AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

AMEENATOU BOOK1&2 CMPLT BY MAMUHGEE

Kaya taje ta dauko ta saka mata saukinsu da rufin asirinsu yau weekend ne Dan haka Babu likitoci da ma’aikata sosai patients Kuma suna dakunansu hakama nurses dinsu.

Dr Fatima CE da sister Ashley sukai mata stitches Wanda ya Sakata sake somewa a gurin daqyar suka Samu ta farfado Wani wahalallen baccin wuya me qarfi yayi gaba da ita.

Alluranta Akai mata Dr Fatima tace Dr JEEY din zaizo da magani anjima suka wuce itada Dr zayyan Dake juranta waje.

Suna tafiya sister Ashley ta tattara kayan Ameenatou din Dake toilet dinsa ta fara kaiwa kafin ta dawo ta dauketa a wheelchair ta tafi da ita dakinta daqyar ta iya kwantar da ita ita kadai.
##MAMUH
#EMJEEY

*_ZAFAFA BIYAR_*

1 *_Ameenatou!!_*
_Mamuhgee_

2 *_Tsutsar Nama!!_*
_Billyn Abdull_

3 *_Gudun Kaddara!!_*
_Safiya huguma_

4 *_Kwankwason Jimina!!_*
_Miss xoxo_

Guda Daya 400
Guda biyu 700
Guda uku 1k
Guda hudun 1200

*_6019473875 MUSAA ABDULLAHI SAFIYAH keystone bank_*

*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*

*_MTN/VTU 09134848107_*

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

*_Arewabooks@Mamuhgee_*
#ZafafaBiyar
82
Tin a hanya kafin su Isa gida siddeeq yaga jikinsa ya rikice Dan haka wayarsa ya fitar Yana kallan JEEY din Yana kallan hanya ya Nemo numbern Dr zayyan ya sake Saka Kiransa Yana daukan wayar ya sanar dashi idan sun gama da Ameenatou ya same su gida Jeey din ma ba lafiya sosai.

Kashe wayar yayi bayan Dr zayyan yace gashinan zuwa,

Ajiye wayar yayi gefensa Yana Dan daidaita gudun motar sbd jikin JEEY din.

Suna Isa gida yayi parking ya fito da kansa ya budewa JEEY din kofa ya fito ahankali cikin nutsuwa da rashin kuzari suka nufi ciki.

Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa Yana Isa ya zare cardigan din kan kayansa ya fada gadonsa ya dunqule guri Daya tareda shigewa bargo.

Siddeeq da kansa ya shiga kitchen ya hadawa JEEY din tea me zafi da sandwich tareda ruwa mara sanyi ya nufi dakin dasu.

Babu abinda JEEY din ya iya kalla saima karfi da zazzabin ya kara tini ya fara rawan jiki sosai zafi na fita jikinsa.

Sai bayan kusan awa biyu kafin Dr zayyan ya Isa bayan ya ajiye Dr Fatima asibitin SEELAHs itama.

Sosai jikin JEEY din ya Dan yi tsanani Dan haka da allura suka fara zafin jikin ya fara sauka kafin ya fara dubasa.

Ba Wani matsala bane bayan zazzabi me karfin gaske na tsananin karfin buqatansa daya sauke a Karan farko.

Bacci me karfin gaske ne Shima ya daukesa bayan tafiyan Dr zayyan Wanda sai a lokacin hankalin siddeeq ya Dan kwanta ganin zazzabin a Dan sauka.

Dayar dakin ya koma Shima Dan ya samu baccin da Bai samu ba tin cikin Daren kaman Shine me angoncewan.

Karfe goma Sha biyu ya samu farkawa ya Bude idanuwansa ahankali da sukai nauyi sosai hakama kansa yayi nauyi.

Tashi zaune Yafara yi Yana Dan rude idanuwansa ahankali ya Bude ya Dan juya ya kalli time.

Saida ya dauki seconds kafin ya ziro kafafunsa kasa ya sauko Yana Dan Jin rashin karfin jiki ya nufi toilet ya shiga.

Brush yayi da Wanka da ruwan zafi jikinsa ya Dan sake ya samu karfi ya fito daureda towel jikinsa na fidda qamshin shower gel dinsa me sanyi.

Underwear da kayan marasa nauyi ya saka yayi Sallah kafin ya fito a natse Fresh dashi kaman sabon saurayi.

Tea kadai ya iya yasha yasha magani har lokacin jikinsa Bai dawo daidai ba,

Yana gamawa ba jimawa amai ya taso masa Wanda ya Sakasa komawa toilet sosai ya ringa sheqasa har Saida ya Dan galabaita tukuna ya sake wanka ya fito ya fada gadonsa ya rufe.

Har yamma sosai Babu sauki a jikinsa haka suka kwana a zaune cikin damuwa da tashin hankali
A asibiti ma haka sister Ashley ta wuni ta kwana tana jinyar Ameenatou cikin tashin hankali da boye boyen kada Wanda ya gane Menene ya samu Ameenatou din gashi tashin hankalinta sai qaruwa yakeyi sbd Ameenatoun Babu sauki ta ko Ina gashi ko karfin da zatai kuka ko Wani tashin hankalin batada shi haka take kwance abin tausayi.

Siddeeq kusan so shida Yana Kira yana Jin Yaya jikin Ameenatou din sbd JEEY da Shima duk ya farka cikin karfin hali Saiya Saka ankira sister Ashley anji masa jikin nata.

Jin Dr din baida lafiyar sosai ya Saka sister Ashley dole daurewa ta nuna musa jikin Ameenatou din da sauki sosai zazzabi ne ya dan rage sai stitches dinta da warkewa ba yanzu ba sai ankwana biyu.

Washe gari dole Dr zayyan ya sake zuwa ya dubasa kaman yansa Dr Fatima itama ta sake komawa asibitinsu Ameenatou din a matsayin dubiya ta dubata ta wuce.

Daqyar ya samu jikinsa ya fara warwarewa da yamman ranar Wanda ya basa Daman Kiran sister Ashley da kansa yaji jikinta.

Ta basa tabbacin da sauki sosai,
Abubuwan buqatansu kawai ya Saka Siddeeq tura mata kudi masu yawa akan tayi musu ko online shopping ne da abinda duka rashin lafiyan ko jinyar zata buqata.

Da daddare sallan ishai kadai yayi ya fito cikin doguwar Riga milk me kyau da tsada,
Kallo Daya zakai masa kasan jinya yayi sbd fuskansa ta nuna hakama yanayin kuzarinsa duk da ya boye Hakan sosai.

Siddeeq ne a mota Yana jiran fitowansa Dan haka Yana fitowa ya shiga motan shikuma ya tayar suka fice zuwa asibiti.

****Ameenatou kuwa tin jiyan yanda aka daukota daga dakinsa kusan Hakan take har lokacin Babu wani kuzari ko motsin kirki,

Ta illatu sosai sbd Bata taba dandana azaba da wahala irin wannan ba tin a lafiyanta har yanzu da batada lafiyan,
Idanuwanta sunyi zuru zuru sun fada sosai kaman wadda tai jinyar wata,
Zazzabin jikinta sosai yaqi sakinta har lokacin jikinta dumi ne dashi.

Tea kadai take iya Sha Wanda sister Ashley ke iya lallabawa tana Bata sbd takasa cin kowanne irin abinci.

Tin jiyan sister Ashley duk yanda zatai ta Hana kowa gane akwai ma rashin lafiya jikin Ameenatou din tayi ta Hana,
Hakama duk iya kokarinta na ganin ta kula da ita akan abinda ya farun tana yinsa Dan haka ne ma yasa Ameenatou din tayi Dan Dama dama hakama ba Ameenatou kadai ba a yanzu itama batason kusancin JEEY din da ita sbd tasan zaiyi wuya Ameenatou Bata fara tsoronsa ba daga yanxu din.

Da daddaren ruwan zafi ta shigar da ita sukai gashi kafin akayo wanka suka fito ta zaunar da ita bayan sun Tako ahankali daqyar sbd raunin Ameenatou din,
Goge mata jikinta tayi tareda shafa mata Dan body mist kawai ta Saka mata kayan bacci masu Dan kauri sosai riga da wandon ta Bata maganinta Wanda taqi Sha Sam Saida tai mata dabara kafin Tasha.

Qamshinsa ne ya fara yi musu ison zuwansa kafin aka Bude kofan dakin Kai tsaye ya shigo cikin nutsuwa, idanuwansa masu haske da se ayau suka dawo daidai sbd ciwo ya saukesu akanta tareda zuba mata su yana takowa zuwa cikin dakin.

Ameenatou Bata gansaba sbd idanuwanta a rufe suke tana kwance bacci ya Dan fara daukanta,

Tsayawa yayi a kanta cikin nutsuwa da Kwanciyar hankali yayiwa fuskanta kallan seconds kafin ya waiwayo sister Ashley a natse ya Bude Baki suka gaisa Yana sake tambayar jikin Ameenatou tareda Jin idan Babu matsalan komai.

Babu matsala ya sanar masa bayan rashin kuzari datake fama dashi sai stitches nata datake kukansu koyaushe Amma Suma zasu dauko hanyar warkewa inshallah.

Numfashi me sanyi mara sauti ya sauke ahankali kafin ya daga hannunsa Daya ya Dora a goshinta cikin sanyayyar kulawa ya rankwafo zai sake Jin jikin nata Dan Bata nasa treatment din da kulawanda Bai samu Daman bataba sai kawai ta bude idanuwanta ahankali akan fuskansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153 154 155 156 157 158 159 160 161 162 163 164 165 166 167 168 169 170 171 172 173 174 175 176 177 178 179 180 181 182 183 184 185 186 187 188 189 190 191 192 193 194 195 196 197 198 199 200 201 202 203 204 205 206 207 208 209 210 211 212 213 214 215 216 217Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Ad Blocker Detected