AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Tashin hankalin dayafi na farko sister Ashley ta shiga da wannan maganar Dan haka ta sake haukacewa da Neman su JAMAAL Amma kaman Hakan bazai taba faruwa ba,

Ameenatou kuwa kaman kada asan da cikin jikin ya Kara rikicewa takai bayan Kwanciya Babu abinda take iyawa hakama zazzabi me karfi kullum dashi suke kwana dasu suke tashi takai Saida su Dr Charles da kansu suka bata Daman ringa kwana da ita a dakin Dan basa son a yanzu kowane nurse ko Wani likitan Yana rabarta sbd kada tsautsayi yasa ma Wani ya San me ake ciki Dan kuwa sun yadda suyi komai ciki hadda ko kamawa tayi su banka mata alluran da zata sakata tafiya har ita har cikin to amma hakan zai saka asan da ciki a jikinta kafin ta mutu sbd zaiyi zuba hakama sister Ashley idan ba harda ita zasu hada ba to bazata taba barin hakan ba dan haka sukai watsi da wannan shawarar ta dr Charles suka zabi ta dr ibrahim a cire cikin sai a tsananta bincike da tsaro asiri rufe.

Sister Ashley kasa yadda tayi da maganar cire cikin Amma Kuma tinda sune manyanta sunfi karfinta take ma suka fara Shirin dauketa daga asibitin gaba Daya Dan Haka hankalinta ya tashi ta nuna tamince dan kada a dauketa daga asibitin tabar Ameenatou da komai zai iya faruwa akan cikin Nan ko qarasa tasan zasu iya.

Ranar tafiya da ita da Ameenatou din zuwa inda zaa cire cikin Akai Dan haka Duk ta sake shiga tsaka me wuya,
Tashin hankali da damuwa da rashin mafita ya Saka ciwo itama sakota gaba takai har kwance daqyar take iya dawainiya d Ameenatou wadda itama take kwance ciwon take fam dashi Wanda ba iya na laulayi kadai ba hadda na kan nata.

Ranar da sauran kwana Daya da zaa tafi cire cikin sister Ashley tin tsakar dare take Kiran Siddeeq da JAMAAL bata samu,

Bata taba tinanin rubuta musu text ba sbd maganarta ganin takeyi tafi karfin text saidai maganar Baki da baki,

Bata Ji dadin bayyanar ciki a jikin Ameenatou ba Amma Kuma batason ayi mata abortion tinda Allah yariga yasa ansamu din hakama me cikin baisan dashi ba ace ancire,
Qari Kuma Rabon da zaa Haifa din shine zai taimakawa auren ya tabbata Kila bayan warkewan Ameenatou.

Washe gari tinda safe bayan ta tagama yiwa Ameenatou komai ta Bata tea Tasha harma da bread
Wanka Tayo mata suka zauna tana shiryata tanajin zuciyarsa na sanyi hakama jikinta.

Ameenatou ma yau jikin nata a Sanyaye yake itama Dan haka fararen idanuwanta da suka rame sosai take bin sister Ashley din dasu har tagama mata komai ta gyara mata gadonta da kanta kwantar da ita tareda dauko apple biyu ta ajiye mata gefenta sbd fita zatai asibiti taso zuwa Kai kanta sbd ciwonta tsananta yakeyi itama Amma gidan umman fadila Data taba Jin anguwan datake a bakin siddeeq zata tafi sbd daga yau dinnan idan Batai waya da JAMAAL ko Siddeeq ba komai zai iya faruwa duk da ta sadakar idan taje ta dawo ta Barwa Allah a cire cikin itama Ameenatou din ta huta da abubuwan da zasu iya biyo Baya idan maganar cikin ta fita har ga familynta ko na JEEY din.

Da zata juya ta fice riketa Ameenatou tayi ahankali tareda dago idanuwanta dake cikeda Hawaye ta kalleta cikin sanyi da nutsuwa tace

“Ameenatou Ashley takeso,
Ameenatou batason kowa Ashley da JAMAAL Haroon takeso”

Juyowa Ashley din tayi ahankali ta Kalli Ameenatoun kafin ta sauke numfashi me sanyi ta dawo ta rankwafo tana shafa kanta zuwa fuskanta tace

“Sister Ashley itama tanason babynta Ameenatou Amma zataje ta kira JAMAAL din Ameenatou,
Ai kinason ya taho ko?

Gyada Kai tayi ahankali tana Dan lumshe idanuwa.

Cikinta sister Ashley ta kalla taji jikinta ya sake sanyi,
Cikin kulawa tace

“Ameenatou tanason babyn da zata ringa goyawa ko??

Shiru tayi tana kallansa Dan batasan me take nufi ba Bata gane komaiba.

Hannunta sister Ashley ta kama ahankali ta Dora akan cikin ta Kalli cikin idanuwanta tace

“Ameenatou tanada baby anan,
Ameenatou zata samu babynta idan ya girma,.kinaso ko??

Batareda tasan me Hakan ke nufi ba ta gyada Kai tana taba cikin.

“Kada Ameenatou ta bari kowa ya taba mata babynta Dayake Nan kinji??
Dan haka duk Wanda ya taba Miki babynki ki fada masa Ameenatou tanason babynta,babyn sister Ashley kinji??

Sake gyada Kai tayi ahankali tana sake Dora hannunta Kan cikin.

“Sister Ashley tanason Ameenatou”

Wani sanyayyar murmushi Ameenatou din ta sake mara karfi sbd farin cikin kalaman sister Ashley din daya ratsata cewan tana Sonta.

Itama murmushi sister Ashley din ta sake tana juyawa ta fice.

Tana fitowa asibitin ta samu taxi ta hau ta suka wuce.

Tafiyan Mintina kusan 30 sukai kafin suka shiga anguwan datasan umman fadilan take duk da street din kadai tasan sunansa yanzu ne zatai tambayar gidan.

Suna shiga anguwan wata Motar su BB Na fitowa shine yaga fuskanta,

Dakatar da Bullet yayi daga tuqin Yana cewa

“Juya naga sister din asibitin Dr Dee da muketa nema Amma ta tare asibiti yau ta fito”

Kallansa bullet yayi Yana cewa

“Itace wadda aka aika mijinta sky sbd tabar asibitin ta zauna gida a kaddamar mata Dan idan tana asibitin gurin Ameenatou Babu Chance??

Cikin sauri BB ya amsa da “eh” Yana bin motar da kallo gashi anguwar Babu mutane sosai Kuma Daman suma umman fadilan suke nema sbd lam Yan zargin tasan inda su Babbah suke Kuma Babbah ne kadai ze iya zuwa ya warware masa auren JAMAAL da AMEENATOU tinda kawar da ita ko cigaba da juyar da kanta ya gagara gwara ya raba auren maganar gadon ya warware sbd MAM ya Dena maganar dukiyar Omar kwata kwata yanxu a cikin tsaurinsu Wanda ya tabbatarda ba dan komai bane sai ya gama da omar da dukiyarsa tinda ‘dansa ya auri ‘yarsa tak.

******A daidai wannan lokacin kuwa taxi din sister Ashley na barin bakin asibitin wata taxi din ta parker Babbah Dake Baya ne yafara budewa ya fito kafin Hafiz dayake gaba ya biya driver din ya Fito.

Dadah ce tayi ta karshen fitowa Dan itama bazata iya zama baa taho tareda itaba suka dungumo zuwa gate babbah na kallan sunan asibitin mahaukatan ace Ameenatou dinsa ce a ciki.

Hafiz ne yake riqe dashi Dan baida Wani karfin Dan bawai warkewa yayiba.
#MAMUH#

 

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
88

*_AISHA’s COLLECTION_*
Hajiyata Kinason kiyi kasuwanci amma bakida jari?
Ko kuma kinada jarin amma bakisan maiya kamata ki fara saidawa ba?
Tou hajiya nesa tazo kusa ga sauki yazo na kawo muku inda zaku samu kaya a cikin farashin sari,muna saida kaya kala-kala inda zaki samu a cikin sauqi da rahusa.Akwai varieties of women accessories ranging from Atamfa, Laces and shoes at both wholesale and retail..
Hajiya da kayan da kika sani da Wanda Baki saniba harma da Wanda Baki taba Gani ba na kayan alfarma da burgewa da asalin kyau na quality kizo karki bari ayi Babu ke,
ko kasuwaci ko sanyawa,ko ankon biki,lefen alfarma,kayan sallah..komaima namu inshallah na musamman ne da zakiji dadin kasancewa a cikin kasuwanci damu…
Join our group to see lot of our amazing products

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected