AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Abu Daya da suka sani shine Babu Wanda yaga hawayensa bayan Dan uwansa idanma yayi sbd ya nesanta kansa da kowa bayan Haroon Babu Wanda yasake ganin ko fuskansa.

Yanayin jikin umma Daya rikice da Kuma shi kansa Jamaal din Daya rufe kansa ya Saka dole aka daga jana’iza din har zuwa da safe dakuma yayan baban fadilan Dayake hanyar isowa Shima.

Sai dare sosai Jamaal ya baro asibiti tareda Haroon suka iso gida bayan Haroon yaje ya kamawa Yan umman din masauki hakama Dan baba ma Daya iso duka guri Daya aka saukesu tinda gidan ya kone Babu yanda zaa iya kwana cikinsa.

Koda suka iso gida karfe kusan Sha biyu na dare Dan haka Kai tsaye part din Jamaal din suka nufa.

Mum da Dad ne a palon suna magana cikin Dan daga murya sbd bacin ran da mum ke ciki me tsananin gaske tace

“Kasan Hakan shine yayi sanadin rasa ran yarinyar Nan bawai gobaran da aketa yadawa ya kasheta ita da mahaifinta ba?

Tayaya zaace acikin asibitin iya oxygen dinta ne datake amfani dashi ake gurbatawa da Poison,
Shin bakai tinanin halinda ‘danka zai shiga ba idan ya rasa macen dayake so fiyeda komaiba?
Tayaya kake tinanin zaka fuskancesa idan yasan sakamakon Poison datake shaqa a oxygen ne ta rasu,
Tayaya kake tinanin zai amsa zancen kaman kasheta ne Akai Kai tsaye Babu kwana kwana?
Bakaji tausayin yarinyar Nan ba tsawon rayuwarta rayuwa takeyi cikin wahalar rashin numfashi sai an Siya mata??

Cikin nutsuwa batareda daga hankali ba Dad din ya kalleta da idanuwansa yace

“Ko zan me kike nufi da wainnan kalaman naki?
Me kike nufi da oxygen nata?
Ke da kike likita kikasan aikinki har kikasan akwai poison a iskan datake shaqa meyasa Baki sanar masa shi ‘dan naki ba kika bari har ta rasa ranta….

Katsesa mum tayi hawayen idanuwanta suna qara gudu tace

“Ban taba son sanin ‘yayana Susan waye Asalin mahaifinsu ba sbd Hakan zai tarwatsa zuciyansu,Amma wlh tallahi Babu ranar da bana danasanin Kaine uban yayana masu tsafta,
Me kake tinani?
Na fito na fadawa JAMAAL Ina tinanin mahaifinsa yasan Menene yake damun matar da zai aura sbd shine yasan meye ne yake damun oxygen datake shaqa??
Bazan fada masa ba Amma koman Daren dadewa yayanka zasusan waye Asalin mahaifinsu Wanda Baya barin komai ba dalili,
Yanzu data bar duniyar saika ringa kwana da Shirin koyaushe danka zai iya sanin waye ya kashe masa matarsa data mutu a ranar da aka daura masa aure da ita…

Wani numfashin me sanyi da nutsuwa Dad din ya sauke zaiyi magana Haroon dayake gaba ya shigo Yana kallan mum dinsu da kalaman dayake ji abakinta Dan kuwa bazai taba yadda da Dad dinsa zai iya kisa ba duk da Barnar dasuke aikatawa bayan fage Amma mahaifinsa bazai iya kashe Rai ba bare macen da already tana fama a tsakanin Rai da mutuwa.

Jamaal kuwa idanuwansa dasuka qarasa rinewa gabaki Daya ya dago ya zubawa Dad din Wanda ya miqe tsaye Yana kallan jamaal din zufa na joqosa daga kuryan jikinsa.

Mum ma mummunan faduwa gabanta yayi zufa na tsitsifo mata Dan kuwa Bata fatan Jamaal yaji abinda suke fada.

Dad Jamaal din yake kallan Yana kokarin danne abinda yake ransa Yana ambatar sunansa cikin kulawa zeyi magana Jamaal din ya juya ya kallo Mum ya Bude bakinsa da yayi masa wani irin mummunan nauyi Kai tsaye yace

“Results din fadila duka sun tabbatarda oxygen nata ne yayi sanadin komai har rasuwanta right??

Wani mugun zufa da faduwan gaba ne ya Saka mum juyawa ta Kalli Dad Wanda Shima ita yake kalla kafin ya matso zaiyiwa Jamaal din magana Jamaal ya katsesa da sake jefawa mum tambayarsa.

Numfashi ta sauke zuciyarta na nauyi ta matso tareda kamo hannunsa Daya cikin tsananin sanyi da baqin ciki tace

“Eh, oxygen nata shine yaringa poisoning nata ahankali harta rasu Amma muna Saka ran daga karfin da yayi mata ne da oxygen din shiyasa ya zama kaman poison ya mata illa..

Baice komaiba zame hannunsa yayi daga cikin nata ya zari keys din hannun Haroon ya juya ya fice.

Duk yanda Haroon yaso binsa kasawa yayi sbd mamaki da shock din dayake ciki Shima duk da Babu tabbacin Dad dinne itama mum kawai zargi ne sbd Dad baiso aurenba da farko.

Koda ya Isa asibiti Kai tsaye file din fadila ya dauko yafara dubawa ko Gani sosai bayayi kafin ya fito ya nufi lab dinsu a cikin Daren ya buqataci sabon awo tsakanin oxygens din sabo da tsoho Dana fadila.

Haroon baro gida yayi ya biyosa asibiti Amma Sam kwata kwata ya kasa samun ganinsa Dan kuwa a cikin Daren gaba Daya ya daga hankalin asibitin akan sabon awo da komai Wanda ya bawa likitoci da ma’aikatan lab dinsu tsoro da shiga tashin hankali Dan kuwa da farko binciken boye Akai baa son daga zancen.

Koda asuba tayi tsaban tashin hankali har an hada results din Wanda ya tabbatarda mutuwar fadila due to gurbatan oxygen nata ne.
##MAMUH

 

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_**_Arewabooks@Mamuhgee_*
27
Wani mummunan jiri ne ya dibi Jamaal din Wanda sai alokacin ya fashe Da kukan Daya girgiza Haroon da mum dinsa da isowanta kenan asibitin cikin tashin hankali da tsananin tsoro sbd Kwana sukai itama da Dad din cikin tashin hankalin fitina da maganganun da suka Sakata Jin son barin qasar a ranar.

Duk wani sheda ko alaman inda poison din ya samu shiga oxygen dinta Jamaal yayi daga daren zuwa safe Bai gane ba sai Abu Daya wato yawan zuwan BB asibitin Wanda ya samu tabbacin duk karshen wata yake zuwa so Daya dubiyan kaninsa yaronsa da suka karya da gangan suka ajiyesa asibitin yaqi warkewa sbd Daya kusa warkewa saisu sake lalata gyaran.

Hakama mum dinsa ta kasa fada masa komai taqi sake maimaita masa tabbas mahaifinsa ne yayi Hakan,

Wane asalin rashin Imani ne zai Saka a taba fadila macen da numfashin duniya Bata iya shaqa saina Siya,

Gida suka dawo Kai tsaye palon Dad dinsa ya nufa zuciyarsa na qunan dayake Jin har wata wuta ce take cin kansa.

Babban abinda fara bawa su Dad din mamaki da shakka shine Kai tsaye kafin goman safe tini akaiwa su BB da yaransa kaf mugun Kamun Daya fara yaduwa a labari tareda tabbaci akan zargin kamasu da sirka poison acikin oxygen na asibitin SEELAHs Wanda yayi sanadin rayuwar matar Dr Jamaal Seelah din,
Hakan ya qarawa labarin saurin yaduwa sosai da gudu kaman wutar daji take Yan jarida sukaiwa asibitin da gidan kawanya.

A yanda Jamaal ya nufo su Dad din mum dinsa ce tayi saurin Shan gabansa tareda riqe hannunsa Dan duk mugun halin Dad bazata so yayanta suyi sa’insa da mahaifinsu ba bare maganar datai da Dad a ajiyan ta tabbatar mata da Dad Babu abinda bazai iyaba Dan haka ta riqo hannun jamaal ta girgiza masa Kai cikin qaramin sauti ta Bude Baki tace Karkayi komai karkace komai wannan umarni nane,
Haqqin dayake hanunusu bazai taba taba yayana ba kaman yanda bakuda sani bakuda haqqi bazanso ka taba gurbata kanka aikinsu ba.

Cikin Bacin Rai me tsananin gaske Dad da Alh Lameenu suke kallanta zaiyi magana cikin hada zufan tashin hankali mum Atee ta shigo cikin tashin hankali tana sanar musu ga asibitin SEELAHs can ana kokarin Banka mata wuta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected