AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

******Su Dad sun dukafa ba ji ba Gani sai barin kudi sukeyi hankali tashe gurin Neman Maryama Dan kuwa suna gap da zubewa gaba Daya Dan haka suka fice hayyacinsu.

BB ma sun haukace Baki ba ganin sunata tsananta bincike da zufafasa akan Maryama wadda daga karshe suka gano kauyensu.

Bayan barin dukiya me yawan gaske su BB Saida suka gano Maryama saigasu da ita har cikin Lagos sedai ko kwana batai a lagos ba Su Mam suka taho har inda su BB suka boyeta da daddare.

Mam ne ya fara tsayuwa akanta kafin Lameenu ya shigo bayan ya kashe wayarsa gabaki Daya daga wayar dayayi ya tsaya Shima yayi mata kallo Daya Yana komawa ya zauna kujeran alfarma dasu BB suka kawo musu na zama.

Shima Mam zama yayi Yana kallan BB batareda Bata lokaci ba Dan baida time na batawan yace

“Tatso mana bayanin komai daga bakinta banason rasa kalma ko Daya komai nakeson Jin a yanda yake dinsa.”

Qwayar datake bakin BB ya qarasa hadiyewa idanuwansa na sake rinewa jajir ya miqawa yaronsa Daya hannu ya Saka masa wata mahaukaciyar wuqa da shape dinta kadai abin tsoro ne.
Nufar Maryama din da idanuwanta suke a daure yayi tareda tsayuwa a kanta ya kamo kanta ya Bude idanuwanta ya Saka mata wuqar gaban idanuwanta da sukasha mugun dauri cikin muryansa me kauri da karajin rashin Imani yace

“Ki kalla Menene a gaban idanunki”

Kafin ma taja numfashin tsoro da tashin hankali bare taga wainda ke zaune a gurin ya mayar mata da daurin idanuwan ya rufe.

Mayar da kaifin wuqar yayi akan jijiyan maqoshin wuyanya Kai tsaye yace

“Meya faru a Daren ranar da matar sir Omar ya ta rasu?
Akwai ciki a jikinta koda ranar tazo?
Wata nawa?
Ta haihu?
Me ya Haifa?
Ina abinda ta Haifa yake?
Waye taredaku a Daren ranar?
Ya Akai kika tsira a Daren????

Cikakken bayani zakiyi sbd rashin kalma Daya daidai take da ficewan ruhinki daga gangar jikinki.”

Wasu Hawaye masu tsananin zafi ne suka gangaro daga idanuwanta dasuke a rufe zuciyarta na wani irin rawar tashin hankali da tsoro Dan kuwa tasan shikenan nata karshen yazo abinda taketa yiwa gudu sbd tasan Hakan zai iya faruwa wata ran sbd akwai tabbacin asan data tsira.

Sake daga wuyanta BB yayi Yana qarawa wuqar seti har seda ta Dan fasa wuyan jini ya Dan fito.

Zufa take fitarwa sosai kirjinta na wani irin mugun bugawar da kusan Suma su mam din kirjin nasu harbawa yakeyi sosai Dan kuwa a Baya duk zance ne sukeyi Basu tabbatarba sai yau din zasu tabbatarda masifar Dake gabansu tana can tana yawo a duniya batareda sunsan a Ina ba.

Lameenu kuwa har wani zufa yake tsiyayowa hannuwansa na rawa Da matsuwan Jin Abinda zata fadan,

Allah yasa Omar din Bai haihuba zance ne kawai,
Allah yasa suji abinda zai kawo karshen matsalar tasu idan ba Hakan ba akwai babbar matsala da kura a gaba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
34
Maryama gaba Daya ta cire tsammani daga rayuwa Dan haka cikin rawar murya da tashin hankalin da Bata taba Shiga ba ta fashe Da kuka zata fara rokonsu karsu kasheta BB ya sakar mata wani mugun marin bayan hannu Saida bakinta ya fashe Da jini sosai ya sake cakumo wuyanta Yana Dora wuqar kafin yace komai Baki na jini tace

“Koda ranar tazo tana daukeda tsohon ciki wata Tara……

Wani mummunan zufa da sarawan Kai tareda bugawan zuciya ne ya saukarwa Lameenu da Mam lokaci Daya,
Lameenu yayi saurin kallan Mam zuciyarsa na wani irin bugawa da karfi da tsalle sbd baitaba tinanin Jin Hakan ba,
Da gasken kenan dai Omar nada magajinsa,
Magajin dukiyar da baimasan Yaya zeyi da ita ba,
Gadon dukiyar tin suna samari suke dakonta cikin ransu,
Dukiyar da suka zama abinda su kansu basuyi tinanin zama ba ko a mafarki Amma daga karshe ace share fage ne kawai sukaiwa abinda Omar ze Haifa.

Mam kasa motsawa yayi bare juyawa ya kalla Lameenu sedai zuciyarsa kusan tafi ta Lameenun shiga mafi girman tashin hankali da firgici.

Shi kansa BB wani irin zufan tashin hankalin ne ya jiqasa Dan haka ya sake danna wuyanta Yana jiran sauran bayanan
Cikin rawar murya da ficewa hayyaci taci gaba da cewa

“Bata rasu ba a Daren sai bayan data haife cikin dayake jikinta,
Sir Omar yasan ta haihu sbd da kansa ma ya karbi abinda ta Haifa,
Oga Ahmed ma yasan ta haihu a daren….”

Kukanta karuwa yayi muryanta ya tsinkewa sbd tsoro numfashinta na Neman daukewa tsaban tashin hankali da tsoron wuqar Dake wuyanta tanajin kaifinta.

Lam da duka jikinsa ke rawa da zufa kasa hakuri yayi cikin zafi da matsuwa yace

“Me ta Haifa a Daren?
Waye Wanda kuke tareda shi a gidan wannan Daren?
Ina abinda aka haifa din yake?
Waye ya tafi dashi?

Wani sabon mari BB ya falla mata cikin rashin tausayi bare Imani Yana cewa

“Koro bayanin amsosin abinda aka tambayeki kafin na ratsa wuqar Nan cikin makoshinki”

Bakinta da duka jikinta na rikicewa da jijjiga Hawaye da majina duk sun cakude a fuskanta cikin matsanancin tsoron rayuwarta tace,

“Banda tabbacin abinda ta Haifa sbd a dare duka muna cikin tsoro da tashin hankali daga sir Omar Se oga Ahmed da ‘yayan Hajiya Ameenatu din ne kadai suka San Menene aka Haifa tsakanin mace ko namiji…
A Daren yayanta yazo daga gombe gurinta Kuma shine ya tafi da babyn”

Wata sabuwar zufa ce ta tsiyayowa kowannensu Dan kuwa abin yazo a yanda basuyi tsammaninsa ba.

Sake danne wuyanta BB yayi tafara jero musu bayanin komai Daya bayan Daya har address din gidan Babbah dake gombe da yanda suka tsare da Kuma yanda Taga girman son dayake wa yar uwarsa da abinda ta Haifa din tabar masa.

Abu dayane ta boye shine cewan tasan mace ce aka Haifa sbd tsaban rufewa da shiga tashin hankali kwata kwata ta manta mema aka Haifa din.

Tana gama fadan kalamanta na karshe Mam ya miqe tsaye Yana ficewa daga dakin zuciyarsa Babu inda Bata tafasa da daukan nauyi.

Lameenu kuwa bayan ya miqe BB ya kalla da idanuwansa tareda yi masa kallan dayasan me yake nufi kafin Shima ya fice Yana Jin ihun Maryama din datai so Daya Bata Kara ba aka rufe bakinta.

Mota suka suka nufa da sauri BB ya qaraso ya budewa Mam driver Kuma ya budewa lameenu suka shiga Kai tsaye aka rufe driver ya shiga da sauri ya tayar da motar BB na musu a sauka lafiya suka bar gurin.

Tinda suka kama hanya Babu me cewa komai sbd kowa da Saka da warwaran da yakeyi a zuciyarsa cikin tinanin Neman mafita data inda zasu fara Neman Dan uwan matar Omar Wanda a yanzu sukeda cikakkiyar tabbacin ‘dan Omar Yana hannunsa.

Lameenu da hankalinsa yafi na Mam tashi sbd yanada labarin project dinsu ba lallai yakai labari ba Dan kuwa komai Baya tafiya yanda akeso,
Idan Mam yaji Hakan abun sake lalacewa zeyi Dan shi Kam ya gaji da Mam Yana sake bawa Haroon Daman shikuma Yana sake rusa su sbd bazai taba zaba me amfanin da sukeso ba Babu amfanin basa damammakin da ake basa,

Shi a nasa son su cire Haroon daga komai nasu Dan baida amfani kawai su bazama Neman magajin Omar Dan kuwa Babu abinda zasuyi yanzu dukiyar ta dawo yanda take koma fiye da yanda suke tsammani bayan su mallaki dukiyarsu ta Omar Dake ransu tin shekara da shekaru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected