anguwansu koyaushe suna kame a guri Daya.
Koda Ameenatou ta shiga watan haihuwanta ta sauya sosai tin daga kan lafiyan jikinta harta kanta sbd Takoma shiru shiru sosai ko magana batason yi hakama komai na juyewan kanta kusan ya dawo daidai kawai abinda take kasa tinawa kanta na juyewa wasu lokutan shine shin haroon Yana Ina??
Waye Jamaal a gurinta hakama waye Haroon??
Hakama kamanninsu na mutum Daya take Gani a idonta Kuma ta kasa tantance Ina kanta yake yanzu Ina ta baro.
Babbah da Dadah daidai gwargwado sunata Shirin haihuwarta Kuma Shima Babbah yanzu Babu abinda yakewa yarsa fata bayan kyakkyawar rayuwa ingantacciya itada abinda zata Haifa masa Wanda sun Riga sun rungumi kaddara basa fatan ma tsayawa Wani janye janyen Neman uban sbd rufawa Kai asiri.
Ta bangaren Hafiz ya zurfafa Neman hanyar isarwa da Omar Jaden Sako ta duk inda zai iya Amma rashin kudi ya Hanasa Isa ga wasu hanyoyin da yawa na Isa ga garesa dashi.
Har Abuja yaje so biyu Dan samun isarda sakonsa a companies dinsa Amma kwata kwata ko Daman shiga Bai samu ba bare Isa ga manyan da sune zasu dan iya masa hanyar magana da Jden din ko Kuma Ahmed hakanan yake kashe kudin mota a banza ya dawo.
#MAMUH#*_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
97
*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products
Location: LAGOS
We deliver nationwide
09013833502
https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL
************
EDD din Ameenatou sauran sati uku Hafiz ya shirya kudaden da suka Tara na haihuwar ya cewa Babbah interview aka kirashi Abuja ya tafi Lagos kwanansa biyu Yana yawo a tsakanin companies din JDENS Dake Lagos Babu nasara harya Yanke shawarar dawowa dai sai Kuma ya tafi Dayan kamfanin Wanda shine ma ya fara zuwa daga farko.
Cikin ma’aikatan da zaawa interview ya samu ya shige daqyar Allah ma yasaka da takardunsa ya tafi Daman Dan Koda Allah zai basa wani aikin duk da basuda raayi ko kadan na zaman Lagos Kuma.
Director din kamfanin ne ya kallesa lokacinda ya gama jero masa bayanin Omar Jaden da kansa yakeson magana dashi idan da hali Kokuma a Isar masa da Sako Dan Allah.
Sake kallansa yayi a wulaqance zai kira securities Hafiz din yayi saurin sanar dashi ‘yar Jden dince ta cikinsa ake magana Akai yayi masa alkawarin ba karya yakeyiba.
Sake mamaki da takaicin zancen yayi sbd a saninsu Jden baida ‘ya ko ‘da.
Rantsuwa da magiya cikin qasqantar da Kai Hafiz yaci gaba da rokonsa akan Sako kadai yakeson ya sanar masa Wanda yayi masa alkawarin wlh tallahi sai Jden yayi masa matsayin da baiwa kowa ba akan wannan sakon.
Tsoki director ya sake Yana daga wayarsa ya kira securities kawai.
Da sauri Hafiz ya Ciro numbernsa Dake dauke da cikakken sunansa Dana Babbah ya ajiye gaban director Yana magiya da rokonsa akan wannan sakon kadai yakeson a isarwa Jden din batareda cewa komaiba.
Jansa securities sukai ciki zafi da wulaqantawa suka fice dashi har wajen gate suka miqawa Yan Sanda Dake waje suna Jira.
A station Hafiz din ya kwana washe gari suka sakesa da kansu ya fito a wahalance yunwa da zazzabin wahala na Neman illatasa Amma hakanan ya daure tareda dangana ya hakura akan maganar Neman Jden yabarwa Allah komai inshallah zasu samu mafitan da zasu reni babynsu da kansu.
A ranar ya tattara ya shigo motar dawowa gida.
Bayan dawowansa jinyar wahala datake cin jikinsa da rayuwarsa yayi tsawon kwanaki Amma dole ya daure ya tashi yaci gaba da fita nema sbd Babu me nemowan sai shi.
Acan kuwa director bayan tafiyar da Akai da Hafiz samun kansa yayi da rarrabuwar tinani,
A iya saninsa Sir Jden Bai taba haihuwa ba Amma Kuma kaman yanda ake magana dukkanin dukiyarsa sunan AMEENATOU ne Akai Wanda da yawa suke cewa sunan matarsa ne data rasu wasu Kuma suce matarsa ta rasu bazai yiyu yaci gaba da Saka sunanta akan kadarorinsa ba da dukiyarsa,
Wannan shine sirrinsa Daya da kowa ya rasa gane gaskiyarsa ko maanarsa,
To idan da gaske wannan yaron yakeyi Jden nada ‘ya Kuma tana hannunsu???
Idan ya miqa sakon zai iya samun matsayin dayake buri kuwa??
Tabbas zai gwada sbd a banza wannan matashin bazaiqi fadan komaiba ya Bada number kawai da suna Wanda Hakan na nufin Jden din na Gani zai iya gane komai kenan??
Kwana biyu director yayi Yana shawara da Tinanin gwada sa’arsa Dan haka a kwana na hudu ya dauko sakon Ya zubawa takardar idanuwansa dakyau ya qarewa sunan Hafiz Nuhu babbah da Nuhu babbah sai Kuma AMEENATOU NUHU BABBAH da manyan baqaqe kafin numbernsa a qasa.
Shiru yayi Yana sake karanta sunan AMEENATOU din Wanda yanda yake rubucen Nan kusan haka sunan yake rubucen a cikin zuciyarsa na tinanin Allah yasa Hakan ne a zuciyar Jden.
Shi kansa baida matsayin magana da Jden din direct Wanda ya Yanke alaqar komai da Nigeria Yana jinya Amma a saninsu ya warke a kwanakin akace Amma dai babu Wanda yasan a qasar dayake.
Da Sir Ahmed suke magana Shima kusan sai Wanda yakai yake iya magana dashi sbd shi kansa babba ne me girman da sai me babban matsayi Amma shi dayake Yana cikin masu yawan gaidasa a waya Dan haka Yana communicating dashi Kokuma yace Yana bibiye dashi sbd duk sati Yana tura masa sakwan gaisuwa sbd Baya daukan waya sedai ka ajiye masa Sako.