AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE
Ashley ce tayi saurin juyawa gabanta na faduwa da karfi ta Kalli babban dayake tsaye bakin kofar kafin yafara shigowa palon gabaki daya a natse.
Ameenatou rintse Idanuwanta tayi Suna sauyawa zuwa ja zuciyarta na nauyi batareda ta juyoba.
Fatmah kuwa wasu hawaye ne masu tsananin zafi suka ciko Idanuwanta sbd kalaman Ameenatou da suke a bayyane zaginta ne tayi itada iyayenta da kalaman data fada.
Tsayuwa babbah yayi a gaban Ameenatou din bayan ya Kalli Ashley ya Kalli Fatmah ya tsayar da kallansa kan Ameenatou din lokacin Hafiz Shima ya shigo palon ya tsaya Yana kallan yanda duka sukai cirko cirko babbah Cikin mamakin abinda yaji yace
“Ameenatou kikace kinsan uban ‘danki?
Da sauri Hafiz ya Kalli Ashley wadda ta rasa abin cewa bayan hawayen Dake Neman ciko Idanuwanta.
Dadah ma da bataji abinda Ameenatou ta fada ba Saida babbah da a maimaita tambayar ta Kalli Ameenatou din da sauri.
Shiru Ameenatou din tayi tana kasa dagowa ta Kalli babbah sai hawayen Dake Ciki Idanuwanta da sukai ja sosai.
Fatmah da zuciya ta gama dibanta kallan Ameenatou din Tayi Cikin radadin kalaman da suka kasa ficewa daga kanta tace
“Zaki fada ne ko na fada masa tinda kince ni da iyayena bamuda hurumi ko iKon sanin mahaifin danki?
Dawo da kallanta tayi kan babbah tace
“Babbah Wani Cikin ne a jikinta na haihuwa sai ta hada duka ta fada Maka waye uba…….” Wani lafiyayyan Marin daya sauka fuskanta ne ya Saka sauran maganarta katsewa tana ganin wasu mahaukatan taurari.
Dad dinta ne tareda su Dad Omar dukansu suke tsaye a bayanta.
Didi ma Wani Marin ta Kuma sauke mata tana son magana Amma zuciya ta cita sbd yanda take maganar kaman hade da rashin kunya ga Babbah.
Hawayen Dake cikeda Idanuwan Ameenatou ne suka gangaro mata tana rintse Idanuwanta tareda yin baya tana kasa dagowa.
Babbah wata nannauyan ajiyar zuciya ya sauke me sanyi kafin ya dago ya Kalli kowa daya bayan daya yaga dukkaninsu shi suke kalla batareda kowannensu ya shiga mamakin abinda aka fadan ba hakama Babu shock ko alamansa a tattareda kowannensu Dan haka Shima saiya Danne yaqi shiga shock din sbd magana ce da baikamata ya dauka da Mahimmanci ba Shima Dan haka Fatmah din ya kalla wadda ke Kuka sosai tana tallafe da fuskanta kafin ya Maida kallansa kan Ameenatou datake hawaye sosai tana bayan dadah ya sake sauke ajiyan zuciya sbd iskan dayaji ya cike masa Ciki kaman ma ya kumbura a take a gurin.
Cikin sanyi da nutsuwa Babu wasa ko kadan ko sakewa a Cikin maganarsa yace
“Ameenatou menene yake faruwa nakeson ji daga bakinki?
Meya hadaki da Fatmah take wannan maganar?
Me Kuma kunnuwana suka Jimin akan uban Arfat??
Uban waye uban nasa da kike cewa kin sani?
Kin sani fa kike fada Ameenatou?
Kuka ta fashe dashi Mai tsananin tsima zuciya da baqin Ciki tareda kunyar kanta da yau take ganin asalin kame fuskan babbah.
Dadah ce ta kalleta tana cirota daga bayanta tace
“Me yake faruwa akace ba Kuma zakiyiba”
Ashley ce ta motsa zatai magana babbah ya kalleta Babu rahama ko daya a fuskansa yace
“Ayshatu ki kiyayeni a daidai wannan lokacin Kuma idan kin jira ai kanki zanzo”
Shiru Ashley tayi jikinta na sake nauyi da shiga Wani mummunan fargaba.
JAMAAL ganin kowannensu yayi shiru ya sakasa matsowa gaban Ameenatou ya Ciro handkerchief dinsa zai share hawayenta ta ture hannunsa da karfi tana sake fashewa da kukan.
Kallan babbah yayi yanason ya sanar dashi duka amsoshin tambayarsa Amma Dad ya girgixa masa Kai sbd babban girman da zaa bawa babbah shine barinsa yayi magana da Ameenatou din da kansa.
Hafiz ne ya dage gefen Ameenatou din ya Kalleta kafin ya Kalli babbah ganin yanda ransa yayi mummunan Baci yace
“Babbah kayi hakuri Nima nasan waye baban Arfat din tare muka boye hakan sbd kada ranka ya sake Baci tinda haryanzu baka yadda da aurensa ba”
Tari ne ya kufcewa babban ya dago ya Kalli hafiz Yana cewa
“Wane auren?
Tanada auren ne daman?
Inace anbar maganar auren dayake kanta ma bare Wani auren”
“Jamaal da Bai iya wannan kwana kwanan zancen ba Jin yayi ya kasa riqe zancensa sbd kukanta dayake cizon zuciyarsa ya Kalli babban Cikin nutsuwa da girmamawa irin tasa yace
“Duka abinda suke son fada shine Arfat ‘dana ne,nine mahaifinsa”
Qin kallansa babbah yayi Yana kokarin Danne abinda yakejin Yan taushe kirjinsa ya juya ya Kalli Dad Omar wanda ya sauke ajiyan zuciya Yana kallan babban Cikin tsananin Jin nauyi Shima.
Hakan da Omar yayi ya tabbatar masa da abinda ake fadan gaskia ne.
Juyawa yayi batareda yace komaiba zai bar gurin JAMAAL ya Bude Baki Cikin sanyi yace
“Babbah kayi hakuri ko yanzu Wani Cikin ne a jikinta”….
Saurin juyowa dadah tayi da karfi ta Kalli Ameenatou Wanda ta sauke Kai kukanta na tsayawa.
Babbah kuwa kafafunsa kasa daukansa sukai ya juyo Yana kokarin riqe shock dinsa ya Kalli Ameenatou ta Bude Baki muryanta na rawa da Kuka tace
“Babbah Dan Allah kayi hakuri wlh sharrin Shedan ne”
Sarewa kafafunsa sukai yayi Wani mugun zama a kujeran Dake kusa dashi rigarsa na jiqewa da Wani irin gumin gaske.
Da sauri Hafiz ya nufesa Jamaal ya datakar dashi ya isa gurinsa shida siddeeq dayayi saurin daukan magazines Dake ajiye a table da alamar Wani yayi karatunsu ya bari a gurin suka fara masa firfita Jamaal na kokarin dubasa sbd da alama attack yake kokarin samu.
Ameenatou na ganin hakan itama ta matso gurin babban tana durqusawa gefensa sbd a zuciyarta ko Arfat tanajin kaman Bata masa tsananin kaunar datakewa babbah ba sbd shine uwarta Kuma ubanta shi kadaice jini dangin mahaifiyata,
Shine Wanda rayuwarsa ta kuruciya ta qare a gurin tsananin so,reno da dawainiyar mahaifiyarta ya Kuma qarar da manyancinsa a tsananin sonta fiyeda rayuwarsa da Kuma dawainiyarta Dan haka Bata hada sonsa da komai a rayuwarta ba.
Tsabar rikicewa babbah ganin yayi kaman ma baya Gani sosai take jininsa ya haye sama.
Jamaal na ganin hakan ya fara basa taimakon gaggawa Yana Hanasa shidewa.
Ganin hakan kowa ya shiga tsoro da tashin hankali sbd da gaske dai babban ya rikice.
Mum Nur tsoronta kada babban zuciyarsa ta buga su shiga uku.
Kamasa dole Akai zuwa bangarensa aka kwantar dashi a kujera Jamaal ya dubasa da kyau aka samu bugun zuciyarsa dayake yawan da baa so ya dawo daidai ya masa abinda zai masa suka samu ya rintsa badan ya samu sassaucin abinda yakeji ba sai Dan dole yayi baccin idan ba hakan ba zai iya samun bugawan zuciyar.
Bayan sun fito dadah zubawa Ameenatou Idanuwa tayi Yana karantar yanayinta ta tabbatarda da gasken dai Cikin ne.
Numfashi ta sauke ahankali tareda kama hannun Ameenatou din sukai dakinta bayan ta kira Ashley itama.
Zaunawa sukai ta kallesu su duka biyun Cikin nutsuwa tace
“Ayshatu da gaske Cikin ne kenan?
Numfashi Ashley ta sauke tinda dai ankai karshen zance kowa ya sani ba Damar boyewan
Gyada Kai tayi tana dagowa cikeda kunya.
Mamaki ne ya sake kama dadah ta juya ta Kalli am din tana mamakin yaushe hakan ta faru bayan tana tareda su.
Samun nutsuwa da farin Cikin Jin Jamaal ne mahaifin Arfat Kuma Cikin na yanzu ya saka mamakin nata taqaituwa da Jin kwanciyar hankali sedai tasan babbah Kam sai anyi fama Dan haka kallan Ameenatou din ya sake Yi kafin ya janyota jikinta tana cewa ta Dena kukan hakan kada Wani ciwon ya shigo Kuma.