AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Fasa kaiwa din tayi tana tsaye ya Saka pins na kofan ya Bude ya shige tareda rufewa batareda yasan Ameenatou din tana cikin ba.

Juyawa tayi ta koma dakinsu tana nade Rigan hannunta zuciyanta cikeda tinanin abubuwan da suka faru din Wanda kwata kwata Babu Wanda ya samu Daman magana ko tantancewa take Dr JEEY ya lalata rayuwan Fahat din cikin qanqanin lokacinda Babu Wanda yayi tinanin Fahat dayazo aiki ya koma gida da safe kafin safen ya koma patient dinsu.

****Dr Dee a Daren tin bayan ishai ya fita da takardansa ta sauyin gurin aikin harma da takardunsa da lameenu ya sanar dashi yayi magana zaa mayar masa da matsayinsa dan haka karfe goma yaje yaga wanda zaiyi aikin a gidansa dan kai masa koman dare sbd a daren zaa sauya da safe ya koma office dinsa.

Hakan ya Saka Dr Dee tin ishai Daya fita yanata Kiran BB Wanda Alh Lameenu yace shi zasu tafi tare sbd asan shine din ya Aiko.

BB Bai dauki wayar Dr Dee din ba sai kusan qarfe goman dare cikin tsananin girmamawa da bayyanarda rashin jin dadinsa yafara cewa

“Dan Allah Dr kayi hakuri wlh wayar a silent take Kuma matata ce take Labor tin magrib muna asibiti shiyasa duk ban luraba kasan yanayin dai me iyali,Dan Allah kayi hakuri.”

Cikin sanyin jiki da janye rashin Jin dadin da yayi tinda dai ya samu BB din ya kira Dan haka ya sake Yana cewa

“Haba haba ba komai ai tinda uzuri ne Kuma uzurinma irin wannan babba,
I hope she’s ok now?
Ta sauka Kuma??

“No tukuna dai Amma ba damuwa Ina asibitin ganinan zan hawo taxi na sameka saimu tafi motana ta tsaya dazu….

No bari kawai na biyo na daukeka mu tafi din sbd dare Yariga yayi gashi idan bamu samu ganinsa yanzu ba ganinsa gobe da safe ko Wani lokacin zaiyi wuya so muyi Savin time muje kafin dare ya sake yin sosai just send the location I will be there in no time”

Take BB ya tura masa Yana kallan yaransa Bullet Dake gefensa Yana zuqan wata fitinanniyar cocaine Dake shiga cikin tsakiyan kwakwalwan kansa tana basa wani irin cajin da ba dr Dee ba ko ubansa aka ajiye masa a gabansa zai iya illatasa dan kansa tini ya juye kaman baida cikakken hankali haka yake.

Baayi mintina arbain ba Dr Dee din ya kira BB ya sanar dashi gashi a anguwan Amma Bai gane asibitin ba gashi Babu mutane sosai bare yayi tambaya.

Parking yayi inda BB yace ya jirasa Yana duba time fuskansa a hade sbd kwata kwata komai Baya tafiya yanda yakeso din Dan kuwa kwata kwata Baya Wani fitan dare Dan girmansa da mutuncinsa harma da ayyukan gabansa dasuke da yawa da mahimmanci Dan idan ba wannan huldan Daya Saka kansa ba da yanzu Yana cikin matsayinsa hankali kwance.

BB na fitowa Kai tsaye motan Dr Dee din ya nufa Yana Saka hannunsa aljihun wandonsa ya tura wayarsa.

Yana isowa fuskansa a sake Yanawa Dr Dee din barka da zuwa ya tsaya gefensa batareda ya zagayo ya shiga ba.

Sauke glass din motan Dr Dee yayi zaiyi magana
bakinsa na budewa BB ya danna masa wasu matsiyatan kwayoyi a cikin bakin tareda danne bakin yaqi saki Saida suka wuce maqoshinsa suka Isa cikinsa.

Bullet ne ya iso da wata shegiyar alluran me karfi irin wadda akaiwa Haroon harma Mil din tasa yafi yawa Babu Imani ko kadan BB ya danne wuyansa bullet ya soka masa ita tareda matse masa ruwanta gabaki Daya.

Wani irin Shure shure yafara da karfi Yana jijjigan data Saka har motan jijjigan tashin hankali da azabar da bata fasaltuwa.

Dannesa BB yayi sbd yanda yake shurawa Yana jijjigan ga wani irin jini Daya fara fitowa da hancinsa da kunnuwansa da bakinsa.

Shikam tsananin masifar alluran Bata Dade a jikinsa ba ransa ya fice a take Dan haka BB ya sakesa bayan ya tabbatarda ya mutu din.

Bullet ne ya motso bayan BB ya matsa ya basa guri.

Tissue ya Saka yafara goge gurare da fuskan Dr Dee kafin ya Ciro wasu qwayoyin cikin ledansu guda biyu ya Saka Daya aljihun wandon Dr Dee din Dayan Kuma a karkashin hannunsa kafin ya zagaya ya Bude motan ya dauko jakar takardun Dr Dee din ya Ciro takardansa ta aikin ya ajiye kan jikinsa.

Wayarsa ya dauko ya miqawa BB ya goge kiran da yayi masa da numbernsa gaba tareda ta daddy lameenu da duk abinda dazai nuna sun taba wata muamalan dashi suka mayar da wayarsa gefensa.

Suna gama komai bullet ya Saka gloves ya fara goge koina ya cire thprint dinsu suka juya suka bar gurin.

Ta inda suka fito Wani lungu ne can suka koma suka bi ta Wani kangon gida suka bulla Dayan layin suka nufi titi inda motansu take suka wuce daidai lokacin siddeeq Shima ya hau titin ya fito daga gurin duba umman fadila.

Motan ya zubawa ido Daya tabbatarda ta BB ce,
Titin da suka fito ya zubawa idanuwansa kafin ya sake kallan bayan motan tukuna ya qarawa motansa gudu yayi overtaking nasu ya wuce Yana kallan motar ya tabbatarda BB dinne ya Gani Amma Basu lura dashi ba Shima Bai bari suka ganesa dinba yayi gaba ya wuce da gudu zuwa inda zashi na Shirin aikin JEEY na Daren.

***Dr JEEY na shiga office din Kai tsaye rigarsa yafara zarewa yana nufan bedroom kai tsaye dan sakarwa kansa ruwa dan wuta ce kadai ke ci tako ina jikinsa tana tafasa zuciyarsa shiyasa bai lura da ita ba ya wuce ciki din.

Toilet ya fada ya sakarwa kansa ruwan Yana rintse idanuwansa Dake jajir.
#MAMUH#
#JEEY SEELAH
#AMEENATOU JDEN SEELAH

 

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
73
Ya jima a toilet din kafin ya fito daure da towel me karfi da tsayi sosai Wanda Hakan ya Saka ya kasa dauresa ma daidai a qugunsa yayi masa wani daurin da kowanne lokaci zai iya zamewa ya fadi ya barsa.

Goge jikinsa yayi idanuwansa har lokacin Basu dawo daidai ba sbd zuciyarsa Dake zafi har lokacin.

Yana gama goge jikinsa Bai shafa komai ba bayan body splash kadan ya Saka underwear black da dogon Fendi trousers ya dauko Riga kenan zai saka ahankali yaji hannuwa masu sanyi sun zagayosa zuwa cikinsa Dake bayyane ba Riga..

Da sauri ya riqe hannuwan da hannunsa Daya tareda fizgowa gabansa da zafin gaske da wani irin karfin Daya Sakata Jin azaba me karfi a hannunta hakama fizgan ya sata mugun firgitana datai gefe zata Fadi Kuma mirror ne a gurin Dan haka ba shiri ya sake kamota da hannuwansa biyu ya dawo da ita jikinsa Wanda ya bawa fatan jikinsu haduwa shi Babu kaya itama Babu bayan halfvest dinta.

Cikin tsoro da firgita ta qanqamesa ahankali sbd yanda ya fizgota da Kuma yanda Bata gama dawowa daidai ba daga abinda ya faru a daren hakama batada karfin jikinta ko kadan Dan haka ta sake shigewa jikinsa ahankali tana zagayosa Dan hannuwanta da sukai sanyi sosai Dan sanyin ne ya tadata.

Hannuwansa biyu ya Saka a kafadunta zai cirota daga jikinsa sbd zafin jiki dayaji Yana kamansa na haduwan jikinsa da nata din abinda Bai taba samunsa ba waton haduwan Asalin fatansa data Wani bama ta hannuwa ba ta jikinsa.

Yana Dora hannuwansa a jikinta tasan cireta zaiyi ya rabata dashi Dan haka ta girgiza Kai ahankali sedai Bai tsaya duba Hakan ba ya dagota ta kwace jikinta tareda komawa da karfi tsakiyan kirjinsa,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected