AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Yana shigowa ya rufe kofar tareda qarasawa ya tsaya gabansu cikin girmamawa da kulawa ya gaidasu Yana kallan fuskokinsu ya sheda akwai sabon bacin Rai da sabuwar matsala wadda kwanan wani zai qare Kila a kwanakin Dan kuwa Kai tsaye yake gane girman bacin ran uwayen gidan nasa.

Kallansa lameenu yayi cikin tashin hankali da son danne tafasar zuciyarsa yace

“Yaya ake ciki a bincikenmu??

Gyara tsayuwa yayi Yana dagowa yace

“Ranka ya Dade tsawon shekarun Nan wlh bamu taba dakatawa daga binciken inda suke ba,
Babu kalar yawon da bamuyiba state state da kauyuka gurin nemansu,
Acan Asalin kauyen na iyayen matar sir Omar din muntashi kauyen gaba Daya Dan kunasa mukayi da gidajen Dake cikinsa dayawansu ma Babu sun mutu,
Hakama itama me aikin munyi nasarar sanin inda aka daukota aiki daga Jos Amma bamu gama sanin a inane take a jos din…….

Cikin daga murya da bacin ran da suke jimawa Basu ganiba a gun Mam ya katsesa idanuwansa na qara yin jajir yace

“Ko nawa zaa kashe a kashe a Nemo mana matarnan Ina buqatan Jin komai daga bakinta zuwa kunnuwana,
A yanzu wannan aikin shine tabbatuwar arzikinmu da tsayuwarmu,
Samun wannan matar shine duk wani abu damuke buqata da ranmu da zuciyarmu,
Omar jeden Yana kallanmu daga nesa amatsayin matsiyata wainda ya take ya wuce nesa ba kusa Dan haka nakeson nuna masa Munfi karfinsa da gaske shi din a tafin hannunmu yake Dan kuwa idan ban zubar da jinin ‘dansa ba bazan taba Ji ko samun nutsuwan zuciya ba..”

Lameenu dakejin zuciyarsa har wani rawa da tsallen tashin hankali takeyi sbd Jin inama zasu samu ganin matar da Gano komai a ranar da hannunsa zai cike aikinsa dabai qarasa ba Dan kuwa barin ‘dan Omar a duniya kaman aikine da Basu samu cikawaba Wanda bazai taba samun nutsuwa ba idan ba cike aikin yayi ba daidai.

Cikin sauti me tattareda radadi da son samun abinda zuciya keso Dad Lameenu yace

“Ko nawa zaa kashe a kashe acika wannan aikin Daya gagara cikuwa shekara da shekaru,
Duk Wanda yasan wani abu gameda me aikin gidan Omar a nemesa aji nasa bayanin a Kuma kawar dashi bayan karban bayanan Dan basason barin sheda ko Daya datasan meyake faruwa Da abinda ma zai farun.

BB da Shima daya kawar da rayuka sunkai nawa akan wannan binciken Jin yayi zuciyarsa ta sake daukan zafi Dan rashin sauki ko kadan Dan haka Koda zasu tada kauyuka da rayuka nawa wannan Karan Se sun Nemo inda matar Nan take sunji me aka haifawa Omar din da inda abinda aka haifa din yake.

Kudi masu yawan gaske Dad Lameenu ya kira Haroon ya bawa BB da yaransa akan aikin Nemo matar wadda Shima Haroon yake tsananin so da buqatan a Gani din duk da Yana Jin shakkar abinda zai iya biyowa bayan samun me aikin da Kuma samun Abinda Dad Omar ya Haifa, duk da haka Shima Yana Nan Yana bincikensa sosai a boye sbd zaiso yasamo information da zai taimaki Dad dinsa Dan ya yaba masa Koda so Daya ne Kuma yayi alkawarin Yana samun Information koman kankantarsa zai sanarwa Dad din.

Bayan bawa lameenu kudin sanar dashi yayi duk information da zaa samu Shima ya sanar dashi ko yayane.

“Angama Barrister” BB ya fada Yana ficewa daga palon Haroon din zuciyarsa cikeda rashin Imani da Jin ya dauki sabon caji Baji ba Gani yayiwa kansa alkawarin Nemo matar Nan duk inda take a cikin Jos da zagayenta.

*****Anyi Hakan da kwana biyu Haroon ya tattara ya tafi Nasarawa sbd gaba Daya Dad ko kallan daraja Baya masa sbd tsananin bacin Ran dasuke ciki akansa Dan haka ya sake shiga damuwa sosai da rashin walwala duk da Bai bari Mum dinsa da Dan uwansa dashi kadai suke communicating a Nigeria sai siddeeq da duk motsin Haroon Yana sane dashi Yana sanarwa Jamaal Dan kuwa kwata kwata Jamaal Bai yadda dasu Dad din akan Dan uwansa ba.

Duk tsananin damuwa da kadaici da rashin mutuntawa ko daraja da Haroon din yake cikinsu Jamaal Yana sane da komai sbd Yana sane ya saka Haroon daukan siddeeq Aiki ya zama Dan hannun damarsa batareda su Dad sunsan asalin waye Siddeeq dinba hakama Haroon kansa baisan ma siddeeq din yanada alaqa haryanxu da Jamaal ba sbd kwata kwata abinda ya sani dashi kadai Jamaal ke magana a Nigeria Dan ko mum Atee duk nacinta ta gaji ta barsa Dan ko kwana zatayi tana kiransa Bata samunsa.

Koda ya karbi aikin project dinnan zuciyarsa cikin shakku da fargaba take sosai tareda tsananin tsoro Dan baisanma ta inda zai fara gudanar da wannan aikin da Dad ya basa damar karshe akansa ba,
Baisan Yaya zai fara ba gashi baisan ta Ina zai fara rokon taimakawan Jamaal ba Dan yasan Jamaal din bazai taba Saka hannu a aikinsu Dad ba Dan haka yake cikin damuwanda tini tafara taba ayyukansa da rayuwarsa Dan kuwa komaima kaman ya Dena ganewa daidai.

Tareda siddeeq suka sauka Nasarawa har babban hotel din da Aka kama masa motar data daukesa ta Kaisa.

Siddeeq ne yakai masa kayansa har dakinsa ya jere masa kafin ya fito ya nufi nasa dakin dayake kusa da nasa Shima ya jere kayansa ya fada toilet sbd zasuyi kwanakin da basusan yaushe ne ranar tafiyansu ba tukuna.

Shi kansa Haroon wankan yayi Yana fitowa ya shirya cikin kaya marasa nauyi yayi Sallah kafin ya kunna wayarsa sai alokacin ya kira Dad ya sanar masa sun iso.

Babu wani yabawa Dad din ya sake maimaita masa mahimmanci da tsananin buri dasuke dashi Akan aikin Nan tareda tabbatar masa da idan aka samu matsala to babusa Babu shi.

Wannan kalman itace kalma mafi Munin data girgiza zuciyarsa ta qarasa tarwatsa duk wani Dan sauran dubaru Dan kokarin Daya rage masa Dan haka ya sake shiga damuwa da tashin hankali me tsananin gaske gashi bayajin zai iya ajiye aikin Dan kaman nauyi ne Daya rataya akansa hakama bayajin Dad din ze barsa ya ajiye din Dan.

Jin yayi ciwonsa na tsananin ciwon Kai da depression na dawo masa sosai Dan kuwa take yafara Jin kaman kansa ze juye Baya gane komai,

Wayarsa ya kashe tareda wurgi da ita Yana silalewa qasa hannuwansa riqe da kansa Dake Neman bugawa tareda bugun zuciyarsa.

Maganinsa yafara rarrafawa Dan nemowa yasha amma kwata kwata Baya Gani daidai saima juyawa dayaji kaman anayi dashi,
Hannuwansa Dake wani Irin rawa sosai suna kakkarwa ya dago Yana kalla sunai masa bibbiyu.

Sake rarrafawa yakeyi Yana faduwa Yana tashi harya Isa gaban mirror inda siddeeq ya ajiye masa maganinsa kafin yakai hannunsa ya dauka ya Fadi akan mirror din kayan Dake Kai suka zube qasa Wanda sautin ya Isa har dakin siddeeq Dake maqale da nasa da sauri ya fito ya shigo dakin Yana ganin Halinda yake ciki da sauri ya qaraso Yana daukan maganin ya Bude roban ya Ciro Daya ya Saka masa a Baki tareda dauko ruwan Roba a fridge ya basa.

Yana shanye magana ko mintina uku beyiba sai gashi ya fara dawowa daidai Yana hada zufa idanuwansa nayin jajir.

Boyayyar ajiyan zuciya me zafi siddeeq ya sauke Yana kallan Haroon dan kuwa da Baya kusa wani abin ya samesa baisan me zaicewa JEEY ba.

Miqewa Haroon din yayi da kansa Yana kasa kallan siddeeq ya Bude Baki ahankali ya furta

“Thank you”

Kujera ya nufa ya zauna ahankali har lokacin zufa yake tsiyayowa ya dauki tissue Dake gabansa aje Yana Dan gogewa kadan.
#MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected