AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Location: LAGOS
We deliver nationwide
09013833502
https://chat.whatsapp.com/JRkPEIt0xVj2vuE8HAGRUL
**********
Tin kafin su isa gida a motan siddeeq yafara wayoyi Yana kokarin Hana labarin fita ko kadan Amma ga alama hakan ba lallai ya samu ba sbd Mam ne da kansa ake magana.
Jamaal har lokacin baice komaiba sbd Baya buqatan magana ko hayaniya da Dad din daga isowansa Kuma siddeeq yasan abinda ya kamata Dan haka magana ma sakawa Kai ciwon Kai ne kawai.
Mum dinsa ma daya San batasan tashin hankali ta lafe jikinsa hannunta har lokacin riqe Cikin nasa Ya Dan juyo ya kalleta itama shi ta kalla zatai magana ya katsesa ta hanyar Bude bakinsa a natse da sauti mara qarfi yace
“Its okay,Siddeeq will handle everything”
Gyada masa Kai tayi tana sauke ajiyan zuciya sbd batason ko kadan Jamaal din na shiga hayaniya da Dad dinsa duk da tafi kowa sanin waye Mam din Amma tinda ya Riga ya haifesa ya gama dashi.
Koda suka isa gida securities tini suka wangale gate din gidan motarsa data Dad din kadai suka shige harabar gidan sauran a waje suka tsaya sbd na mansion din Mam ne Dan haka can suka shige kawai.
Suna parking Mum Atee da Ayesha Dake jiran isowansu a gidan tareda masu aikinsu fitowa sukai tarbonsu Cikin farin Cikin dayake ba har zuciya ba sbd sanin waye Aleena a gurin Mam,
Duk da basuda aure matsayin Aleena daban a gurinsa Cikin matan duka duniyar Dan itace ta haifar masa rayuka biyu dayafi so duniya fiyeda tasa rayuwar hakama itace macen dataso shi tsakaninta da Allah har ranta take sonsa.
Daga gefen danta Mum din tasa ta gaisa dasu Mum Atee tana amsawa da thank you a welcome din da ake musu,
Shima Jamaal din Bai saki uwarsa ba har Saida suka isa Ciki yakaita har sama bedroom dinta tukuna y sauko ya koma nasa palon ya haye samansa.
Siddeeq kuwa kayan Mum din ya Saka masu Aiki suka Kai sama har bedroom dinta aka jere mata komai aka sake gyara koin kaman tana Poland dinta sbd duk abinda aka Saka gidan na wanda zaiwa Mum din da Jamaal daidai ne siddeeq yayi wannan aikin sbd a wannan Dan lokacin Shima yayi yawon jirgi kaman tsutsu Dan haka Shima yanzu ya samu nutsuwa tinda zasu zauna guri daya.
Bangaren Jamaal kuwa tini yayi masa gyaran daya San shine daidai raayinsa da rayuwarsa da kansa yayi aikin,
Closet dinsa a cike take da dukkanin kayansa tin daga kan kananu da kaftans, designers kuwa kaman baa San zafin kudin ba Dan kuwa wardrobe dinsa gabaki daya designers ce originals daga kamfani.
Shoes,clips, toiletries, cosmetics da komai na amfaninsa Babu abinda ba designers ce take bugun juna ba.
Shi kansa siddeeq yanzu a gidan zai zauna sbd part dinsa me zaman kansa dayaji wata sabuwar kudin aka Gina da sunasa tareda zuba luxuries Shima abubuwan da sukai masa daidai raayinsa da buqatansa ya zuba hakama wardrobe dinsa Shima duka designers ne Dan Shima a yanzu kudin sun zauna masa iya zaunuwa.
Tsit gidan yayi bayan komawan Dad dasu Mum Atee mansion dinsu ta kofar garden din gidan zuwa nasu garden din daya hade Mansions din.
Hutawa masu gidan keyi Babu wanda ya fito sai dare lokacin masu Aiki tini suka gama shirya dining da koina suka fice zuwa dakinsu.
Siddeeq ne yafara fitowa cin abincin ya nufi dining room din Yana kunna wayarsa dan duba halinda ake Ciki yaga labarin ya Riga ya fita Amma ba sosai ba sbd kokarin da yayi na Hana fitar tasa Dan haka zaiyi wuya ya isa kunnune Dad Omar ko Wani daga Cikin jdens din kafin JAMAAL ya tinkari Dad Omar da kansa.
Mum ce itama ta sauko sanyeda doguwan jallabiya black daya masifan mata kyau sbd farinta tana qamshin English perf me shegen tsada da sanyi itama.
Tana ganin siddeeq ta sauke ajiyan zuciya tana Jin dadin ganinsa ta sake tana sakin murmushi tana qarasa saukowa ya miqa mata hannunsa ta kama ta qarasa saukowa Yana mata sannu Cikin tsananin kulawa da kauna sbd uwa yake jinta kaman yanda takejinsa kaman Haroon dinta data rasa sbd shine ya zama kaman kariya daga kowanne cuta ga ‘yayanta duka biyun,
Tana masa kauna me tsafta da karfi sbd sanin zai iya bada ransa ga ‘danta hakan ya Saka take masa tsaftatacciyar so kaman yanda take kaunar danta Babu qabilanci ko kadan.
Dining room suka nufa Suna magana Shima Yana dariyar abinda take fada masa din.
Suna zama Mum din ce tafara juyawa sbd qamshin Paco Rabanne daya shiga hancinta tasan JAMAAL dinne ya shigo.
Shi dinne sanyeda Off-white Nikes gashin kansa me santsi a kwance hakama na fuskansa a kwance kwance yayi duhu sbd farinda yakeda dashi sosai.
Qarasowa yayi Yana sakarwa Mum dinsa nitsatsen murmushi me sanyi da nutsuwa ya rankwafo ya Dora bakinsa a hankali gefen goshinta ya Bata kiss Yana zaunawa kujera kafin ya Kalli siddeeq Dake son tsokanarsa da kallan dayake masa akan maganar dazun ta Yan jaridan.
Wani kallo ya watsa masa Yana cewa
“Karka fara,
Nasan Kuma zancen dole zai iya kunnen Dad Omar so gobe Mum acan zamuyi dinner tareda su zanyi magana da Dad Omar din”
“Hakan ya kamata kayi magana dashi kafin Dad Dinka ya Riga Omar bazaiji Dadin hakan ba,hakama itama AM din zancen zaije mata a Wani irin sbd Abu ne da batai tinani ba Kuma jinsa daga sama baiyiba.”
Siddeeq ma Naam yayi da hakan Dan haka suka fara cin abincinsu Cikin nutsuwa,
Siddeeq Tuna fried rice yaci da Salad din Nikakken nama,
Jamaal da Mum kuwa chicken vegetable Farfalle sukaci dataji cheese Suna gamawa Jamaal fita yayi tareda siddeeq zuwa Wani gurin da suke sakaran samun Wani labarin inda zaa iya samun Ashley.
Basu dawo gidan ba sai dare Dan haka kowa shigewa yayi.
Samansa ya haye ya wuce bedroom dinsa Kai tsaye yayo wanka ya Saka silk pyjamas ya kwanta bayan yaje ya duba Mum dinsa tayi bacci tini.
Washe gare sai Rana suka fito breakfast Suna gamawa siddeeq ya dawo bakin aiki
Masu aikin gidan kaf dinsu ya sallama bayan ya Basu albashin wata daya duk da aikin kwana biyu xuwa uku kawai sukai Amma Sam bazai iya barinsu ba sbd ba shine ya daukosu aikin da kansa ba daga bangaren Mum Atee suka fito.
Suna barin gidan kafin yamma ya kawo wasu da suka Fi waincan din kwarewa da ingancin kamfanin daya daukosu din Dan haka take suka fara Aiki bayan sungama sauraron dakokin yanda masu gidan suke musamman me gidan da kansa da bayason hayaniya.
Tareda Dad dinsa sukai lunch din Rana a mansion dinsa sbd Mum dinsa data sakasa hakan daga Nan suka shiga Mum dinsa ta duba daddy lameenu dayake gida kwance hakama mum Sarah.
Suna fitowa mum din ta wuce gida shikuma ya sake fita tareda siddeeq.
Da daddare ansan da zuwansu cin abincin daren a jdens Dan haka aka shirya table da wadatatten abincin kala kala masu kyau da lafiya da kyan Gani sbd komai kana Gani kasan cooks din kwarai ne a gidan.
Tareda Dad dinsa zasu tafi sbd family dinner akace hakama Kai tsaye ya sanar da tareda shi din zasu tafi sbd Shima Yan buqatan zuwa ganin Dan uwansa da yimasa barka da zuwa an Dade baa hadu ba lokacin haduwan yazo Dan haka a mota biyu tsaf suka shirya suka nufi gidan jdens din.
Mam din da mum Atee ne a mota daya sai Jamaal din da Mum dinsa da Siddeeq a daya Ayesha bata biyosu ba sbd Batama gida Amma daga can zata wuce jdens din.
Mam Bai fito ba Saida ya biya ya duba lameenu Kuma ya sanar dashi inda zashi,
Lameenu na kallo Mam din ya wuce zuciyarsa na Wani irin radadin daya rasa yanda zaiyi ya motsa bare iya tashi akan kafafunsa,