AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Ashley kallan Dadah tayi tace

“Dadah Dan Allah ki rarrashi babbah kada zafinsa ya haura wlh nidai nasan nayi kuskure Amma bazan sake ba.”

Dariya suka so sakata musamman Ameenatou da duk tayi Sanyi ga zazzabi tana ji me qarfi sbd kukan datake fama dashi tin ranar da Cikin ya bayyana a Cikinta har yau din Amma Kwata kwata batajin ma zazzabin bayan babbah tinda su Dad sun sani tin jiya su.

Jamaal barin gidan yayi Dan Basu Damar daidaitawa Amma da Arfat ya tafiyarsa hakam idan cikinma sunqi amsa kaman yanda sukaqi amsar auren mamaki zai bawa kowa.

Fatmah kuwa Kuka takeyi kaman ran zai fita sbd Jin Jamaal ne uban Cikin Kuma yasan da hakan yabarta ta tsaya gabansa take sanar dashi Ameenatou nada ‘dan shege Ashe kallan sakarya ma yake mata duka wannan lokacin.

Gasu Dad take kowa ya dauki mummunan fushi da ita Jin itace ma tafara fadawa Jamaal Ameenatou na da Dan shege.

Wannan kalman ta girgixa kowa musamman iyayenta duk da Dad Omar yayi kokarin Danne fushinsa sbd Ahmed daya bayyanarda nasa sosai da Mummy dinta.

Ta bangaren babbah ma zuwa dare Yana warwarewa haukace musu yayi da kowa gidan fada ne yakeyi sosai akan mummunan cin amana da taadancin da Akai masa Yana zaune da ‘yarsa an sake cutarsa an mata Ciki a karo na biyi bayan an San zaman dagar da yayi na Raba auren sbd matiqar b Jin yayi ance Mam ya rash an rufesa da qasa ba bazai iya bada yarsa a zuriar gidan ba Ashe kallan Mai saman ruwa suke masa,sun cucesa sunci amanarsa.

Ameenatou da Ashley dayace auren dole zai Mata idan Bata fidda miji a satin ba zaune zuke gabansa Suna kuka musamman daya sake tabbatar musu da ita Ameenatou bazata sake fita aikin kowa ba saita haihu ya kaiwa Dr Aleena abinda ya Haifa ita Kuma Ashley ba ja da Baya auren dole zai Mata koma da waye ya samu Kuma ya bada umarnin Maza Maza a dawo masa da Arfat.

Gabaki daya gidan dauke wuta sukai tareda kama kansu sbd ba qaramin zafi babbah ya dauka ba Dan Babu wanda ya ragawa hadasu yayi har Omar din yaci musu mutunci bayan hakuri Babu abinda suke basa sbd tabbas kowa yasan an masa laifi.

Jamaal kuwa damuwansa gabaki daya ta koma ne akan matarsa datake fama da kanta Kuma ana sake sakata tsoro da Kuka gashi ko wayarsa Bata dauka kwata kwata ta Dena yadda kota Yaya ya ganta Dan haka yake Cikin tasa gagarumar damuwar.

Fatmah ma tsananin fushin da uncle Ahmed yakeyi da ita yanke shawaran maidata France karatu yayi babbah na Jin hakan yace ba inda zata a hadasu duka ai musu auren sadaka shine kadai zai daidaitasu.

Take uncle Ahmed ya amince da hakan hakama Dad Omar Dan haka Fatmah na Jin hakan tafara Kuka da birgima tana rokon babbah ya taimakesu sun tuba.

Ashley ma tayi rokon babbah da Neman tuba harta gaji.
#MAMUH

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
146
Mam a ranar daya cika kwana hudu a asibiti Omar ya bada umarnin kawai a miqasa asibitin mahaukata sbd cigaban da Babu ko kadan a tattare dashi sbd duka matakin dayaso dauka ma akansa ganin yanda gaba daya fatar jikinsa yayi Wani mummunan baqi a Cikin kwana hudun sbd balain ruwan alluran da suka shigesa Wanda likitoci sun tabbatarda qwayoyin Cikin ruwan alluran sun Riga sun kama ruwan jikinsa sedai idan zaa fiddasa waje ne.

Ahmed baima bari Omar ko Jamaal sunji wannan sakamakon ba ya sanar da Dad Omar abinda zai sanar Anan ne Omar din yace a miqasa asibitin mahaukata kawai.

Jamaal kuwa baima San meyake faruwa ba sbd ya Riga yabarwa Dad Omar din yaji da komai.

Haka aka nade Mam din da idonsa daya aka kaisa asibitin qazanan mahaukatan Dake wajen gari aka basa daki bayan an cike masa komai.

Yanaji Yana Gani baya iya magana bare motsawa aka ajiyesa da Ido daya tsiyaye aka barsa Cikin dakinda gwara wata bolar dashi sbd tsananin wari da sauro ga Kuma wasu ruwa Dake kwance gefen dakin wainda har sunyi baqi da alama ruwan sama ne ke zubowa idan anyi Suna taruwa aciki.

Ko ficewa Basu gama yiba sauro da quda suka fara yayyabesa daga kwancen dayake.

Sama ya Dan kalla ahankali yaga Babu ko ceiling take wasu hawaye masu radadi da Ciwo suka gangaro gefen Idanuwansa Yana rufe Idanuwansa yanajin wasu irin qwari ja shigewa rigar jikinsa da ko ita Bai samu an sauya masa ba duk jinin daya zubar mata ya bushe yayi Wani irin baqi.

Duhun dakin kadai idan dare yayi wata azabar datake firgita ruhin dan Adam dayake cikinsa ne,

Sanyi jikinsa yayi Yana sake rintse Idanuwansa hawayen cikinsa suka gangaro sbd yasan har abada bazai taba qara moruwaba sbd shi kadai yasan azabar dayake ji a jini da jikinsa.

Dare nayi gurin ya dauki tsit bayan kukan sauron masu yawan gaske dayake tashi a dakin Babu sautin komai,
Wasu azababbun cinnaku ne ke cizonsa Tako Ina azabarsu na ratsashi Amma baya iya ko motsa ko yatsansa bare Wani abin
Ga Wani irin duhun da ko a Lokacin da suke shiga gino zinari a Cikin duhun Rami me zurfi da tsayin gaske Bai Kai wannan ba sbd wancan akwai hasken fitila Amma ayau ko wanda zai kunna masa hasken fitila Babu,

Wannan duhun duhu ne da Yan uwansa Dake kwance kabari Kila sunfisa samun rahamar hasken kabari akan wannan dayake Ciki.

Haka ya kwana Babu sauki ko rahamar ubangiji ko daya har gari ya waye sai guraren 10 aka shigo aka Bude dakinsa Wani qazamin dattajo ne da yake a Buge ya zauna ya tayar dashi zaune ya fara Tura masa abincinda ta ringa dawo masa sbd azabar dayake Ciki ta Fi masa abincin Dadi da saukin wucewa a cikinsa.

Ganin hakan me basa abincin ya Saka hannu ya dame tuwo da miyar kaman kunu ya zuba musu ruwa suka sake sakewa ya maqure bakinsa ya dura masa shi gabaki dayansa a bakinsa ya wuce cikinsa.

Yana fita amai ya fara feso masa har jikinsa har qasa take gurin ya lalace da Wani irin qarni da qazantar Aman Amma Babu wanda yazo ya sake dubasa haka Nan ya wuni Cikin aman tareda ruwan qazanta.

Haka ya wuni sai dare aka sake zuwa basa abinci Nan ma Babu Bata lokaci Aka dura masa ya sake feso Wani Aman Cikin azabar ciwon Ciki Mai tsananin azabar daya sakar masa gudawa.

Anan ne aka zo aka daukesa suka wanke masa jikinsa Shima bayan ya wuni Babu wanda ma yasan halinda yake Ciki bayan wari da qazantar sun ma fara bushewa a jikinsa.

Lokacinda suka zaune dashi a bakin Wani fanfafo Cikin qazanta suka fara sheqa masa ruwa qarnin amai Dana jinin rigarsar daya bushe Dana gudawar suka fara Wani mummunan tashi a jikinsa take suka suka rufe hancinsu Suna sake Dan yin baya daga jikinsa suka sheqa masa ruwa kaman Wani Dabba.

Wani irin kukan baqin Ciki da qunci ne ya taso masa Yana rintse Idanuwansa.

Suna gamawa Wani gajeran wandon dinki suka Saka masa suka kaisa dakin hakanan suka kwantar dashi suka tafiyarsu.

Sanyi ne Me karfin gaske suka fara ratsa fatarsa zuwa namansa har zuwa qashinsa suna ratsasa cikeda azaba da qaiqayi Amma ba halin motsawa.

***A daidai wannan lokacin Omar na tareda Dr Aleena wadda sukai tafiya a safiyar zuwa Abuja shi da ita da Ahmed gurin Wani Taron manyan likitocin da zaayi na qasa Wanda tana Cikin manyan baqin likitoci masu Mahimmanci da aka gayyata sbd shi Omar din daya Saka sunanta sbd ta daukaka a qasarsa kaman yanda takeda daukaka a tata qasar akan aikinta.

A lafiyayyan luxury Bangalore dinsa suka sauka Wanda yake tsare da securities da luxuries Tako Ina hankalinsu kwance.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected