AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Sannan ganin irin kallan tsananin so da kaunar da Aleena ke masa ya Saka maman fadeelan sake tabbatarda abinda tayi tinanin sedai tinda Babu wanda yace mata komai so itama batada hurumin magana bare tambaya.
Dr Aleena daga karshe itada Dad Omar palonsa suka nufa Dan tattaunawa a tsakaninsu wanda Mum Nur Bata damu ba ta barsu su samu tattaunawansu sbd tasan shaquwa da kaunar dayake tsakaninsu
tin ba yanzu ba tasan asalin kaunar da Omar yakewa Jamaal ta Aleena ce bawai Dan Yana Dan ‘dan uwansa Mam ba,
Kaunace yake masa wadda ta fito daga wadda yakewa mahaifiyarsa
Ita Kanta Dr Aleena Babu lokacin da batai fatan inama ace Omar dinne mahaifinsu Jamaal din sedai kaddara haka ta zuwar musu Allah baiyi iyayensu da sukazo aurensu zasu gansu a tare ba.
Ameeenatou ma tinda taji maman fadeela itace maman fadeelan Jamaal take jikinta yayi sanyi Dan haka ta Dan sake janyewa daga palon karshe ma sama ta koma sbd tanada shiga office washe gari dan haka Aiki ma ta koma tafara a laptop.
Hafiz da Fatmah Basu dawoba sai a satin Suma zasu dawo Dan haka shigarta office dole zatai Aiki idan sun dawo sun huta su fara fita ita Kuma ta zauna gida ta huta kafin ta sake komawa.
Sai dare sosai su Dr Aleena suka tafi Mum Nur ta Rakata har harabar gidan Suna fira kafin suka wuce ita Kuma ta dawo Ciki.
Washe gari Ashley ta rigata fita aikinta da zata fara itama a ranar na tsadaddiyar clinic din JDENS da aka Bude sbd ita din tareda daukan likitoci masu kyau harma da Dr Aleena a Cikin manyan likitocinsu da zata ringa Dan zuwa time to time tana duba manyan cases nasu.
Da sabuwar motarta Lexus GX grey color Ashley ta fita daga Mansion din sanyeda wata tsadaddiyar jallabiyan Cairo sai designer handbagsm dinta tana qamshin me sanyi ta fice.
Ko data isa asibitin wadda Suna Macau Akai bikin budeta Dan haka Kai tsaye Cikin girmamawa aka tarbeta ana Bata girmanta na sune masu asibitin tukuna ta nufi inda zata fara aikinta duk da ba Wani dadewa zatai ba karatu zataci gaba bisa ga shawaran Uncle Ahmed daya bayar akan ta wuce ta zama likita kawai.
Ameeenatou ma sai sai 10 saura ta fita itama ta wuce Aiki Cikin tata motar.
Ashley ta Riga Ameeenatou dawowa Dan haka Koda Ameeenatou ta dawo da dare harta huta ta sauka kitchen Suna tareda dadah tana tayata Aiki sbd yau Didi Bata Nan ta fita.
Wanka tayi da sallan magrib ta sauko ta nufi gurin Dad dinta da zai Yi tafiya tareda uncle Ahmed gobe suka zauna sun jima Suna magana kafin Akai dinner ta gida gaba daya harsu babbah sbd hakan sukeyi indai akwai baqi gabaki daya ake cin abinci a table hardasu babbah kokuma idan Wani zaiyi tafiya hakan sukeyi.
Dan haka gaba dayansu sukai dinner cikeda kauna da kulawa da juna tareda bankwana tukuna kowa ya wuce dakinsa.
Washe gari itace da kanta takaisu airport kafin daga can ta wuce Aiki Dan haka gidan tsit sbd mum Nur ma ta fita ta tafi gidan Jamaal gurin dr Aleena itada Didi.
ARFAT kuwa Yana gurinsu dadah Shima Hafiz kadai ake jiran ya dawo shine zai masa komai na school din dazai fara zuwa daman anbari ne yafara sabawa da Sabon gurin tukuna.
Kwanasu Dad dinta biyu da tafiya Jamaal suka sauka Nigeria Kai tsaye tin a airport Yan jarida suka rufesa da ihun tambayar rashin ganinsa a gurin rasuwar wanda yake tamkar uba a garesa wato Mam da iyalansa da suka rasu lokaci daya.
Cikeda shock da tsananin mamaki ya juya ya Kalli siddeeq wanda yakeda tabbacin ya sani dole boye masa yayi sbd shine idonsa da jinsa a harkar komai dayake gudana a duniyar media.
Siddeeq sallamar Yan media din yaji tareda securities har suka samu Jamaal din ya shiga mota Yana Jin kansa na riqewa da Wani irin nauyin gaske sbd Bai taba tinanin daddy lameenu zai rasu da familynsa duka a Lokacin daya Bai jiba,
Tayaya?
Meya faru bayan tafiyarsa?
Juyawa yayi ya Kalli siddeeq Dake gefensa Cikin motar batareda yace komaiba
Shima siddeeq din batareda yace komaiba ya kamo bayanin komai daya Adana a iPad dinsa ya miqawa Jamaal din.
#MAMUH*_Arewabooks@Mamuhgee_*
133
Zubawa ipad din Idanuwansa yayi Yana karanta duka labaran dayake rubuce akan rasuwar Aliyah zuwa ta Mum Sarat da Daddy lameenu tareda Mum Atee.
Labarin Dad dinsa da Baya qasar bayan ya yanke jiki ya Fadi sbd rashin Dan uwansa da matarsa ya zubawa Idanuwansa Yana kalla Idanuwansa jajir.
Radadin rasuwar Aliyah data Mum Sarat yafi ji fiyeda ta sauran Amma ko Daddy lameenu uba ne tinda suka kasance iyayensa Dan haka ko yayane akwai ciwo da radadin rashinsa,
Yasan ya aikata abubuwa da yawa Amma Bai cancanta hakan daga Dad ba sbd koma menene suka aikata a tare suka aikatasa dole akwai gurin ragawa,
Shi kansa baida niyar qyalesu dukan Amma Bai taba tinanin aikata kisa garesu ba Amma dai yaso rabasu da abinda suke so fiyeda rayukan duniya da mutanen Cikinta,
Yaso rabasu da komai sai sun koma nera goma tana Basu shaawa Amma basuda halinta ta yanda sunaji suna Gani zasu dandana baqin Cikin dayafi na rashin Rai da suka ringa kashewa ba tausayi.
Jajir Idanuwansa suka sake tareda cikowa da Wasu irin ruwan hawaye masu radadi da Ciwo ya rintse Idanuwansa Yana Jin abinda Bai taba ji ba akan mahaifin daya haifesa,
Mahaifinsa ne me wannan mummunan rayuwar ta rashin digon Imani ko kadan harga wanda suka kasance Rabin jikinsa.
Kasa riqe hawayensa sukai Saida suka gangaro ya sake rintse Idanuwansa Yana kasa cire tsananin ciwon dayake ji na kasancewan Dad dinsa mahaifinsa.
Handkerchief ya Ciro ya goge fuskansa datai ja take abinka da farar fata.
Miqawa siddeeq iPad din yayi yace
“Kasan duka takardun dukiyarsu da signing Dina suke Akai lokacinda Haroon ya tafi Poland na taho a matsayinsa duka ka hadasu komai na dukiyar Dad zai bar hannunsa
Wainda ba signing Dina bane Akai a hada musu takardun zan Sakashi signing dinsu batareda saninsa ba.”
Gyada Kai siddeeq yayi Cikin shiga nazari da tinanin abinda zai biyo baya sbd Mam Babu abinda ya hada da dukiyarsa,
Jamaal ne kadai a duniyarsa yanzu dayafi masa dukiyarsa Amma bayan Jamaal Babu wanda bazai iya kawarwa akan dukiyarsa daya zubarda shekarunsa tin na samartaka har tsufa Yana tarawaba data tafi da rayukan duka Yan uwansa da abokan arziki da yawa,
Dan haka ayanzu abinda Jamaal zaiyi shine babbar balain da Mam bazai iya daukaba ace ya wayi gari kaf dukiyarsa ta koma ta Jamaal din Kuma a gaban Idanuwansa ya rabar dasu ga Al’umma yaqi barin komai???
Hummmm” ya sauke ajiyan zuciya da numfashi a Lokaci daya marasa sauti.
Koda suka isa gida Jamaal gaba daya baya Cikin dadin zuciya ko kadan sbd labarin rashin,
Yana isa gidansa ya tararda Ayesha a Cikin su Mum dinsa itama ta fito Cikin sanyin jiki tayi wata irin ramar data sauya kamanninta a qanqanin lokacin.
Su Mum na kulawa da ita sosai kaman yarsu sbd tausayinta da tinanin rashin kowa datake Ciki Amma sun dage sun zama gatanta Suna debe mata kewa musamman dukkaninsu dasuke shaawa da kewan rashin ‘ya mace,
Maman fadeela na mata kallan fadeelanta ita Kuma Mum na mata kallan batada ‘ya macen dayake shaawa samu tin lokacin baya.
Ita Kanta Ayesha tana Jin yanda suke kaunarta hat zuciyarta sedai rashin mahaifiyarta Abu ne da bazata iya mantawa lokaci daya ba musamman daya kasance itace uwarta itace ubanta.