AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Wani numfashi da sanyi ne ya saukarwa Ashley lokaci daya Dan haka ta rungume Ameeenatou ta fasa kukan data dibi shekaru tana Adana Ciwo aranta batai Kuka ba sbd ko Babynta data rasa batai kuka ba sbd batada wanda zataiwa kukan,
Tsawon shekarun Nan duk qunci da baqin Cikin rayuwar datake Ciki Bata taba zaunawa tayi Kuka ba sbd batada kowa da zai rarrasheta Dan haka zafin da ciwon ya maqale mata arai sai yanzu taji duka nauyin Yana sauka data ga Ameeenatou ta rungumeta da qarfi tana sake fidda sautin kukanta.

Shiru Ameeenatou tayi tareda bawa Ashley daman kukan yanda take so tsawon lokaci kafin ta saketa ta dago jajayen Idanuwanta ta kalleta kafin ta Bude bakinta tafara tambayarta lafiyanta da yanda take.

Cikin kulawa da sanyi ta amsa itama ta tambayeta yanda take.

Murmushi me sanyi Ashley tayi tana kallan nutsuwa da Class din da Ameeenatou din take tattare dashi ta sake sake murmushi tana Tina baby Ameeenatou dinta a Lokacin asibitin.

Hafiz da Shima sai alokacin ta juyo suka gaisa ya gabatar mata da kansa
Cikin kulawa ta amsa masa tareda tambayarsa babbah sbd ta fahimci shi ‘dan babbah ne.

Da mamaki suka kalleta ta sake murmushi tana cewa

“Yes na San babbah sbd shi Bai fita a bakinta ba ai ko a wancan lokacin shine da Haroon a bakinta kafin Jamaal yazo ya shiga harya koma shi kadai ne take ambatar.”

Da Wani Sabon mamakin suka sake kallanta kafin Ameeenatou ta share hawayenta tana son tambayarta tasan tanada Ciki Koda tabarta asibitin Amma Kuma ta kasa hakan sbd batasan tayaya zata fara tambayar waye yayi mata Ciki ba.

Hafiz daya fahimci hakan hakama ga dare yanayi Kuma dole ayau zasu koma Lagos saiya gyara zama Kai tsaye ya Kalli sister Ashley data kawo musu ruwan pure water masu sanyi ta ajiye gefen Ameeenatou tanajin kaman zata hadiyeta sbd kauna ta zauna yafara jero mata bayanin Asalin rayuwarsu da komai da komai da ake Ciki har zuwa yau din da suka taho gurinta.

Shiru tayi tana sake shiga tashin hankalin da mamakin masifun da aka jero a Cikin tarihin komai.

Numfashi ta sauke tana sake jinjinawa Dad Omar da tausayinsa harma da girmamawa sedai Kuma Jamaal ma ko acikin zancen shine jaruminta Kuma zaici gaba da zama zataci gaba da zama yar amanarsa har abada Dan haka Bata ce komai ba dakinta ta shiga ta dauko tsohuwar laptop dinta da duk ta goge ta kunna ta nemo folder guda data boye wadda Babu abinda yake Cikinta sai hotina da videos din da suka shafi Ameeenatou Tin daga wainda take mata ita daya tana aikawa siddeeq tin kafin Jamaal ya taho har zuwa inda Jamaal ya taho rayuwarta ta sauya gaba daya ta koma cikakkiyar mutum Da wainda take mata idan Suna gyara Kai Bata yadda dana rigimar datake wa Jamaal harma da inda yake fama da ita gurin cin Wani abin idan ba tea ba.

Tinda suka fara kallan abubuwan Ashley ke dorawa da bayanan da sukafi na wainda suke kalla tashin hankali da mamaki tareda tsananin shock na jin hadda irinsu wanki Jamaal din da kansa yasha Yi mata da Kuma illata rayuwar Wani akanta kafin ta dire da baby a date na ranar da Jamaal yafara kwanciya da ita amtsayin mace tareda Bata tabbacin itace takaisa ga hakan tareda karfin son dayake mata hakama kaman yanda siddeeq ya sanar da ita kafin tafiyansu JAMAAL ne wanda tafara Gani rayuwarta ba Haroon ba,sannan ta rufe zancen da cewa

“Dr JAMAAL SEELAH shine uba Kuma mahaifin duk abinda kika Haifa sbd da cikinsa ne a jikinki kika bar asibitin Dan haka babynki bana kowa bane na mijin da shi kadaine igiyoyin aurensa suke kanki”

Kasa motsawa Ameeenatou tayi bare iya magana sbd numfashinta daya toshe Dan nauyin da kirjinta yayi me tsananin gaske.

Hafiz da jikinsa yayi mugun mutuwane yayi saurin riqota sbd jikinta dayake Dan rawa Bata ita numfashi da kyau.

Ashley ma da sauri tayi saurin tarota Suna Kiran sunanta a tare Cikin damuwa da tashin hankali.

Hafiz ne yayi saurin cewa suyi asibiti kawai.

Itama Ashley Naam tayi da hakan Dan haka suka fito da ita Hafiz ne dauke da ita ya Saka motar Ashley ta shiga suna kokarin shiga yace Ashley ta dauko abubuwan buqatanta Dan Lagos zai wuce direct baya buqatan asibitin Nan.

Handbag dinta kawai ta dauko tareda cheques din Dad Omar sbd ayau da akaga motocin da suka kawo mata ziyara Wani bayan Wani ko tana gidan sai barayi sun shigo mata bare anga ta fita.

Hafiz kuwa Cikin Wani irin speed ya kamo hanyar Lagos dasu har lokacin numfashin Ameeenatou daqyar yake fita Ashley na tarairayarta da Bata taimakon gaggawa.

Koda suka isa Lagos tayi laushi sosai ko hannunta Bata iya dagawa Dan haka Kai tsaye asibiti ya nufa da ita tareda daga wayarsa ya kira Dad Omar wanda yanajin hakan Bai sanar da kowaba daga shi sai Ahmed suka nufi asibitin gashi dare yayi sosai.

Suna isa suka tararta Ashley asibitin take Dad Omar da uncle Ahmed suka shiga tashin hankali sedai Ameeenatou dataqi sakin hannun Ashley ya hanasu magana da ita dole suka bar maganar sukaita lafiyan Ameeenatou din wadda da gasken gaske shock ne yakusan Bata attack.

Ashley da Hafiz da su Dad din Babu me magana sai gumi suke hadawa kowa Cikin tsananin fargaba har kusan asuba tukuna ta dawo daidai sedai abinda tafara buqata shine Ashley.

Suna shigowa kallan Dad dinta tayi a hankali Cikin kasala bayan ta riqe hannun Ashley Cikin nata ta Bude Baki ba qarfi jikinta tace

“Dad wannan itace Ashley din Ameeenatou,
Itace wadda tasan JAMAAL SEELAH ne mahaifin ARFAT….” sai a Lokacin ta fashe da wani irin Kuka Mai ratsa zuciya da sanyi tana kasa qarasawa.

Shiru duka dakin sukai Dad dinta Yana rintse Idanuwansa da sukai jajir sbd Bai dauka lamarin zai saurin cabewa da wuri ba duk da baima kawo tinanin Ameeenatou tasan uban danta ba Jamaal kadai yayiwa Ashley gargadi Akai.

Cikin Kuka me tsananin ratsa zuciya Ameeenatou ta fadawa Dad irin rayuwar datai tana Jin radadi a zuciyarta.

Ganin munin halinda take Ciki ya Saka Dad dinta zaunawa kusa da ita ya Bude hannuwansa ta fada jikinsa ya rungumeta Yana Bata tabbacin komai ya wuce Kuma suna Nan akan bakansu sanin uban Arfat ba Yana nufin basa kowacce irin Dama ba duk da Shima zuciyarsa ta girgixa da rayuwar da Jamaal yayi da Ameeenatou din ya jingine komai na rayuwarsa ya koma Yana Aiki a karkashin wasu sbd Bata kariya kawai Amma Yana buqatan gama hada shirinsa na Kai Mam qasa kafin ya bawa Jamaal Dama.

Ashley ta kalla tareda kallan Dad dinta ta sanar dashi bazata iya rabuwa da Ashely ba duk inda take Ashley na tareda ita daman alkwarine yayi mata idan Taga Ashley zasu inganta rayuwarta kaman jininsu.

Kallan Dad Omar Ahmed yayi Shikuma baida abin fada bayan sauya shirinsu zuwa na ajiye Ashley a tareda su Dan hana komai fita.

Anan asibitin suka rufe zancen Babu wanda zaisan zancen a family bayan iya su Dad ya kashe zancen kwata kwata kaman yanda ya aminta Ashley ta zama daya daga cikinsu.

Ameeenatou da zuciyarta take a nauyaye da abubuwa da yawa kasa walwala tayi hakanan suka tattaro da safe suka dawo gida bayan anyi discharging nata.

Hannunta na Cikin na Ashley ta kamota Dan itace da kanta zata shigar da ita familyn jadens ta zama tasu Babu abinda zai sake rabata da Ashley kaman yanda sukai wannan alkwarin.

Hakama zancensu sun kashesa acan ko gidan Basu shigo dashi ba anbar maganar waye uban Arfat rayuwarsu zasuyi kawai sedai Kuma zuciyarta ta shiga tsaka me wuya San tinaninta dayake rarrabuwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected