AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Ruwa Jamaal din ya buqata da E-Bull energy drink dinsa.
Daukowa siddeeq yayi ya kawo masa ya ajiye a gefe hakama already tarin manyan takardun abinda zasuyi suna gurin zube.
Kafin ya fara aikin bayan ya zauna dago fararen idanuwansa yayi ya Kalli siddeeq ya Bude Baki a natse yace
“Zamu bi morning flight zuwa Lagos ka duba mana idan akwai”
Dagowa siddeeq yayi ya Kalli JAMAAL din cikin mamakin ta yanda zasu fuskanci juna da Dad dinsa batareda ya gane shi bane,
Hakama shi kansa Jamaal bazai iya kwantar musu da Kai ba komai tsanani kaman yanda Haroon kansa bayama dagowa a gabansu saita Baci.
Cikin nutsuwa da tinani siddeeq ya sake kallansa Yana cewa
“Dr ko zan kira Dad din na sanar masa wani uzurin dazai daga tafiyar gobe zuwa jibi idan Barr da Mum din sun iso”
Girgiza Kai yayi a natse Yana cewa
“Ba buqatan Hakan,zangansa da kaina”
Sake shiga fargaba Siddeeq yayi duk da yasan idan Jamaal din ya fada ta zauna Amma a gaban Dad Kam Abu ne me wuyan gaske idan baa take zai sheda Jamaal ne gabansa ba ba Haroon dinba ko daga kamshinsa da Baya boyewa kowa da Kuma fatansa data banbanta data Haroon duk da idan suna rarrabe baka ganesu Se Wanda yayi da gaske gaske idanma kayi musu farin sani kenan hakama izzar Jamaal har abada ba Daya take data Haroon dinba.,
Tayaya Jamaal zai iya tsayuwa a gaban Dad dinsa batareda yayi masa kallan dazai Saka Dad din take Ji ajikinsa Jamaal ne.
Jamaal Daya miqa hannunsa a natse ya dauki drink din gefensa ya Bude yakai bakinsa yasha kusan Rabi ajiyewa yayi Yana Bude laptop din Dake gabansa ya kunna kafin ya fara janyo takardun Yana budewa tareda jerawa a gabansa sbd acikin kankanin lokacinda bazai ci masa time din komawa rayuwarsa ba yakeson kammala dukkanin aikin project din sabo da zaiwa Dan uwansa ya tattara ya koma bama tareda wani yasan ya shigo qasar ya fice ba.
Shima siddeeq tattara hankalinsa yayi sbd nutsuwa ga aikin da Jamaal zasuyi.
Nutsuwa yayi sosai Yana aikin cikin kwarewa da tabbatarda komai ya tafi daidai,Shima siddeeq mayarda hankali yana Wanda zaiyi a cikin aikin.
Har kusan hudu saura na guraren asuba suna aikin kafin suka ajiye suka nufi dakunansu.
Jamaal na shiga bedroom dinsa Kai tsaye toilet ya nufa yayo alwala ya fito ya Dora gatuwar jacket akan kayan jikinsa na bacci ya rufe batiran rigarsa Dake Bude ya Saka qaramar hulan sallah fara akansa ya tayarda sallan nafila.
Yana gama sallolin nafilansa ya miqe Dan sallahn asuba da Akai kira har ana kokarin tayarwa daga masallatan nesa Dayake jiyowa.
Bayan gama adhkar da adduoinsa miqewa yayi ya cire hulan da jacket din ya nufi gadonsa ya haye tareda kashe komai tin daga kan wayoyinsu da wutan dakin ya shige bargo a nitse Yana lumshe idanuwansa.
Bacci sosai yayi ya samu hutun jikinsa Dana kansa harma Dana zuciya kafin ya tashi guraren 10 da wani abu.
Toilet ya nufa Kai tsaye yayi brush da sauransu tukuna yayo wanka ya fito daure da towel ya nufi inda wayoyinsa suke ya miqa hannu ya kunnasu kafin ya wuce gaban mirror Dan shiryawa.
Bai wani dauki time ba ya shirya ya fito cikin Ash kaftan din Tsadaddiyar yadin cashmere data tsananin sake sauya kamanninsa zuwa wani bakon baturen bahaushe hakama hulan Daya Saka ya rufe gashinsa Daya sake banbantasa Dana Haroon ta qara masa kyau sosai.
A Karan farko rayuwarsa dayayi amfani da wani turaren daba nasa ba Dan haka yakejin Baya wani Jin dadin iskan Daya bayarwa a jikinsa duk da Wanda yayi amfanin dashi Shima mugun designer ne sedai qamshinsa Daya Saba dashi daban yake a gurinsa.
Siddeeq da tini yayi musu booking tickets din 12 Dan haka Shima ya shirya tsaf cikin kaftans din Shima sai Jakar takardun aikinsu Dan laptop din dasuke hannunsa.
Jamaal na saukowa cikin girmamawa ya masa barka da saukowa kafin ya biyosa suka fito tare Jamaal din suna magana.
Siddeeq ne me tuqin Dan Jamaal Kam bayajin zaiyi tuqi harya gama ya tafiyarsa inda ya fito.
Kai tsaye office din dazai fara gabatar da aikin anan Abuja ya nufa ya zauna dasu ya gabatar musu da sauyin aikin dayayi tareda sababbin plans din dasuka matiqar Basu mamaki da sakasu farin ciki me tsananin gaske Dan kuwa tini suka fara Shirin gabatar da takardun soke aikin kwata kwata tareda raba hannunsu Dana Seelahs,
Hannu suka miqa masa cikin Jin dadi tareda taya junansu murnan sake samun damar aiki a tare Shima hannun ya miqa musu Yana sake gabatar da kansa BARR HAROON SEELAH.
Cikin farin ciki suka sake amsar tayin aiki da juna take akai hotuna da sabon Saka hannu akan new project din dazai maye wancan.
Sai guraren 11:20 suka baro Kai tsaye daga Nan office din airport suka nufa suna Isa suka ajiye motar anan airport suka shige jirgi sbd sunma iso kusan late.
A cikin jirgin yayi breakfast dinsa hankinsa kwance da nutsuwa sabanin siddeeq Daya kasa samun nutsuwa ko Kwanciyar hankalin sbd abinda zai iya faruwa idan aka samu matsalan Dad suka gane.
Suna sauka Lagos drivern Dad dinne yazo airport daukansu sbd shi Jamaal din da kansa Daya turawa Dad text din azo a daukesa daga airport Nan da awanni.
Da farko kaman Bai gane ba Saida ya sake karantawa ya tabbatarda Haroon dinne yayi masa sakon A tura driver ya daukosa daga airport.
Numfashi ya sauke ahankali Yana jinjina lallai Haroon din yafara samun karfin zuciya tinda ya iya masa sakon Kai tsayen Nan Mai kama Dana Bada order.
Driver na Isa airport Kai tsaye siddeeq ne ya budewa Jamaal kofa ya shige bayan kafin Shima ya zagayo ya shiga gaban motar driver Dake Satan kallan Jamaal din ta mirror cikin girmamawa yace
“Barka da dawowa Sir Haroon”
Gyada masa Kai kawai Jamaal yayi sbd hankalinsa na kan sakwannin asibitin Haroon da aka turo na can Poland Yana karantawa.
Suna isowa mansion din Jamaal ya hadiye wani abu Daya danne maqoshinsa Yana kashe wayarsa gaba idanuwansa na Neman sauyawa Amma ya Hana hakan sbd dawowa ko shigowa mansion din seelahs wani abune dabai taba tinanin zai sake ba har abada idan ba yanzu da Dan uwansa Dake tsananin buqatansa ba.
Sedai abinda Basu saniba shine kaman yanda yayi alkawarin duk ranar Daya Sako kafarsa ya dawo musu Saiya tabbatarda sun rasa komai to tabbas tinda ya Sako kafarsa ayau din ya dawo Saiya gyara musu komai sbd Haroon kafin suna kallo ya rabasu da komai daga ranar Daya tabbatarda Haroon ya mallaki macen dayake so fiyeda komai ayanzu.
Kai tsaye bangaren Haroon ya nufa Yana amsa sannu da zuwan da securities din gidan ke masa cikin tsananin girmamawa da mamaki me girma na sauyin Haroon din.
Yana shiga palon Haroon Kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ya shige toilet alwala yayi ya fito yayi Sallah Yana idarwa wayar Dad na shigowa wayar Dake gefensa.
Kallan wayar yayi tareda dagawa cikin nutsuwa yayiwa Dad din gaisuwan Data Saka kirjinsa mummunan bugawa Saida yayi shiru ya sake sauraron muryan da kyau yaji sai yaji Yana Neman rudewa sai kawai yayi Watsi da abinda yaji Kai tsaye ya Bude Baki yace
“Ka sameni yanzu a office din cikin mansion din.”
“Ok” kadai Jamaal yace tareda rigan Dad kashe wayan Wanda ya sake Saka Dad din mamakin halayen da Haroon ya fara sauyawa.
Saida yaci abincin da siddeeq yayi masa ordernsa daga tsadaddiyar restaurant ya koshi kafin ya shirya ya fito tareda siddeeq Wanda shine yake nuna masa hanyar da office din yake tinda Bai saniba.