AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Kafin ta cire hannunta Akai Ameenatou ta Dora hannunta akan na Dadah din tana cewa
“Babyn Ameenatou inji Ashley,
Ashley tace Babyn Ameenatou kada kowa ya tabasa…….
Yanke jiki Dadah tayi a bakin toilet din tsakar gidan ta zube qasa zaune jikinta na wata irin rawa sosai zuciyarta na tsananin bugun datake Neman bugawa.
Bakin na rawa tace
“Me kikace?
Zaunawa a kujeran wankanta tayi tana cewa
“Ashley tace baby ne anan Kuma babyn Ameenatou ne”
Hannu Dadah ta Dora Akai tanason fasa ihun tashin hankali Amma Kuma batasan ma me zata fada a cikin ihun ba.
Babbah Baya gidan hakama Hafiz bare a taimaketa da radadin dayake Neman illata ganinta da Jinta,
Rarrafawa tayi ta dafa ta tashi sbd kasa yadda dataji tanayi da wannan mugun fata da mafarkin.
Hannuwanta na rawa jikinta Babu karfi ko kadan ta danne abinda take ji Akai wankan tana kasa kallan cikin Dan tsoro ma takeji fatanta zancen rashin hankalin Ameenatou dinne kawai take maganar baby a cikinta duk da girman cikin ma ga fada Hakan Amma bazata iya yadda cikin mutum na haihuwa ne a jikin ‘yar yarinyarsu ba da batama cikin hankalin kanta.
Kwata kwata ba nutsuwa ko Kwanciyar hankali ko Daya a tareda dadah suka fito ta shiryata cikin doguwar rigar material da Hafiz ya siyo mata su a kayan sawa tinda batada wasu kayan a tareda su.
Duk yanda taso dafa abincin Rana kasawa Dadah tayi sbd zazzabi ne na tashin hankali ya rufeta take,
Tea kawai ta hadawa Ameenatou din ta Bata tana sake zurfafa a tinanin abubuwa da dama da Suka sauya daga Ameenatou din Daya kamata ace sun gane Amma sbd ganin rayuwarta ma ta sauya gaba Daya ya Sakasu daukan duka akan kanta ne Daya juya.
Karfe Hudu na yamma Babbah ya dawo gidan dauke da ledan fruits Daya siyo a hanyarsa ta dawowa daga inda ya samu Yana Dan shiga kasuwancin dabbobin Daya Saba.
Zazzabin Daya tarar da Dadah ya Sakasa mamaki Yana zaunawa yace
“To lafiya dai kuwa?
Meya sameki ne tinda lafiya kalau muka fita muka barki kina aikin gidan,
Ko cizon sauro ne? To Amma Kuma ai bamada Wani sauro tinda Akai akai anawa gidan feshi sbd yar buduwata da banason sauro ya ciza”
Ajiyan zuciya ta sauke idanuwanta sai a lokacin suka cika da wasu hawaye masu tsananin radadi da ciwo ta dago ta Kalli Ameenatoun Dake kwance tana bacci ita Kuma tanai mata fita.
Ajiyan zuciya ta sake saukewa a Karo na uku kafin ta dago ta Kalli Babbah Daya zuba mata ido Yana jiran abinda zata fada Dan bayason delay a gurin Bada labari ko Fadar Abu.
Sanyi jikinta yayi hakama muryanta tace
“Babbah Ameenatou ciki ne a jikinta ga dukkanin alama Dan ni dai na kasa tabbatarwa a rude nake Kuma itama da kanta tace baby a cikin Ameenatou…..”
Kallan Ameenatou din yayi kafin ya juyo da kallansa kan Dadah yace
“Meyasa haryanxu kin kasa sabawa da yanayin tashin lafiyanta,
Kinsan yanzu batasan me take fada ba batasan Menene wannan ba bare wancan.”
Girgiza Kai dadah tayi idanuwanta na sake cikowa da Hawayen da suka gangaro mata tace
“Ciki Kam akwaisa da alama Dan gashinan a bayyane harya fito Dan kuwa da alama zaiyi wata hudu komai fiye,
Kullum saitace cikin Ameenatou tsalle sosai na dauka idan tana Jin yunwa take Fadar Hakan shiyasa duk ta fada saina Bata Wani abin taci da alama Motsi ne yake mata…….
Ajiye kankanar Daya dauka zai Sha Babbah yayi Yana sake kallan Ameenatou din dakyau ya dawo da kallansa kan Dadah idanuwansa na sauyawa yace
“Wai maganar me kikeyi??
Cikin haihuwa ko me??
Gyada Kai tayi hawayenta na sake gangarowa.
“Ni bangansa ba to” ya fada muryansa na sarqewa.
“Nima wlh bantaba Gani ba sai yau Amma wlh Babbah naga ciki me girma Kam ni Amma na kasa yadda da cikin mutum ne a jikinta,
Nidai muje asibiti a duba mana Dan jinina Neman Hawa yakeyi da wannan babban tashin hankalin dayafi kowanne dayake Shirin bayyanar mana”
Wani azababben zufan tashin hankali ne ya fesowa Babbah lokaci Daya a ko Ina jikinsa,
Hannunsa dayake Dan rawa yakai goshinsa ya share tareda qurawa Ameenatou idanuwansa dasuka qarasa sauyawa gaba Daya suna yin wani Jan tashin hankali da masifa.
Kaman tasan abinda ake ciki ta juya Kwanciyarta ahankali zuwa Dayan bangaren Wanda Hakan ya bayyanarda cikin sosai take Babbah ya sarqe da yawun bakinsa da suka kasa wucewa sbd muguwar bushewan da maqoshinsa yayi take.
“Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Innalillahi wainna ilaihirrajiun,
Badai ciki ba wannan sedai koshi ne yayi mata yawa Amma tayaya zaa samu ciki a jikin yarinyar datake budurwa Babu miji,Babu hankali Kuma tana can killace asibitin da baama barin kowa shiga sai dole.
Wurgi yayi da kayan gabansa Yana miqewa tsaye jikinsa na sake jiqewa da zufa ya Saka takarmansa Yana cewa
“Shiryo asibiti zamu yanzu basai gobe ba”
Miqewa dadah tayi tareda shiga daki ta shirya ta fito ta dauko hijab ta tayarda Ameenatou ta Saka mata suna kokarin fitowa Hafiz ya dawo ya tsaya Yana kallansu cikin mamaki Amma Kuma ganin Babbah a mummunan halinda Bai taba ganinsa ba a ciki ya Sakasa Maida kallansa kan Dadah da jikinta yake a mace gaba Daya Babu kuzarin komai,
Ameenatou ya kalla itama yaga ita baccinta ne ma Bai isheta ba fuskanta duk a daure sedai itama a kasalance take.
Magana zaiyi Babbah ya dakatar dashi ta hanyar cewa suje kawai.
Ciki ya shiga ya ajiye ledan siyayyar kayan tea da wasu abubuwan Daya siyo ya fito ya rufe gidan ya biyo bayansu zucuyarsa Shima tini tayi nauyi ta shiga Wani mummunan damuwa Yana fatan ba wani abin ne ya samu Ameenatou dinba Dan zuciyarsa bazata iya dauka ba Dan yanzu haka duka nemansa akanta ne sbd ita yakeson yaga sun samu sauyin rayuwa itada iyayensu.
Mota Babbah ya tsayar ko Gani sosai bayayi sbd yanda zuciyarsa ke bugawa da hawan jinin Daya kamasa take Amma bazai iya tsayawa ba idan ba asibitin suka Isa ba likita ya kallesa ya fada masa gaskia duk da yasan gaskiyar zata iya illata rayuwansu gabaki dayansu Dan Ameenatou itace hasken zuciya idanuwansu da illa Daya gareta tamkar radadin mutuwa ne garesu.
Shiga motar sukai Hafiz na gaba ya kasa tambayar komai sbd fargaban abinda zaa iya fada masa duk da Bai taba kawo tinanin ciki ba sbd abune da yama manta da cewan ita macece ma gaba Daya.
Suna Isa asibitin Hafiz ya sake shiga rikitaccen tinanin ko Wani ciwon ne ya kama Ameenatou Dan haka ya matso da sauri ya kama hannunta Yana kallan fuskanta zaiyi magana Babbah ya silale qasa ya zauna Yana cewa Hafiz yayi komai likita zasu Gani yanzu yanzu.
Jin Hakan ya saki hannunta nauyin zuciyarsa na qaruwa ya Isa inda ake yanka Kati ya biya komai take aka Basu Kati sbd Babu layi Kuma asibitin private ne Dan haka duka abinda ya samo haka ya tattarasu Akai komai akace a shigo da ita.
Dukkaninsu suka shiga dakin ganin likitan.
Kallansu Dr yayi da mamakin ganin su dukan yace su fita ita kadai zasu bari.
Hafiz ne ya samu karfin yi masa bayanin matsalarta ta Rashin hankalin.
Hakan ya Saka Dr din Dan kallansu yace to yanzu Menene matsalanta.
Kallan Babbah Dadah tayi kafin ta Kalli Ameenatou din
Shi Kuma Hafiz su babban ya kalla Yana jiran Jin Abinda ya kawosu.
#MAMUH
*_ZAFAFA BIYAR_*
1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_
2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_
3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_
4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_